MISBAH BOOK 3 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
Dama nina rabashi da wannan abin da yake
Alla ya ya ba ni damar maida masa, sai dai kafin in
kai ga daukar wani hukunci ko zuwa Lagos din, sai
na yi magana da shi, na ji ta bakinsa, in ya so sai
mu je ni da ke mu samu Bahijja mu yi mata
magana ta hanyar nasiha da fahimta, ba ta nuna jin
zafi ba ko tsangwama ko nuna mata Farida tamu ce ita ba tamu ba.
“Saboda ni
na yarda
da yarinyar nan da
tunaninta da al’amuranta, ba mace ce mai son
zuciya ba, sai dai kawai kishi irin na mata, dan
haka ina ganin mutuncinta da girmanta kuma ina jinta kamar diyata, dan haka mu bi abin nan a hankali mu fahimtar da ita, ina fata kin fahimce ni
Hajiya Aisha ta girgiza kai na fahimta,
“ba zan
ki ta taka ba, sai dai kam insha Allah auren Farida da Deeni ba fashi.”
Ya kalle ta ya girgiza kai ya ce,
“Dadina da mata
saurin mantuwa da gajeren tunani,”
“miko min
wayata in kira Deeni.
Bata bata lokaciba ta mika masa ya kira shì a
bugu na hudu Deeni ya amsa tare da yin Sallama, yanayim muryansa ya san cewa eh lallai yana cikin
damuwa, bayan sun gaisa ya ce,
“Deeni lafiya ko?”
Ya dan gyara murya ya ce,
“lafiya Baba, ya su
mama?”
“Lafiyanta kalan, da ma munz0 da wata shawara
ce ni da mahaifiyarka, amma fa in ka yarda ka
amince ba lallai ba tilas Deeni, ni ko ina ga mai zai hana ka auri Farida, matar danuwanka da ya rasu
wannan ka ga ka rufa wa iyalansa asiri, haka nan
yaransa ba za su yi maraicin rashin uba ba kuma ba
za su rabu da uwarsu ba, ba za kuma su je agola
gidan uban wani ba tunda Allah ya ba ka ikon da wadata kuma wani abu ne da ton farko ka so Allah bai kaddara ka samu ba, sai yanzu kaga kuma za
ka samu lada har a gun Allah.
Ras! Deeni ya ji gabansa ya fadi, wani tashin
hankalin iyayensa ke son sake jefa shi, da ma
Misbah na zarginsa sannan ga tashin hankali da
rashin fahimtar dake tsakaninsu sannan shi har cikin ransa ga Allah ba ya son Farida, ba ya son
Aurenta, rayuwar auren da ya shirya suka shinfida
shi da matarsa ya fi masa komai jin dadi irin hakuri
da fahimta da Misbala ke masa, irin na yanayin
tsarin rayuwarsa da aikinsa, ba ko wacce mace za
ta iya masa wannan fahimtar da UZURIn ba, sam
shi ba ya son wani rikici ko rudani a rayuwarsa.
Allah ya ce in za ka yi adalci ka kara aure, maganar
gaskiya ba zai iya adalci tsakanin kowacce mace da
Misba ba, koda kuwa Farida ce.
Alhaji ya katse shi
‘Deeni, kana ji na? ya na ji
ka yi shiru?”
ina ji Baba, gaskiya ba dan za ku ce
na muku rashin biyayya ba gaskiya ni dai ba ni da ra’ ayin ko sha’awar kara aure,
su Deeni kuwa
yarana ne duk abin da zan iya yi wa dana ko uba zai yi wa da suma haka zan musu, zan iya dawo
da su gidana in mamansu za ta amince isakanina da
Farida abu ne da ya wuce.
“Zaman lafiya
da kwanciyar hankalin dake
tsakanina da Bahijja ya fi min komai, ba na son
wani rudani ko tashin hankali
a rayuwata.”
Mahaifin ya katse shi da cewa
“Deeni kamar baka
fahimce ni ba, yara ne ba na so a raba su da
uwarsu kuma karsu je gidan wani agola
sadaukarwa ce nake so kayi kuma Farida wata abu ce da ka so kuma kake so.
Baba me ya sa kake son ruda abubuwa ne? ka
na hada da da yanzu, Baba har yaushe za kuna min haka? lokacin da nake son Farida kun hana ni yanzu kuma da na manta da ita na ci gaba da
rayuwata kuna son dawo da ita lokacin da ba na bukata, Baba kubar ni in samu kwanciyar hankali,
da can kun jefa rayawata cikin rudani da kunci,
yanzu ma kuma son sake haka, ba na da bukatar
kara aure ko wata mace a rayuwata in ba Bahijja
ba, don Allah ni ba yaro ba ne yanzu, na san me nake, na san
ciwon kaina, ba na bukatar kuna
yanke min hukunci a kan rayuwata, Baba alkawari kamin tun kwanaki ba za ka sake min shisshigi a rayuwata ba to, ban san me ya sa kake son canza
maganarka ba.
“Don Allah Baba ka bar maganar nan, ku yafe
min, ba zan iya yin abin da kuke so ba.
Bai saurari
me mahaifin na sa zai ce ba ya ajiye wayar, tuni ran Hajiya Aisha ya baci ta dinga ji zuciyarta na
mata, kuna da zafi domin kuwa ta ji duk abin da suke fadi saboda a speaker ya sa wayar wato da gaske ne Bahijja ta mallake mata da tana zaune ba
ta sani ba, ta yadda ta san Deeni na son Farida, wani
abu ne mai wuya a ce soyayyar nan ya tafi har yana
kin aurenta gaskiyar Farida ne, saboda Bahijja ne yake gudun auren Farida, amma ba ta isa ta hana
yaranta da jikokinta abin da suke so ba, tsintacciyar
mage mara asali ta samu wuri, shine za ta hama
wani shiga.
“Farida da Deeni tare da jikokinta za su zauna a inuwa daya inuwar aure gida daya, ni zan je Lagos
din da kaina in samu Bahijja,
ta fada cikin bacin rai tana kallon Alhaji ya ce,
“za mu je tare, amma
mu bi abin a hankalì ba tashin hankali a ciki.
“Na sani Alhaji, zan je in kalli fuskar Bahijja, in
tambayar wa Deeni izinin auren Farida tunda shi ba
zai iya ba, zan ga yadda za ta ki amincewa da
batuna.
Deeni kuwa ransa ya mummmunina baci da
maganar mahaifinsa, yanzu ma yana cikin wani
tashin hankali, meyasa iyayensa kullum suke masa
hakan? Wannan karan ba zai iya musu abin da suke
so ba, ya tuno kwanansa uka ke nan rabonsa da
gida yana ga lokaci ya yi da zai koma su daidaita
da Bahijja, ya kawar da duk wani rashin fahimta
dake tsakaninu saboda ya san dai yanzu kan ta
huce, za su yi magana ta natsuwa da fahimta.
Sun iso Lagos bayan Azahar, gidan suka
wuce kai tsaye, sai dai ba su samu kowa
ba, kasancewar ba su sanar da kowa suma
zuwa ba, su Baba Audi sun masu hidima sosai
kasancewar sun san muhimmancinsu ta ce zata buga wa Bahijja waya, Hajiya Aisha ta ce ta bari
kawai, in sun yi sallah za su je office din su same ta, haka ko aka yi ba su bata lokaci ba suka fita,
abincin da aka kawo masu ma sama-sama suka ci,
suna fita suna
Allah-Allah su je wurin Bahijja
domin sunyi abin da yakawo su.
Sun same ta a office dinta zaune tana duba
report din was marasa lafiya, suka yi sallama da ta
gansu ta mike da sauri ta tare su cikin girmamawa ta musamman
tare da nuna mamakin ganinsu
“Hajiya, kuma haka ba labari ai da na bar zuwa aikin ma da na san da zuwanku.
Hajiya Aisha ta dan yi murmushi,
“ai ba komai
ga shi mum zo gara dai da kika zo ai kinga kin rage aiki.
.»* A take Bahijja ta sa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma. Bayan sun ci sum sha, ta ce, za mu wuce gida saboda ku huta?”
“Ah’a” in ji Alhaji,
“in kin ga mun bar nan to,
mun yi maganar da ta kawo mu,Babijja ta kalle
shi ta ce,
“Baba ai da ba sai kun zo ba, da sai mu
mu je har inda kuke,
Hajiya Aisha ta karba ta ce,
“Ai tunda kika ga munzo to, maganar tana da
muhimmanci ne, gaban Bahijja ya tsinke,
“ba dai Deeni karata ya kai gida ba,
ta fada a zuciyarta
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe