MISBAH BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
Ta mike, «mama mu isa gida ku samu ku huta,
ai wucewa ma za mu yi tunda mun yi abin da ya kawo mu.
«A’ah ba za a yi haka ba mama, mu je gida ku
dan kara hutawa dan Allah.”
***Alhaji Umar ya ce,
“shi ke nan, mu je. » Nan
suka fita tare, suka nufi mota daya wato motar
Bahijja har da Deeni wanda ya tsinci kansa cikin
rikici da rudani har yanzu ba su yi ido biyu da
Bahijja ba, yayin da ya lura ba ta cikin wani tashin
hankali, fuskarta bai bayyana wani tashin hankali
ko rudani ba, alamar bacin rai shin meke faruwa meye a zuciyar Bahijja me take nufi da abin da ta
fadawa mama itama tumaninta daya da mama ne ko
yaya? Itama ta min rashin fahimta ne kamar na mama tana tunamin ina da ra’ayin auren Farida ko
ina son Farida wani irin tunani ne da mata
wani lokaci suyi min rashin fahimta mesa suke son mai da r rayuwa baya? Da wannan tunane
tunanen da maganar zuci suka iso gida da niyar zai
fahimtar da Bahijja bashi da ra’ayi kuma ba wanda ya isa ya sashi abin da bai yi niya ba.
A gida rashin fahimta da sabuwar rigima ya
kara kancamewa tsakanin Bahijja da Deeni duk iya
kokarinsa na ya fahimtar da ita abin ya faskara ta
riga da tayi nisa kuma ta sawa zuciyarta Deeni yaje ya hada ta da iyayensa.
Ransan yayi mummunan baci akan yadda ta kasa fahimtarsa tayi masa wata fassara ta daban ya kalleta ya ce,
“‘aure ne dai bani da niyar yi kuma ba zan
yi ba, ke ko iyayena ba mai tursasani inyi abin da ba naso kuma bani da niya.
Cikin tsawa da daga murya Bahijja ta ce,
“Ya isheku juyamin rayuwa da kuke yi Deeni aure da zaka yi duk wannan nuna min ba kaso da kake ni nasan ka na so na riga da na fahimci komai
sannan maganace wanda ya shafi iyayenka har suka sa baki suna kuma ganin ni na hanaka auren
Farida, ko ni na shiga tsakaninka da farin cikinka
da abin da ka ke so, sannan yanzu kuma in shiga
tsakaninka da yayenka wane farin cikin kake ganin
zan samu a haka kaje ko mata uku ne kayi zai fi
min kwanciyar hankali akan ka zauna dani ka
kasance cikin tsangwama da bacin ran iyayenka ni
Bahijja ban taba shiga tsakanin
wani da farin
cikinsa ba balle kai da iyayenka kunyi man alfarma
sosai a rayuwa da nake ganin ba zan baku tukwici da bacin rai ko shiga tsakaninka da iyayenka ba
kishina soyayyata komaì a a kanka na cire.
Haka takunkumi da nauyin alkawari da ka daukar min na janye na hakura da komai kaje kayi duk
yada ka keso da rayuwarka ina tare da kai bana fada bana fushi bana kuma adawa da aurenka da
Farida kaje kayi bin da Allah halatta maka kuma zan faranta ranka da na iyayenka ko ba komai a
yau na sauke nauyin alfarmarka da kai da iyayenka
a kaina bani da iko ko wani dama akan rayuwarka
sai tawa rayuwar kuma daga yau dinnan yanzunnan
zan fuskanci rayuwa ta ce,
“‘in sauke nauyin aure
da Allah ya daura min maganar aurenka ko Farida bazai sake zama wani issue a tsakanin mu ba.
“Ina maka fatan akhair Allah ya bada zaman
lafiya in har ina da wani sauran mutuni ko daraja a
idonka to ba zaka yi abin da zai jawo min bakin
jinni ko wani gaba a wurin iyayenka ba, in kayi
haka ka dau hakkina saboda a yanzu har ga Allah
har cikin zuciyata bani da matsala da aurenka da Farida ko wasu yammata.
Tana fadi tana tattara kayanta da ke dakin
Deeni tana gamawa ta sa kai ta fita ta nufi nata
dakin tana gyara zaman kayayyakin.
Deeni kansa ya dau zafi sosai Bahijja ta caja
masa kai da tunaninsa a yadda ya lura ya kuma fahimci tamkar babu sauran soyayyarsa a ranta baya gabanta kuma bata da abin da za tayi
da shi baya gabanta tana masa kallon maci amana mayaudari ba sauran yadda a tsakaninsu dan haka
bashi da abin da ya wuce ya kyaleta kamar yadda
take bukata dan idan har ya tada nasa fushin bacin
ran da zasu fuskanta ba zai musu kyau ba duka dan baka ya yanke hukuncin fita harkarta haka nan
yadda ta keso tace ita da iyayensa haka za’ayi
kowa yana da dama yayi abin da yake so akansa
iyayensa da matarsa amma shi da yake rayuwarsa ce ba wanda ya bashi dammar yadda yake so da
rayuwarsa kowa son kansa da son zuciyarsa kawai yake biye mata dake bawa ko wani da namiji natsuwa da kwanciyar hankali shi yau ya rasa shi gaba daya yaji rayuwarma ta fita masa a rai dan
wannan bashi ne rayuwar da ya so kuma ya zabawa kansa ba.
Amma ya tsinci kansa ciki ya samu iyayensa a
masu san kansu kafin ma ya ce wani abu mama tace,
‘”mu zamu wuce ba zama muka zo yi ba wani
hukunci ka yanke kuma wani lokaci ka yanke”? ya tsuguna gabanta ya ce,
“duk hukuncin da kuka
yanke da duk rana da lokacin da kuka tsayar daidai ne
Tayi dariya jin dadi, tare da fadin “Allah ya
maka albarka ka sanya tsohuwarka farin ciki ta kalli mahaifinsa ta ce,
“Alhaji yau ina cikin
tsananin farin ciki Allah ya cikamin burina na
gain auren Deeni da Farida yau burin dana zai
cika zai mallaki abin da ya fiso a rayuwarsa sanna ya yan dan’uwansa Shamsa zasu
rayu giddan
ubansu da zuri’ arsu ba zasu yi maraici ba, suma tare
da uwarsu da ubansu saboda da Deeni da Shamsu
duk abu guda ne, Allah ya maka albarka”
“Ameen ya fada murya kasa kasa yana kallon
mahaifiyarsa tana cike da farin siki a ransa ya ce,mama kin san wani hali nake ciki ko me na keji a raina da zuciya ta da abin da nakeso da baki kira wannan da burina ba Farida ba burina bace aurenta
bashi nake so ba, ba shine farin cikina ba asalima
shine dalilin rushewar farin cikina ba zan sammu farin ciki da kwanciyar hankali ba haka Misbah zata ci gaba da min kallo mayaudari maci amana
wanda ya karya alkawari.”
Mahaifinsa ya zura masa ido ya so ya fahimci
yana cikin damuwa ya ce,
“Deeni lafiya ko ko dai
akwai wani abu”
Yayi murmushi ya ce,
“ba komai in kun shirya
taliya (driber) zai kaiku (Airport) ni kaina na ciwo
ina son in kwanta ba zan samu dammar kai ku ba sannan duk lokacin da kuka tsayar na daurin aure
sai ku sanar dani zanzo daurin auren sanna in ta yanke hukuncin zama a nan to ga can bangarenta
za’a gyara a zuba mata komai ba sai an hado mata
wani abu ba sanna Kaduna ma duk abin da take so
za’a sa mata sai ta zabi daya cikin gidajan banda
na Bahijja yana da kyau kowa ya zauna a gidanshi.
Hajiya taji dedin maganar Deeni sosai duk
bacin ran da tazo da shi sai da ta nema ta rasa ta
dinga masa godiya tana sa masa albarka yayi
murmanshi mai tatare da bacin rai ya ce,
“bakomai
mama ai Farida kanwa tace komai zan iya mata.Nan suka yi sallama zasu tafi ya ce mama bakuyi sallama da Bahijja.
‘” ba tayi dariya ta ce,
“kaga duk farin ciki yasa na manta.
ya kalle ta tare da fadin
“yana da kyau ki ringa tuna baya kar kuma
son kai da son zuciya yasa mu manta da wacce ta
ke tare damu lokacin da muke cikin kunci da
tsanani yin hakan butulci ne.
Hajiya Aisha ta kalleshi tare da girgiza kai ta ce,na fahimta.Bahijja da ke tsaye daga gefe nesa dashi kadan ta matso inda suke duk abin da suke fadi taji sai dai tayi kamar bata jisu bata kalli
Hajiya tana murmushi ta ce,
“zaku wuce”?
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe