MISBAH BOOK 3 CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

To yana da kyau zan je inji dadin rayuwata ko da ke ko bake tunda shedan ya riga da ya gama maki huduba,ya juya maki tunani kin makance ba kya ji bakya ba gani sai abin da zuciyarki ta fada maki, ki je duk

yadda kika dauka haka ne,ki na jin Deeni ba zai iya jin dadi ba, ko Rayuwa ba sai dake ba mu je zuwa tunda haka kika zaba.

Ta yi murmushi tare da fadin to menene na fushi kana daga murya

zaka iya maganar ka a hankali ba sai ka daga

murya ba, ni na tafi nan ta juya ta wuce ta tafi ta kyaleshi cikin mummunan bacin rai daga karshe ya tashi ya shirya ya fita haka nan.

Misbah ta isa asibiti ta ci gaba da aikinta sam

bata bari ta zauna balle wani damuwa da tunani ya shigeta ba. haka nan ta dage da addu’a ba dare ba rana duk wani addu’oi na yayewar bakin ciki da bacin

rai ba a rasa shi a bakin ta, wani lokaci takanyi

kuka taji sanyi a ranta a duk lokacin da bata ganin Deeni takan manta da shi yayin da ko muryarsa taji sai taji wani mummunan bacin rai maci amana,mayaudari me karya alkawari shine sunan da ta bashi take kuma kallonsa da shi.Haka ta bangaren Deeni ya tattara Bahijja ya watsar da ita aikinsa yasa gaba sai dai duk iya kokarinsa wani lokacin yakan tsinci kansa cikin tsananin kunci yadda rayuwarsu ta rikide ta dawo wani irin rayuwa mara dadi mai cike da kunci da rashin fahimta. Haka rayuwarsu ta kasance ba wani walwala ba farin ciki ba jin dadin aure ko kadan,har akayi daurin auren Deeni da Farida amarya ta tare yayin

da “yan’uwanta da Deeni suka hadu suka rakota kowa na nuna farin cikinsa.

Bahijja ba tayi kasa a gwiwa ba ta taresu tare da musu hidima matsayinsu na

bakinta,kwanansu biyu tana musu hidima wanda ta,nuna bata ma san kishiya ake mata ba wasu maganganun ma da ake jifan ta dasu ita bata san suna yi ba dan ba sanin hakan tayi ba kuma ba sabawa da hakan tayi ba asalima in banda gaisuwa ba abin da ke hada su ta wuce aikinta bata dawowa sai dare.

Nan ma tayi musu sai da safe ta shige bangarenta ba zama cikinsu take ba dan ba sabawa tayi da hakan ba,dukkan ruyuwarta bata da wasu kawaye

irin wannan balle a ce tasan wani hayaniya ko

hargowar biki ko wani bakar magana ita ba dangi ba balle tasan irin wannan.

Dan haka duk maganar da suka jefeta da shi ma duk a banza ba tasan ma da ita suke ba dukkan rayuwar ta ya kare a

karatu,bincike,aiki ko dai

wani taro na karawa juna ilimi,sai asibiti sai kuma Rubuce-rubuce bata da abokan da suka

wuce wannan ko wani hidima hakan nan tayi rayuwarta da Mislihu rayuwarsu iri daya hakan nan tayi rayuwarta da Deeni kowa harkarsa yake dan haka

suka gama gutsuri tsomarsu da iyayensu suka tafi ba ta masan sunyi ba. Hakan nan rabonta da tasa Deeni a ido tun da suka yi maganar sai dai ta tsinci muryarsa, ko taga wurgawarsa shi ma haka wanda

dukkansu a wannan lokaci basu da bukatar ganin juna.

Bayan yan rako amarya sun watse akabar Farida da wata mata adanginsu can akasamota ta dunga mata wasu aikace aikace tare da kula da yara.

Deeni bai tako kafarsa agidan ba har sai da akai sati da kawo amarya

wanda hakan ba karamin

konawa Farida rai yayi ba tadauki laifin duk ta

dorashi, kan Bahijja duk da kuwa tana ganin shiga da futan Bahijja agidan,rannan da yamma liss bayan ta dawo daga aiki ta tareta ina kika boyemin

mijina,Bahijja tayi mata wani irin kallo ta girgiza kai ta watsar da ita,tasha gabanta malama dake

nake ina kika kai min mijina duk mufurcinki da

kulle kullenki bai hana ni auren Deeni ba wanda daman nawane kika samu aronsa.

Bahijja ta kalle ta ce,kiyi a hankali Farida irin

wannan daga hankali ai sai yasa maki hawan jini ko ki samu tabun hankali, mijinki kuwa ban san inda yake ba kina iya zuwa kikai report gurin yansanda su nema maki shi idan ni bani da power din dazan iya nemo mijinki sannan maganar mijinkine dama na yarda kije na barmaki shi gaki gashi Allah ya bada zaman lafiya za ta sake wani magana

Farida tayi saurin tsai da ita da hannu ta ce.

‘ah Farida karki kuskura ki sake fada min

wata magana in bata arziki bace ban iya hayaniya ba da hayagaga kada ki sake tako bangarena in ba alkhairi ya kawo kiba,ta kalle Baba Audi ta ce”Baba

Audi in sun fita kisa mun key a kofan nan ta shiga ciki. Farida ranta yayi mummunan baci ta kalli me aikinta ta ce,

“Sabuwa kin ga tsintacciyar mage

tana mana wani gadara wai a rufe mata kofa to dawa take gadara in ba Deeni ba to Deeni nawa ne,nawa ne na kwace shi,danginsa ma nawa ne wa take da shi me take da shi banza mara asali.” Sabuwa ta ce

“Abin kunya tsabar bata da asali

kishiya za’a mata,amma bata da wanda za ta

gayyata su tayata jaje da danne kirji, wayasan

dauda da kazantar wani kwatamin ne aka kwaso.Baba Audi tana tsaye tana jinsu tana kallon ikon

Allah, suka gama surutansu suka juya sai Deeni suka gani gabansu yanayinsa yasa

gabanta faduwa yayin da sabuwa ta sha jinin jikinta sai dai Farida ta dage ta wayence ta nufe shi da wuri za ta rungume shi ta ce

“Haba Deeni ina ka shiga ka bar amaryarka cikin kewa a nan”? Yayi saurin tsai da ita ganinsa awurin yasa Baba Audi shigewa ciki,ya kalli Sabuwa ai dai nan ba gidanku bane ko? To ina so gobe da sassafe ki bar min gida,koda wasa kar in bude ido in ganki a gidana.  jiki sumi-sumi ta bar wurin. Farida ta

hau mita haba dan Allah kula dasu Deeni fa zata taya ni.ya mata wani mugun Kallo da bata taba gain ya mata ba ya ce,

‘”‘su Deeni ‘ya’ya na ne Hakkin kula dasu a wuyana yake Inke matsayinsu na mahaifiyarsu baza ki iya kula dasu ba ki kyaleni da nauyin kula dasu,abu na karshe ina son magana dake kije ki jirani a falo na juyawa tayi ba tare da ta bashi amsa ba ranta a bace

ta isa falon tana huci wai anya wannan Deenin da ta sani ne mutumin da ko kallon banza baya iya mata a baya ko ita tayi laifi shine mai bata hakuri yau an wayi gari Deeni ya juya mata baya shin da gaske Deeni ya daina sona? A lokacin dana ke jin sabon sansa a cikin zuciya Bahijja ba zan bari ki kwace soyayyar da Deeni ke

min ba zan yi fada akan soyayyata da right dina ko ta hanyar tsiya ko arziki wani cin mutunci ya wuce ayi aure ango sam baya dakina amarya balle sha awarta hawayen bakin ciki ne ya gangaro mata ta

fashe da kuka.

Deeni kuwa dakin Bahijja ya wuce kai tsaye ya

same ta kamar kullum ya sameta gaban laptop tane danne-danne

gyaran murya yayi

sannan

yayi

sallama bata dago akai ta kalleshi ba amma ta amsa sallamar saboda har cikin zuciyarta bata da sha awar kallon Deeni a halin yanzu ya daure ya iso inda take ya ce,

“ina so kizo falo na akwai maganar da za muyi

Ta amsa masa da

“To” ta mike tare da dauko

hijabinta. Ta lullube jikinta kasancewar sai an fita waje an tsallake masu gadi da sauran ma aikatan gidan kafin aje falon Deenin dan kuwa tuni suka raba bangare da Deeni.

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE