MISBAH BOOK 3 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
Hajiya ta fadà tana kallonta tana dariya ta ce,
“na gode Bahijja da hadin kai da kuma fahimtar da kika mana komai yazo cikin sauki son da kikewa Deeni
da kuma girman da kika ba mu matsayin iyaye kin cikawa Deeni burinsa na auren abin da yake so yake muradi, da Deeni da Farida basu da burin daya wuce na su mallki juna, mukuma iyaye ba mu da burin da ya wuce burin yayanmu wannan
sadaukarwa da kikayi Allah ya baki ladansa ya rufa maki asiri duniya da lahira.Ta yi murmushi tare da fadin “Ameen. tausayin
kanta taji ya kamata ta tsinci kanta cikin wani irin kewa da raunin zuciya duk karfin hali irin nata sai
da taji kuka mai karfin gasket yazo mata abin da ta tsana ke nan tsintar kanta cikin wannan yanayin
duk da ta san ita marainiya ce karo na biyu ta sake tsintar kanta cikin maraici ta so kai su Airport
amma ta gagara da kyar ta iya tsaida kanta tayi
musu sallama tare da musu shatara na ariki kamar yadda ta saba ta rakasu har mota sannan ta dawo
ciki ta nufi dakim Baba Andi ta sameta zaune kan sallaya tayi jigum dan kuwa itama tasan meke
faruwa Deeni ya fada mata ko za tayiwa Bahijja
magana ko za ta saurareta dan tana jin maganarta donta dauke ta tamkar mahaifiyarta.
Sai dai Baba Audi itama tabi bayan Bahijja
saboda ta naga hukuncin data yanke shine daidai
dan haka tana jin tashin hankalin Bahijja tamkar
nata tashin hankalin, Bahijja ta fada kan cinyar
Baba Audi ta fashe da kuka mai karfin gasket Baba Audi bata tsaida ita ba yana da kyau tayi kukan ta samu saukin
abin da takeji a zuciyrta. sai da tayi kuka mai isarta
sannanta mike ta kalli Baba Audi ta ce,
“Baba Audi
na gode da kika bani wanna damar har na samu cinyar da zan kwanta inyi kuka na samu wacce ta
tayani jin zafin da nuna damuwa dani da halin da nake
ciki?* Baba Audi ta share hawayenta ta ce,
“in ban damu
da ke ba Bahijja dawa zan damu? Kina marainiya baki da kowa, ni da nake bani da da ba jika sai dangi wanda suka jima da ya dani saboda na zame
musu kaya gashi bani da komai sun gaji dani da talauci na da yasa ko nemana ba sayi dan haka ni da ke muka zamewa juna
‘yan’uwan juna a
musulunci kin darajani kin mutuntani fiye da tunani na ko yata ba za ta min abin da yafi haka ba.
Bahijja ta share hawayenta tayi murmushin
bacin rai ta ce,
“Baba Audi kin san a rayuwar nan
akan mutum irin kamar mutum
yayi maka alfarma a rayuwa har ya zame maka
nauyi da kaya akanka ka rasa dame zaka biya su zama da wannan nauyin abu ne mai wuya dan haka
yau na samu sauki, kauna soyayyata da iyayen Deeni da
“yan’uwansa suka nuna min yau na
biya su alhamdulillah ina da abin da zan iya biyansu da shi so da Deeni ya nuna min darajar aure da ya bani yau na biyashi da abin da ya fiso a rayuwa da
Deeni ina ganina kullum cikin shaukin Farida da begenta amma saboda ni yaki aurenta, Baba Audi
ba zan iya rayuwa haka ba ina tare da miji amma
Kullum hankalinsa nakan wata ko yana tunanin
wasu daban wannan ba nasara bane a tare dani sai
faduwa wannan ba ci gaba bane ci bayane a tare dani.
Deeni ya auri Farida da duk yan matan da yake
so yake muradi yake buri shine nasara ta ya samu
duk abin da yake so yake bukata abin da iyayensa
da sauran yau uwa ke son masa suke bukata dan haka yau bani da wani sauran nauyi ko fargaba ko
tashin hankali a gabana yau din nan yanzun nan shine rana lokaci na karshe da zan yi kuka in zubar da hawayena akan
Deeni da aurensa ko Wata
rayuwarsa da bata shafeni ba.
Haka nan ba zan sake yin rauni ba akan Deeni
ko wata soyayyata zan fuskanci rayuwata tare da ci gaba da yin abin da zai bani farin ciki da kwanciyar
hankali wanda Deeni baya daya daga cikinsu ni kuma na iya cire duk abin da ke kuntatamin zuciya
da rayuwa a raina soyayyar da za ta sa maka kunci
bacin rai da tsana da jin zafi a zuciyarka da
Rayuwarka ba soyayya bace, baka da abin da zakayi da wanna soyayyar dan haka duk wani
shauki ka watsar da shi ka cireshi a zuciyarka da rayuwarka shine daidai.”
Baba Audi ta katse ta “Bahijja karki yankewa
kanki hukunci cikin zafin zuciya da rashi fahinta”
Ta yi wani murmushi na takaici ta ce,
“Baba
Audi nasan Deeni na fahimceshi na karance shi fiye da yadda yasan kansa zaman lafiya nake nema wa
kaina wannan kuwa shine zaman lafiyata ba zan kuma biyewa son zuciyata ba, duk yadda tayi dani
sai nafi karfinta da yaddar Allah.”
Tana gama fadi ta mike Baba Audi zan je in
kwanta sai ku shirya mana abinci yau dai kaina na
ciwo ba zan samu leko kicin ba, dan Allah ina so ki
tsaya kisa ido akan abincin Deeni kin san yadda
muke shirya masa komai in ya so sauran kowa ya
da fa abin da ya masa Baba Audi ta amsa mata da
to tare da binta da kallo tana mamakin halayya da
kar fin hali irin nata tana mata addu’a Allah ya
kawo mata sauki a zuciyarta ya kuma daidaita
tsakaninsu.
Deeni dake tsaye a kofa yana jinsu ya din gajin
kalaman Bahijja tamkar tana watsa masa wuta tabbas yasan,,,,,,cikin gidansa
da rayuwar
aurensa me dadi yazo karshe ya rayuwa zata
kasance bai sani ba kin sauke nauyin da ke kanki
kin cire Deeni a zuciyarki shin ni kuma ya zan yida nawa nauyin da ke kaina da ke da ke cikin
zuciyata da rayuwar da kuka zaba min keda
mahaifana yazanyi cikin rashin fahimta?
Deeni na na tsaye yana maganar zuci har Bahija
ta fito ta wuce shi amma tsabar zafin zuciya bata ma lura yana tsaye a wurin bata wuce shi kamshin
jikinta yadawo da shi hayyacinsa ya bita da kallo ta
rikide ta zama wata abu daban tamkar ba Misbah
dinsa da ya sani ba kuma yarasa meyasa ya kasa
kyaleta yana kokarin kawar da rashin fahimta
amma kuma abin sai karuwa yake alamura sunyi nisan da bazasu warware ba.
Dakinta ta nufa tayi alwala tare da daukar
Littafi mai tsarki ta karanta tare da yin addu’a sanna ta
dauko magani tasha bata jima ba kuwa barci mai karfin gaske ya dauke ta har bata san inda take ba
wanna ya bawa Deeni dammar shigowa dakin ya
jima tsaye yana kallonta yana jin tsananin son ta da
kaunarta ga tausayinta a zuciyarsa ga kuma jin
haushinta duka suka hadu masa lokaci guda tare da
tsananin sha’awarta ya lura ta fada ta rame saboda
damuwa nan yaji yana son rungumarta a jikinsa ko
ita ba taji sauki ba shi zai ji saukin abin da ya keji a
ransa yasa hannu ya dauki maganin da tasha
maganin barcine mai karfi wanna ya tabbatar masa
duk taba ta da zai yi ba za taji ba.
Hakan yasa ya matsa dab da ita ya zauna tana
kwance yasa hannu ya dagota ta sauke numfashi
hade da ajiyar zuciya yanajin tsananin shaukinta
na shigarsa hakika bashi da wani shauki ko farin
cikin natsuwa da kwanciyar hankalin daya wuce
wannan me ya faru ne tsaninmu Misbah na? me ya
jawo mana zama cikin wannan yanayi ina sonki
Bahijja ina tsananin bukatarki please karki kyaleni
karki cireni a zuciyarki karki cireni a rayuwarki
zan iya jure komai amma banda nuna min rashim so
Da kike yi, wannan halin ko in kula da ki kike nuna
min yana min ciwo fiye da komai Bahijja ni me
sonki ne ban taba yaudaraki ko maki karya ba.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe