MISBAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI
Mun tsaya
Ta mike, “Ni zan wuce, zan dawo gobe in Allah Ya kaimu. Sannan zan ci gaba da bincike akansa daga gare ku, da fatan za ku bani hadin kai”.
Mama da ke sharar kwalla ta ce, “Inshaa Allah za muyi duk abinda ya kamata, mungode”. Nan suka yi sallama ta fita.
Alhaji dake tsaye yana jinsu hankalinsa ya matukar tashi, tsananin nadama ya kara shigar sa, tausayin dansa ya kama shi. Ya iso falon hankalinsa a tashe, ya kalli Hajiya.
“Ki yafe min abinda na miki, abinda na yiwa danmu ban kara fahimtar illar da na yiwa yara na ba sai yanzu”.
Hajiya tsayawa tayi tana kallonsa, don kuwa a tsawon shekarun da suka yi na aure bai taba budar baki ya bata hakuri ba komai girman laifin da ya mata, haka bai taba nadama akan wani abu da ya zartar don ra’ayinsa ba.
Washegari karfe sha daya ta nufo gidan, bayan ta gama zagaye marasa lafiya a asibiti. L) Kamar yadda ta same shi jiya haka ta sake samun sa a yau, hannunta rike da (tray).
“Assalamu alaikum Nuraddin”.
Dago kai yayi ya kalleta ya watsar, ta kalle shi ta girgiza kai.
“Ka manta me na fada maka jiya? Ka dinga bude (window), kaga yau ka kara min aiki, dole in dinga zuwa bude maka (window tunda ina son abokina ya shaki iskar duniya”.
Nan ta zuge komai kamar jiya, sannan ta zo ta hada (coffee) ta mika masa. Ko kallonta bai yi ba balle ya karba, ya dage kai. Bata hakura ba, “Kayi kokarin sha (l’am Www.bankinhausanovels.com.ng
a very good coffee maker). Oh na gane, ko sai
na sa maka a baki ne?” Nan tayi kokarin kai (cup) din bakinsa, ya yi saurin doke hannunta sai da (cup) din ya fadi kan (tiles) ya fashe har ruwan (coffee) din ya dan kona ta.
“Auch!”. Tayi kara.
“In ba zaka sha ba meye na bigewa? Kaga yanzu ka kona ni. (You are such a bad friend)”.
Har yanzu bai kulata ba, nan ta hau tattara (glass) din da ya fashe, bata ankara ba kuwa ya yanke ta. Ga mamakinta ta ga ya mike ya dauko (first aid box) ya yi (dressing) wurin.
Ta jima tana kallonsa tana mamaki, saboda bata zaci hakan ba. Ya kalleta fuska a murtuke, “Wai me kike
so ne gare ni? Na ce miki bana son ganin kowa a
inda nake, bana bukatar wata
DANGANTAKA!”.
Ya fada cikin tsawa da huci.
Kinji ciwo saboda ni, ban so, don haka kar ki sake kuskuren zuwa inda nake”.
Da karfi ya fisgeta zai yi waje da ita, sai yaji kansa yana wani irin sarawa, yana masa azabar ciwo. Nan ya saketa ya rike kai yana nishin azaba tamkar mai shirin barin duniyar.Hankalinta ya tashi, tayi saurin ciro wasu allurai guda uku a cikin jakarta tayi masa a hannu, ta taimaka masa zuwa gado ya kwanta, bacci mai karfin gaske ya dauke shi. Ta jima tana zaune tana kallon sa cikin damuwa da tausayawa, sannan ta mike ta karasa abinda take yi a dakin, sannan ta fita. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka Bahijja ta kasance kullum sai ta zo gidan su Deeni duk da baya son hakan, baya kulata, haka zata yi ta masa surutu tana masa hira, har ya soma sabawa da hakan. Wataran cikin dabara zata dinga jefa masa magani cikin (juice) ko abinci.
Ganin har yanzu bata samu yadda take so ba tsawon wata uku amma Deeni bashi da niyyar canjawa, don haka tayi niyyar sake canja salo, ta cewa Hajiya tana son zuwa har Kaduna gidan su Deeni inda ya zauna da inda ya yi rayuwa, sannan tana son ganin Farida don mata wasu tambayoyi akan Deeni.
Hajiya ta ce, “Da zai yiwu da na raka ki, to amma ba inda zan iya tafiya in bar Deeni, don haka zan yi waya in sanar da su Shamsu zuwan ki, zan baki cikakken (address) ba zaki fuskanci matsala ba inshaa Allah”.
Ta mike, “Na gode Hajiya da yarda da kuma hadin kai da kike bani”.
Hajiya tayi murmushi ta ce, “Ni ce da godiya, ba abinda zan miki sai addu’a, Allah Ya saka miki da alkhairi”.
Sun rabu akan zata yi kwana biyu kafin ta dawo.
Kwance yake yana ta juye-juye a gado, ya ra same ke masa dadi, tun dazu yake sauraron zuwanta amma shiru. Ya riga da ya saba da tana zuwa kullum dai dai wannan lokacin, amma yau har yamma shiru.
Nan ya mike ya zuge labulen dakin kamar yadda ta saɓa masa, nan ya dinga kaiwa da komowa. Can ya bude kofar dakin ya fita, abinda ya jima bai yi ba tunda ya dawo daga asibitin yana nan a cikin dakinsa.
Hajiya na tare da Alhaji a falon kawai suka ga Deeni ba zata yana leke-leke, a tare suka mike cikin mamaki.”Deeni”.
Suka kira sunansa a tare. Ya kalli Hajiya ya ce, “Mama ba wadda tazo gidan nan yau?”
Kallon sa take cike da mamaki, ta jima sosai rabon da taji Deeni ya kirata balle magana, kuka zata yi ko dariya? Ta rasa.
Ta ce, “Deeni wa kake nema?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Bai bata amsa ba ya koma ciki ya tura kofa ya kwanta, kwanciyar da yaji bata masa dadi, ya mike ya nufi bakin (window) ya tsaya yana kallon motoci da ke wucewa bisa titi.
Zaune take a falo tana jiran isowar masu gidan, yayin da take kallon yadda aka tsara ginin gidan da yadda aka tsara falon. Farida ta iso tare da ‘yan yaranta guda biyu
suna ta tsalle-tsalle Deeni da Aisha, ta tarbi Bahijja cikin fara’a, itama ta amsa tana dariya,suka gaisa.
Deeni karami ne ya gaisheta, ta amsa tare da jawo su tana musu wasa da dariya, tana tambayar su makaranta suna bata amsa.
Farida ce ta ce, “To maza aje ciki ayi wasa a barni zanyi magana da Aunty ko?”
Nan suka yi ciki, sannan ta mai da kallonta kan Bahijja ta ce
“Hajiya ta min bayanin za ki zo, sai dai bata fada mana ko mene ne ba”.
Bahijja tayi murmushi ta ce, “Abu me muhimmanci ke tafe dani, sunana Docter Bahijja kamar yadda na fada miki, ni likitar Deeni ce”.
Jin sunan Deeni yasa Farida taji zuciyarta ta tsinke, hankalinta ya tashi. Nan da nan Bahijja tayi mata murmushi.
“Kwantar da hankalin ki, ba wani abu me wahala ke tafe dani ba, illa iyaka ina so ki taimake ni in taimaki Deeni. Inaga wannan shi ne iya abinda za ki iya masa ki taimake shi, shima ya ci gaba da rayuwa kamar yadda kika ci gaba da naki rayuwar”.
Kanta sunkuye jiki ba kwari ta ce “A shirye nake da in baki kowane irin taimako, zanyi farin ciki in har akwai taimakon da zan iya yiwa Deeni”.
Bahijja ra ce “Naji dadin haka, ina so ne ki fada min komai akan Deeni, ina nufin haleyyar sa, me yake so? Meye baya so? Banda wanda na sani, a ganina kece mutum mafi kusa da Deeni, wacce tasan kananan abubuwa akansa wanda wasu ba za su sani ba. Komai ina son sani, me yafi sa shi farin ciki? Ya yake rayuwar sa? Kamar (Hobbies) dinsa, wane abinci yafi so? Wanne yanayi yafi so? Me yafi sa shi nishadi da farin ciki?”
Farida tayi shiru ta fada duniyar tunani,
rufe ido tayi tana tuno komai a game da shi, tana tuno wasu yanayi da suka yi tare a da. Ta bude ido jikinta a sanyaye ta ce, “Tashi mu shiga ciki”.
Nan ta ja ta sama zuwa bangaren da Deeni
yake, ta bude mata dakinsa, ta kunna wuta haske
ya bayyana, ta ce.
“Ga dakin Deeni wanda ya shirya shi da hannunsa, ina ga ganin wannan ko ban fadi ba zai fahimtar dake ko wane ne Deeni”.
Bahijja tayi murmushi ta ce, “Kwarai dakinsa ya bayyana shi a zahiri, daga (sturdy room) dinsa na fahimci Deeni mutum ne me son karance-karance”.Farida tayi dariya, “Kwarai yana son
karance-karance da binciken takardu tun daga kan na Addini har na boko. Www.bankinhausanovels.com.ng
Deeni ma’abocin ilimi ne, ma’abocin soyayya. Yana samun farin ciki a kananan abubuwa, mutum me son zama cikin dabbobi, tsuntsaye da son kiwon su.
Deeni yana son (spat) yana son (swimming), yana matukar son MISBAH da labaransa”.
Ras! Bahijja taji gabanta ya fadi, ta maimaita.”MISBAH?”.
Ta tambya cikin mamaki.
Farida ta girgiza mata kai, “Kwarai MISBAH (the author) wannan marubuci Deeni yana sonsa da labaransa. (Ideologies) dinsa suna matukar burge Deeni, a kullum in munyi fada da Deeni to akan littafin MISBAH ne, har na dauki litta fansa kishiyoyina saboda ba abinda ke dauke hankalinsa daga gareni sai takardun MISBAH”.
Tana maganar tana bude mata wani (drawer) dake cike da takardun MISBAH, gaba daya ba wanda bashi da shi, daga na Hausa har
na Turanci, daga na labari har na addini. Shiru tayi tana jinjina soyayyar da yakewa
takardunta, ko ita bata da wasu (copics) na takardunta sai dai (original) dake cikin (computer) dinta.
“Lafiya Doctor?”
Farida ta katse mata tunani. Ta girgiza kai, “Ba komai”.
Farida ta ci gaba, “Deeni yana son rayuwa mai sauki, haka nan yana son ganin ya taimaki marasa karfi. Deeni bai dauki rayuwa da zafi ba”.
Bahijja ta kalleta, “Na gode kwarai da
wannan bayanai naki da hadin kai da kika bani”.
Farida ta kalleta, “(Please) likita ki taimake shi”.
Bahijja ta girgiza kai, “Inshaa Allah”. Bahijja bata bar gidan su Farida ba wanda yanzu anihin cikin gidan su Deeni suka dawo tunda suka koma Lagos, sai da ta sa Bahijja ta ci abinci tayi wanka da sallah sannan suka rabu.
Bahijja ta gama abinda take a garin
Kaduna, washegari ta hau jirgi ta koma Lagos tare da sake sabon shiri wa yadda zata tafiyar da Deeni.
Assalamu Alaikum”.
Ta fada lokacin da take kokarin kutsa kai Yana tsaye bakin (window) bai juyo ba, ta cikin dakin.
Ta karasa dab da shi.Deeni sallama nake”.
Nan ya juyo ya kalleta a yatsine ya watsar, sannan ya amsa ciki-ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi murmushi, yau ce rana ta farko da ya
amsa sallamarta. Tayi murmushi, a ranta ta ce, “Wannan
akwai son nunawa mutane isa”.
Gado ya nufa ya kwanta, ya juya mata baya. Ta matsa kusa da gadon. “Deeni abokina ba gaisuwa? Ko fishi kake
dani ne? Sorry”.
Ta kama kunne, “Na tafi na bar abokina, to ai ba laifina ba ne, in na zo baka kula ni, ba ka jin magana ta, ba ka taya ni aiki, shi yasa na daina zuwa. Ina zaune yau a gida sai (mind) dina
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG