MISBAH BOOK 3 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
«Maza ina-so in ja hankalinku a nan, mace wata
halitta ce mai rauni duk hankalinta duk tunaninta
duk shekarunta, wani lokaci
sai ta kwaba maka
wata wautar, ko da kuwa mahaifammu ne mata,
wani lokaci ita mace tunaninta yana takaita ne ahalin da take ciki, musamman in tana cikin bacin rai da fushi, shi ya sa ake cewa,
ba a biye wa mata,
to, ba kullum ne ba a biye musun ba, sai in
ka fahimci suna cikin wani hali dake gusar da
tunaminsu na daidai ko akasin haka, kamar mace in
tana jinin haila to, hakanan ba dalili ma ka ga tana
bacin rai tana cikin fushi, ta ji ranta ba dadi ko
kadan, za ka ga model dinta, sai da lallabi a lokacin
ba a biye matà saboda tana responding to hormones
saboda wannan jini da take, ko kuma mace mai ciki
ita ma wannan sai a hankali, da ma ita jira take a
taba ta, kamar kububuwa, yanzu-yanzu ta ji haushi
ta kufula, abu kankani za ka mata ta hau fushi da
fada, shi ya sa mu’amalar da ake yi wa mace
lokacin da ba ta da ciki daban yake da wanda
tokacin da take da ciki saboda komai kankancin
bacin rai zai shafi abin da ke cikinta, duk yanayin
da take ciki, haka yanayin da yaron cikinta zai
kasance, dan haka maza a kula, sai an dinga hakuri
da mata in muna cikin wannan yanayi.
Wata kuwa tunanin ta na tafiya ne a cikin halin
da take ko wani zargi ko wani tunani da hange da
take sai ka ga duk abin da zuciyarta da tumaninta ya
Raya mata ,shi za tayi kuma duk abin da yazo
bakinta zata fadi dan haka yana da kyau kar a yi saurin daukar hukunci ko hukunta ta a kan abin da
ta yi ko ta ce a ire-iren wannan yanayi.
ban ce ko yaushe ba, amma ka zama mai
lura da halin matarka da yanayin ta a duk lokacin
da aka samu canji to sai ka yi bincike ko ka auna
hankalinta da tunaninta da kuma dalilin da ya kawo
wannan canji kamar yadda ita ma macen za ta
zauna ta karanci halin mijin dan jin dadin zama da
juna da samun maslaha, sai an daure ya zamana
ana kau da kai wataran wani ka ga ya auri mata bila
adadin har ana masa suna auri saki kuma ba wani
halin banza gare shi ba jin dadin zaman ne ya
gagara.
Wanda yake nema bai samu ba, in ka biye haka
kuwa ba za ka taba zama da mace ba ka dinga auri
saki ke nan, soyayya da aure aiki ake musu, a dasata har ta girma da mata da mijin duk aiki za su yi
masa in kin masa gaye kin kyautata masa kin
tsabtace kanki da gidanki tare da biyayya a gare
shi, a nan kin yi aikin aure, haka idan ka kyautata
mata ka jikanta ka tausaya mata ka mata adalci to,
a nan ka yi aikin aure, sai ku ga an samu zama mai
dadi tare da fahita, Allah ya sa mu dace.
Zaune take gaban hajiya kanta sunkuye, alamar
tana so ta yi magana mai muhimanci da ita, mama
ta fahimci haka don haka sai ta fara mata maganar
“yaya dai Farida?” Farida ta sake gyara zama ta ce,
“‘mama da ma maganata da Deeni ne”‘
Mama ta ce
“Deeni kuma, me ya faru?” Farida ta
sake sunkuyar da kai ta ce
“da ma mama kwanaki
da na je Lagos, mun yi magana da Deeni ta fahimta
sosai, ya nuna min har yanzu yana son aurena sai
dai akwai alkawari mai karfi tsakaninsa da Bahijja
na cewa DANGANTAKAR AURE ko wata alaka
ta aure ba zai taba shiga tsakanina da shi ba, dan haka ba zai karya alkawarin da ya yi wa Bahijja ba
har sai in ita ta amince da kanta wannan kuma bamai yiyuwa ba ne saboda ta ce,
“duk ranar da ya
aure ni ita kuma za ta rabu da shi’ shi kuma
HALACCI da Bahijja ta masa a rayuwa lokadin da mu muka cutar da shi ba zai manta da shi ba, ba zai
cutar da ita ko ya karya alkawarin da ya mata a kaina ba.
Ta fashe da kuka tana cewa
“mama na ga
tsananin soyayyata a idon Deeni wanda na jima ina
gani har gobe akwai soyyata a zuciyarsa lokacin da
na ce masa zan yi aure, na ga tsananim tashin
hankali da kishi a idonsa mama ni ma akwai
soyayyar Deeni a zuciyata da tausayinsa dan haka
na fasa aure nabar maganar aure dan ba zan kuntata
wa Deeni ta hanyar sake auren wani ba ko da ba zai
aure ni ba, na zabi in koma karatun da in rungumi
yarana in kare rayuwata a haka dan haka mama na
roke ku kar ku sake min maganar aure.
“Kuma ki taimaka ki yi wa Ummana magana kar
ta sake matsa min da maganar aure.
» Tuni Hajiya
Aisha ta ji bankalinta ya tashi tsananin tausayin
Deeni da Farida ya kama ta.
Saboda me Bahijja za ta hana yaranta abin da
Allah ya halatta musu saboda wani HALACCI data yi wa Deeni a baya, ban taba tunanin Bahijja zata zama mai son kai ba, Allah ya halatta masa yin
mata hudu amma ita ta ce za ta hana ba shi yiyuwa
sam, a da an fi karfina a kan Deeni da Farida amma
ban da yanzu,
“Deeni Allah ya ba ni damar na cika
maka burinka yau dan’uwanka ba ya duniya in
akwai wanda ya fi dacewa da ya rufa wa matarsa
asiri ya rike
“ya yansa da matarsa to kai ne balle
akwai tsananin soyyar Farida a zuciyarka, wanda ni
ce shaidar haka,
ta kalli Farida ta ce,
Ki share
hawayenki ba mai danne muku hakkinku ba wanda
ya isa ya hana ki yin abin da Allah ya halatta na baza ki yi aure ba, Deeni na son ki amma ya zauna da
kuncin rashinki saboda ya faranta wa wata saboda
jin dadin wata zai kuntata muku duka ai ba ita
kadai na haifa wa dan ba, zan samu Alhaji in masa
maganar, za mu je har can Lagos din in samu shi
Deenin da Bahijjan, ki share hawayenki ki soma
shirye-shiryen zama amaryar Deeni
Farida kanta sunkuye tare da share hawayen
karya ta ce,
“To mama na gode, nan Hajiya Aisha
ta mike ta yi bangaren Alhaji dan fada masa abin
da ke faruwa, Farida ta yi dakinta ta fada kan gado
tana dariya tare da dauko doton Deeni tana kallo tace
“Deeni alkawari na maka na yi wa kaina sai na
aure ka duk kuma hanyar da zan bi in shigo in
kwace duk abin da yake da ma nawa ne, Deeni
zuciyarsa iyayansa da duk wata dangantakarsa na
Farida ne nawa ne, ba zan jure wata ta raba ni da abin da yake mallakita ne ba, ni daya zan shigo in
gwada maki maisayina da karfin soyyyar da Deeni yake
min, ki zauna
matayinki
na marainiya
Tsintacciyar mage’ mara asali in zauna a matsayina
na sarauniya a birnin zuciyar Deeni kuma yar dangi
‘yargata, dukkan wani kulawa da attention sai ya
dawo kaina ni Farida na iya kwatar hakkina da ka
danne min hakki, banda yanzu da na dada girma da
wayo ko ta girma da arziki sai na dama kowa a
hannuna, mulki matsayi status power, zai dawo tafin bannuna
Hajiya Aisha ta samu Alhaji Umar, bata boye
masa komai ba, shi ma nasa hankalin ya tashi yace,
“saboda me, in ra’ayinsa ne na ya zauna da
mace daya wannan ruwansa, in ba shi da karfin iya
rike mata biyu ne wannan shi ma dalili ne amma
haka kawai saboda wani dalili mara tushe saboda
matarsa ya ce ba zai auri abin da ransa ke so ba, ni
kuwa a yadda na san dana namiji ne da ya isa da
kansa da gidansa, mace ba dai ta juya shi ba, in yana son yin abu ba wanda ya isa ya hana shi.”
Hajiya Aisha ta ce,
“Mace ke nan, kadan ka
gani daga sharrinta, duk taurin kan namiji ta san
yadda za ta karya shi ta juya shi ya yi yadda take SO.
Alhaji Umar ya ce,
“Haka ne, a da na yi
alkawari ba zan sake shiga harkar gidansa ba, ko
yanke wani hukunci a kansa da rayuwarsa ba
saboda yana da hankalin kansa da tunanin kansa
amma tunda abin ya z0 da haka kuma ya kasance
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe