MISBAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

olabarin ma?”Ras! Taji gabanta ya fadi.Ya tsarela da ido, “Ina littafin?”  Tayi saurin kau da kai, “Ban sani ba, don
kawai kana neman littafi sai ka wargaza min kaya? To sai ka tattara” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba zan tattara ba”. Ya bata amsa kai atsaye.Ba zan tattara ba, kuma sai kin bani littafin nan”, in naki fa?
In kinki yau bazaki fita a dakin nan ba
Hannu yasa ya danna password din kofar

“Ba zaki fita ba sai kin bani”.
“Deenii”. Ta fada cikin zare ido. “Baka da hankali ne?”
“Bani da shi”.(Please) ka bude”.
“In kina son tafiya ki bani”.
Ya juyo ya kalleta, “Kar ki damu ba abinda zan miki, ni kaninki ne”.
Nan ya dare gado ya hau ya juya mata baya tana ta masa masifa amma bai saurare ta ba. Nan tayi ta kokarin daddanna (numbers) din tana kokarin canka, ya ce. “In kika yi sau uku ba dai dai ba to ko
ansa na dai dai din ma ba zai budu ba, kinga
zama daram ni dake (my sweet) Yaya”. Ya fada cikin zolaya.
Nan ta hau masa magiya har yamma, ta ce masa ta tafi da littafin gida ta manta, gobe zata kawo masa. Nan ma bai kulata ba, nan fa ta hau lallaba
shi lana lallashi, duk wannan bai yi aiki ba. Ta ce, “Deeni in na tafi fa ba zan sake zuwa ba, ka manta sharadin mu zaka dinga jin
magana ta?”Ya juyo ya kalleta, “Maganar ki wanne ne banji ba? Na sha magani, na ci abinci irin wanda kike so, na sa kaya irin wanda kike so, na saurari shawarwarun ki, kullum muna karatu tare sannan yanzu mu abokai ne, surutun da bana yi kinsa na fara magana, tun bana so har na fara so, mene ne baki sani nayi ba Doctor Bahijja… Oops Abokiyata Bahijja?”


Ta daka masa harara, “Akwai abinda ya saura baka yi ba, shi ne kunce abotar mu, daga yau na daina abotar, kuma ta (window) zan fita kaje ka nemi wata abokiyar ta karanta maka labarun, don ba zan baka littafin ba, kuma ko ina zaka shiga ba zaka samu ba”.Me yasa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya bata amsa, “Saboda ke ce MISBAH da zaki hana ni ko kuma zaki ɓoye min labarin.. Sannan batun neman wata abokiyar ba zan iya ba, saboda ko ba komai a tare da ke akwai muryar da take taba mini zuciya in kina karanta min labarin, don kuwa ko shi MISBAH da ya rubuta labarin in yaji yadda kike karanta shi da dukkan (feelings) dinki da (emotions) dinki zai ji kamar ba shi ya rubuta ba.Sannan batun fita ta (window) kuwa Bimillah, iyakaci kugunki da kafarki daya ta karye, iyaka ta in sai miki ayaba da lemo”.
Harara ta galla masa, ta kuwa nufi (window) gadan-gadan zata fita, ya yi saurin fisgota da rigarta.Ta daure fuska, “Ka kyale ni”.
Zuwa yayi ya bude mata kofar, “Fita, kin kira kanki da abokiyata amma ba zaki iya daukar wasa da nake miki ba”.
“Eh bana son irin wannan wasan”. Nan ta sa kai ta fice, ya lura ranta ya ɓaci,
sam bai ji dadi ba. Kwana uku Bahijja bata zo ba, Deeni ya rasa me ke masa dadi? Ya samu sabuwar rayuwa
tare da ita da (company) dinta.
Hankalin sa ya matukar tashi da rashin ganin Bahijja, ya kasahakuri har sai da ya tambayi Mama ina ne gidansu ne A wanne asibiti take aiki? Www.bankinhausanovels.com.ng
Mama ta kalle shi, “Deeni kenan yanzu duk zuwan da Bahijja take gidan nan baka taba tambayar ta ita wacece ko daga ina take ba?”
“Mama ki ban amsa”.”Nima ban sani ba, sai na bincika. Zan tambayi mahaifin ka”.
Ranshi ya ɓaci, ya juya ya koma ciki. Wannan ya bata damar yiwa Bahijja waya ta fada mata halin da yake ciki.
Bahijja ta ce, “Mama ina ga lokaci yayi da Deeni zai soma zuwa asibiti yana shiga cikin ajin da muke musu (lecture da ba da shawarwari, ya kamata ya fara shiga mutane. Munyi mai wuyar, kiris ya ragewa Deeni. Kafin ya samu waraka sai ya daina kebe kansa a gefe”.
Bahijja tayi kokarin janye kanta daga gidan su Deeni saboda tana gani lokaci yayi da zata janye daga gare shi, yanzu ya soma dawowa hayyacin sa. Abu kalilan ne ya rage masa yawan nasiha da masa tuni akai-akai, don haka ta ba da shawarar in yana zuwa daukan darasi a (couseling center) dinsu zai mike.
Mama ta same shi a daki ta mika masa (address) din su Bahijja, ta lura yana cikin damuwar rashin zuwanta, tabbas Bahijja tayi tasiri a rayuwar Deeni.Tunda ya karbi (address) din yake tunanin yaje ko a’a? Haka zuciyar sa da kwakwalwar sa suka dinga tunzura shi da yaje.
Washegari ya shirya ya fita, tunda ya shiga wurin kwakwalwar sa ta dinga tunano masa da abinda ya faru. Hankalin sa yaji yana tashi, yaji kamar ya koma, ya tsaya shi bai shiga ba shi bai fita ba. Wani ma’aikacin wurin ne ya masa magana.
“Malam wa kake nema? Ba a tsayawa a nan, ko shiga ko fita”. Deeni ya kalle shi ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya ce.
“Ina tambayar Doctor Bahijja ne”.
Mutumin ya kalle shi ya ce, “Madam tana can bangaren koyarwa, tana cikin aiki amma ka jira in ta gama zan mata magana, in kuma kana sauri sai ka dawo gobe da wuri kafin ta fara aiki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Deeni ya ce, “In ba zaka damu ba ka raka ni zuwa inda take sai in jira ta a can”.Tare suka jera da mutumin zuwa ciki, suna tafiya yana kalle-kallen yadda wurin yake, da irin jama’ar da ke zarya a wurin.
(Hall) dan madaidaici cike da ne majinyata kuma dalibai, Bahijja tsaye gaban su tana ta bayani, tana ilmantar da su tare da wayar musu da kai, su kuma suna mata tambayoyi tana basu amsa, yayin da ta dinga binsu daddaya tana tambayar su matsalolin su suna fada mata tare da musu misalai da mutane daban-daban. Wani lokaci takan koma tarihin Annabawa, Sahabbai da manyan bayin Allah da irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwa. Don haka ba wani bakin ciki ko ɓacin rai da zai sa ka tsayawa da rayuwar ka bayan kana da Allah da addini, kuma Allah ba Ya baka yadda zaka yi in ka koma ga Alkur’ani, sannan zaka ga kai baka da matsala ma akan tasu ko na wasu.
Allah Ya mana kyautar rai da lafiya ne don mu bauta masa, don samun rabo duniya da lahira, ba zamu samu wannan babban rabon ba sai mun kula da kanmu da lafiyar mu, sannan muji dadin kyautata ibadar mu.Nan ta basu addu’o’in da za suyi na cikin Hisnul Muslim, wanda yake cike da Azkar din da Annabin mu ya yi, kuma ya yi umarni da a yishi.
Deeni ya harde hannu a kirji yana tsaye ya kwantar da kai yana’ jinta da saurarenta, maganganunta na ratsa shi. Hikimar ta na iya zance da iya fahimtar da mutane ya burge shi, iliminta da fahimtar ta yasa shi jin wani sauyi.
Ya zura mata ido yana kallonta yana murmushi, wai da wa wannan likitar ke masa kama? Yanayinta, koyarwar da, hikimar ta akwai inda ya sansu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamar da wasa ta juyo suka yi ido biyu, ta hango shi tsaye gabanta. Nan ta dage kai kamar bata ganshi ba.
Murmushi yayi ya kutsa kai ajin, ya wuce kai tsaye gabanta ya kama kunne. Am Sorry”.
Bata kula shi ba, ya juya ya kalli ajin, “Sannun ku ‘yan uwana dalibai majinyata, wannan malamar ta ku kuma likitar ku nima malamata ce kuma likita ta, na mata laifi na zo bata hakuri kuma nima daga yau zan fara zuwaajinku, ku taya ni bawa malama hakuri na dawo dan uwanku kuma abokin ku”.
Nan suka hada baki suka ce, “Muna maraba da sabon abokin mu”.Suka kalleta, “Malama kiyi hakuri”.
Nan suka sake hada baki suna ta bata hakuri har sai da ta amsa ta hakura, Deeni ya kafa mata ido yana mata dariyar zolaya. Bata kula shi ba har suka tashi ya bita har (office) a nan ya sata gaba yana ta mata naci tayi hakuri.
“Ba zan kyaleki ba kamar yadda ba ki kyale ni ba kwanakin baya, kiji ya fitinar take? Gara ma ki hakura mu shirya”.
Ta kalle shi ba alamar wasa, ta ce. “Mr. Deeni, nan ba gida bane, wurin
aikina ne inda ma’aikata dake ganin girma na da girmama ni, don haka ban son wasa. In har zaka dinga zuwa daukan darasi to ba wasa, muna da (discipline) da dokokin da zaka kiyaye. Ba latti, ba fashi, kuma ba yin yadda kake so”.
Dauke kai yayi ya ɓata fuska, “Bana son (classes) din naki”.
Ganin yadda ya juya ya murtuke, lokaci daya kamanninsa suka canja ya firgita ta, ta mike. “(Please) mana Deeni, ka saurare ni”..
Damuwa ta bayyana karara a fuskarta.
Nan kuwa ya kwashe mata da dariya yana
tsokanar ta.”Na firgita wata”.Deenii”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta fada tana zare ido.”Kai ko, zan kama ka ne”.
Dariya yayi ya fita yana fadin, “Gobe karfe tara na safe (I will be here) ba latti ba karya doka, ba fashi”. Nan ta bishi da kallo tana dariya, har ya tafi ya dawo.
“Zan samu littafin nan ko sunan littafin?” Juyawa tayi bata kula shi ba, ta rufe kofar (office) din. Don haka Deeni ya dage da zuwa kullum ba fashi, haka kullum yana mata nacin labarin nan ko sunan sa, amma bata saurare shi ba, ba irin nacin da bai yi ba har ya hakura. Har (internet) ya shiga yana (searching) sabbin littattafan MISBAHI amma bai samu ba, tun na Karshen da ya sani da ba sunan wani sabo a cikin (list) din litatta fansa.
Abin yana matukar daure masa kai, duk nacinsa da kokarinsa ya kasa samun ko mutumn daya da ya cc ya samu sabon littafinsa.
Haka Deeni ya samu sabuwar rayuwa tare da sabbin mutane da suke tare da Doctor Bahijja, kullum takan musu darasi tayi musu tambayoyi, duk wanda ya ci takan fita da su yawo zaga gari da zuwa ziyarar wuraren tarihi na ilimi. Duk wanda ya warke gaba daya a sallame shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Anan Deeni ya dinga taimaka mata da wasu ayyukan kasancewar sa likita, duk da kwarewar sa da karatun sa bai kai nata ba zama da ita yau da gobe yasa ya fara sabawa da koyon aiki sosai, daga dalibi ya bige da (practicing) da (trainning).
Bahijja takan yi mamakin kokari da nuna kwarewa na Deeni gashi da saurin fahimtar aiki, tabbas da ya jima yana aiki da karo karatu da ba karamin taimako zai yi ba.
A kwana a tashi Deeni ya warware shakuwa da sabo yana karuwa tsakanin sa da Bahijja, sukan wuni tare a asibiti suna aiki tare.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE