MISBAH BOOK 3 CHAPTER 19 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 19 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Shi yayi gaba tana binsa a baya ba tare da kowa yace wa kowa kala sun samu Farida zaune kafa daya kan daya tana karkada shi sai shan kamshi take Bahijja ta kalle ta ta watsar sannan ta nemi wuri nesa da ita sannan ta zauna,shi ma zaman yayi ya

tsinci kansa a tsaka mai wuya shi namiji ne da baya saurarawa, ba mace ba wani ma bai isa ya juyashi ba a yau an wayi gari mahaifiyarsa da matan sa biyu sun jefashi cikin wani hali da bai taba tunani zai shiga duk da hakan kuma kowa laifinsa yake gani musamman Bahijja da yake gani wani irin tsana a idonta tamkar bata taba sonsa ba. Wayarsa ya ciro ya kira layin mahaifiyarsa bata lokaci ta dauka suka gaisa sannan ya ce mata kamar yadda kika umarce ni na hadasu duka zan

bawa Bahijja kuyi magana in kun gama se in bawa Farida nan ya mikawa Bahijja wayar ta karba tare da yin sallama ta gaida mama cikin girmamawa ta amsa. Ta shiga sauraron fada da nasiha akansu zauna lafiya kuma tayi hakuri da duk wani abu da za ta ga

Farida tayi ba dai-dai ba tunda ita ce babba sai ta dinga mata gyara nan ta kare maganar nata da addu’ar Allah ya bada zaman lafiya Bahijja ta amsa da amen sannan ta mikawa Deeni ba tare da ta kalleshi ba ta mike za ta tafi ya tsaida ita. Ban gama magana dake ba” hakan yasa ta nemi

“‘wuri ta zauna tana jin zuciyarta na ta tafasa dan in kwai wanda jininta yaki gani a wannan lokacin bai wuce Deeni ba ko muryarsa ta tsani ji da duk wani abu da ya taba faruwa a tsakaninsu mai dadi ko mara dadi ta

tsani, tunoshi ita kallon

mayaudari, munafiki maci amana take masa, da kyar ta daure har Faridan ta gama waya da mama. Sannan ya kallesu duka ya ce,

“abin da ya faru ya faru kuma mutum baya wuce kaddararsa da abin

da Allah ya rubuta ma ko ina so ko bana so Allah ya kaddara ya rubuta ku duka biyun matana ne.”

“Ina muku nasiha da kuji tsoron Allah ku zauma lafiya ba cuta ba cutarwa ke kina aikinki da asibitinki ke kuma karatu zaki fara dan haka ina so daga yau din nan mu shifida sabuwar rayuwa, mu manta

da baya ko da wasa Farida ban yadda ki dinga min zancen baya ba ko kina wani nuna isa da gadara akan soyayyarmu ta baya kamar yadda baya ta

wuce ba za ta sake dawowa ba haka wannan babin na rayuwarmu ta baya ya wuce kuma na mance da shi hasalima ba wannan ne dalilin aure na dake ba,iyayena da Bahijja sune silan da yasa na aureki Dan haka in akwai wani tunani na daban ma

akanki ki cireshi mu zauna lafiya a gidan nan raina Bahijja ko fada mata magana da nuna mata warinta

kaskanci yakan iya jawo maki mummunan fushi a kaina ban yadda ki raina min mata ba ko da wasa ya juya kan Bahijja da ta juya kai tamkar bata jinsu ya ce. Bahijjah Allah ya baki girma sannan ke macece mai halin girma ina fata zaki manta da duk abin da

ya faru a baya ki daure ki yafe ki manta da shi mu dauke shi hukunciN Ubangijinmu, Farida tana Kasanki ki dinga hakuri idan ta yi maki kuskure ni nan nayi alkawarin

kare maki mutuncinki da martaba duk wanda ya taba Bahijja na ba zan kyale

shi ba Ta girgiza kai tare da fadin’

“na ji na gode abin da ya wuce ya Wuce.

Ya ce Alhamdu lillah kamar yadda addini ya

tanadar zan yi kwana uku tare da Farida daga nan sai ku fara raba kwana daddaya ko bibbiyu ko uku-uku duk wanda kuka yanke.”

Farida tayi carab ta ce,

“kwana bibbiyu kuma

ta kaina za’a fara ma’ana in ka gama kwana ukun ka wurina sai ka fara biyun a wurina,sannan ka koma kayi biyun.

Tuni Bahijja ta runtse ido tana tuno kalaman

mayaudarin maci amana Bahijja na maki alkawari fatar jikina bazai taba gogan na wata mace ba sai matata Bahijja zuciyata baza ta taba shauki da sha’awa ko muradin so wata ‘ya mace ba sai ke kadai,idona bai iya kallon wata mace da sunanso haka nan zuciyata cike take da so da kaunarki ba sauran

wani fili da zan iya bawa ya mace.

Wani gululun bakin ciki da bacin rai taji ya tokari zuciyarta me yasa kaimin karya ka yaudare ni tun farko da ka fada min gaskiya dana kwana da shirin wannan amma ka min karya da dadin baki dan

kawai ka yaudareni in aureka.Muryar Deeni ya dawo da ita daga tunanin da ta

fada ya ce,Bahijja ke muke sauraro kece babba zaki yanke hukunci ba Farida ba. Ta yi murmushi ta kallesu duka a duk lokacin

da tayi irin wannan murmushin yakan daga masa hankali saboda yasan za ta kwaba tsiya ke nan, ta kallesu duka ta ce

“in dai nice me yanke hukunci

kuma zaku amince da duk hukuncin da na yanke to ku saurari nawa ra’ayin da hukuncina,

Ni dai a matsayina ta babba wanda kuka bani

damar na yanke hukunci,to hukuncin da na yanke shine cewa ni Bahijja a cikin hankalina, kuma ba wanda yayi min dole sai don ra’ayin kaina da kuma

jin dadi da kwanciyar hankalina da gamsuwa ta na yafewa Farida dukkan kwanakina na yafe mata kai HAR ABADA, na maka alkawarin kame kaina da

sha’awata zan tsare maka amanar aurenka da

mutuncinka.

Hakan nan zanci gaba da maka biyayyar aure

insha Allah ba zan gaza ba,sannan magana ta

karshe ina so ka gayawa matarka ni ban iya tashin hankali da hatsaniya ba,idan za ta zo wurina mu yi gaisuwar arziki to bismillah idan kuma fada ne da bakar magana da hatsaniya zai dinga kawota tayi

zamanta a bangarenta ina nawa tana nata,kowa yayi harkarsa inuwar aure ya hadamu dan haka

zamu yi ibadar aure in sha Allah” tana gama fadin haka bata Bata lokaci ba ta mike ta fice wani irin gululun bakin ciki Deeni ya ji ya tokare masa kirji wai tsanar da Bahiija tayi masa har ta kai ta sallamani gaba daya wato bani da amfani gaba

daya a gareta ? Shi ke nan mu je zuwa tunda in haka ta zaba ni mai iya zama da ita haka ne idan bata da abin da za tayi dani nima ba abin da zan yi da ita.A fusace ya mike ya

bar falon Farida kuwa duk dadi ya ta mike ta

fita, Deeni ya zama mallakinta ita daya

Bahijja dai sunace kishiya,haka nan Deeni bashi da zabin da ya wuce. ni dan kuwa nice nan uwar

yaransa zan cika masa gida fal da yara wanda

wannan zai taimaka min in mallake Deeni zuri’arsa da komai ma nasa.

Dan haka fitar da yayi a fusace bai bata haushi ba sai mikewa tayi tabi shi tana iyayi da rangwada gashi dai tayi kyau amma duk haushinta sai ya kamashi yaji bata birgeshi ita ce silar kawo rashin fahimta tsakaninsa da Bahijija saboda ita Bahijja ta

tsaneshi tsanar da har ta kan bata ko iya kallonsa balle ayi maganar kwanciyar aure, wancan rayuwa mai dadi da suka a baya da Bahijja ta zama tarihi.

Tunda Bahijja ta koma bangarenta ta wuce

taki ta haye gado tayi kokarinta tayi kuka amma ta gagara sai azabar zafin zuciya da kunar zuci tare da

jin tsananin haushin Deeni da kinsa a

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE