MISBAH BOOK 3 CHAPTER 22 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 22 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
ta daga masa murya ta kai ta ga kwasar zunubi a banza. Bai hakura baya sake janyota jikinsa ya ce Haba Misbah na nine fa Deenin ki.
Hakan ya fusata ta ta mike da sauri kamar wanda ya dona mata wuta ta ce
Don Allah ka rabu da ni niba Misbah dinka banene ni Bahijja ne ka daina kira da wannan sunan Misbah ya mutu tare da mai sunan, Misbah bata (existing) ta fashe da kuka tana fadin nayi nadamar ranar da Misbah ta hadu da Deeni da ina da hali ko iko da na share wannan yanayin a rayuwata. Tuni ransa yayi mummunan baci ya dinga jin zuciyarsa na ta fasa ya rasa da wata kallama zai yi mata amfani wajan yin magana idan sa suka yi jajajur ya ce Idan har kina nadamar sanin Deeni to zaman me kike yi da shi me kike yi a rayuwar Deeni da gidansa har yanzu. ya fada cikin tsawa da daga murya.
Ta kalle shi idanunta babu tsoro ko shakka tace,zaman aure ne zaman ibada wanda Allah ya kaddara min ya kuma rubuta min zan wannan zaman a karkashin inuwar auranka wannan wani abu ne da Allah ya rubuta min tun kafin kazo duniya don haka na yarda da kaddarata na yarda kai Deeni kaddarata ne. “kafin ya bata amsa Baba Audi tayi sallama ta shigo ta ce,Hajiya fana jiranki.Sai a lokacin ya tuna mahaifiyarsa ce ta zo ta ce
ya kira Bahijja tana son magana da ita,nan ya kalli Baba Audi ya ce kice tayi hakuri muna zuwa.Nan Baba Audi ta juya shi ma ya bi
bayanta.nan Bahijja ta yi sauri shiga bayi ta wanko fuskarta tare da gyrawa don kada a gane tayi kuka sannan ta zari Hijabinta ta fita falon tana ganin mama ta kirkiro murmushi tana mata maraba tamkar bata cikin wani
damuwa ta zauna gefen nata.tana fadin mama ki yi hakuri ya samu ina wanka ne ban san ke bace da tuni na fito. mama ta yi murmushi ta ce ai babu komai na
samu Baba Audi muna ta hira daman a tsai tsaye na zone mu yi wata magana da ke ne duk da dai maganar tsakaninmu ce kuma shawarace sai dai ina ganin zan iya yinta ne a gaban Deeni da Baba Audi tunda dukkansu naki ne abokan sirrinki ne.” Ta yi murmushi tace,wannan gaskiya ne mama.
Hajiya Aisha ta kalle ta ta ce Bahijja na ji dadin
yadda kuke zaman lafiya da Farida wanda duk
yadda ta so tayi wani yarinta da wani kishi ba kya biye mata na ji dadin hakan kwarai dole dama saikin yi hakuri kin kau da kai tsakanin Farida da Deeni soyayyarsu daga Allah ne kuma shi ya hadasu dole wani lokacin za ta nuna kishi kan Deeni. Bahijja tayi murmushi ta ce mama nima na jima da fahimtar haka wannan shi yasa ma ban damu ba
kuma insha Allah in dai nime Farida da Deeni ba zasu taba samun matsala a kai na ba, naci girma na bar musu fagen. To Allah yayi maki albarka yasa ki gama duniya da lahira lafiya. tayi murmushi ta amsa da Ameen.
Sannan mama ta ci gaba maganata gaba shine gaskiya ba ma jin dadin yadda dangi ke ta magana akan ki daga ta bangare na har ta hangaren Alhaji Bahija ina so ki sani Jama’a Rahama ne dangi da yawa suna korafi akan idan sunzi basa samun sakim fuska a gurinki
zaki basu abinci da abin sha ku gaisa daga nan basa kara ganinki sai sunzo tafiya a nemo ki ko dai kina wurin
karance-karance ko kan compate, Bahijja tun da hutu kuka zo mai zai hana ba zaki bakura ba har sai kun koma gida idan idan baki sunzo ki tsaya ki sauraresu ai zasu ji dadi.
Na sun kina masu hidima kina musu alkairi amma ki zauna ki basu lokacinki ai zasu ji dadi idan kuna hira amma kin yi watsi dasu ai
wannan ba daidai bane maganar nan koda yaushe sai sunyi min ita duk wanda yazo sai ya fada Farida ce kadai take kula da su sabo da itace tasansu ke sai ki yi banza da su.ai abin sai yayiwa Farida yawa a bar mata hidimar gida ita kadai tunda ba ita kadai ce matar Deeni ba ya kamata ki tayata dawainiya da jama’a Nasan al’adarmu da taku da irin yanayin da kika tashi daban amma tunda kin auri dan dangi dole ki koyi mu,amala da danginsa da jama’arsa shawarace na baki saboda ba zan so inji ana zaginki a cikin zuri’a ba. Tsit suka yi duk suna sauraronta shi kansa Deeni bai ji dadin irim kalman da ya fita daga bakin mahaifiyarsa ba ba sai daì ba zai yi musu da itaba shi kansa shaida ne Bahijja na zama daga sun fara habaice habaicansu zata mike ta basu wuri ita ba gwanar zama bace na dole take yi. Bahijja tayi murmushi karfi hali ta ce mama ke babbace sai dai yana
da kyan kafin ki yanke hukunci yana da kyau ki fara jin daga bakin kowane bangare su kin ji nasu ni baki ji nawa ba kin yanke hukunci anya kuwa mama anyi min adalci,nì dai abin da zan iya cewa shine iyakar kokari na ina yi musu wurin karbar dangin Deeni sai dai zama da su tare da sakin fuska babu wanda bana yiwa haka ina yi musu daidai karfi na badan wata ko wani ba ni dai kawai haka naga ya
dace nayi musu. Amma tunda haka suka fada to Allah ya basu hakuri sai dai ni nasam iya gaskiyala ba zan taba yin abin da zaifi karfina ba wannan ne iya abin da zan musu ko nace iya karfi na ke nan. Hajiya Aisha ta kalle ta cikin zafi tace Ai kuwa na zaci zanci
Albarkacin uwa a gareki in ban haifeki ba ai na haifa mijinki kin fadamin magana a fakaice cewa ba zaki yi yadda nake so ba ke nan
wannan ya nuna min matsayi na mijinki a gurina tabbas da kina girmamashi yau da baki kalli idon mahaifiyarsa kin yi musu da ita ba.
Bahijja ta sadda kai kasa ta ce kiyi hakuri mama na bata maki wanna ba shine niyata ba , wallahi kina da mutunci da daraja matuka a idona haka mijina ina ganin kimar sa da darajarsa. mama ta mike a fusace ta ce Ka gani ko Deeni ka ga illar ko ‚illar auren girman bariki da marasa asali basu da tarbiyya .nan ta mike a fusace tana cewa nagode Allah da Farida ta zama matarka ko ba komai dangi zasu ji dadi gurinta yar dangi wannan yar barikin bazata bata mana zuri’ a. Ba
Haka ta fita tana ta suruai Deeni ya bita yana bata hakuri. Bayan fitarta Baba Audi ta fashe da kuka saboda tana jin ciwon abin da ake a Bahijja tamkar yadda uwa za ta ji zafi in anyiwa yarta ba daidai ba,gori dai Bahijja tana shanshi tun daga auran Farida
har zuwa yanzu duk da Farida tana nuwa babu ruwanta amma ita tabi duk ta siye dangin Deeni ko dai na makudan kudi ko zannuwan daurawa duk wanda ta sani zasu fada aji cikin dangi su tabi tayi musu hidima cikin hikima da kissa. Duk ta gama
saye kowa Baba Audi na sharar kwalla sai kawai ganin Bahijja tayi tana murmushi,Baba Audi tace’lafiyar ki kuwa yar nan wai kin san ciwan kanki kuwa ko dai babu zuciya a kirjin ki ne da ke jin zafi da bacin rai”‘
Ta kalli Baba Audi ta ce Duk ina da su Baba
Audi ina jin bacin rai sai dai nuna hakan bazai
kawo min saukin matsalata ba sai ma kari ni kuwa nayi alkawarin yaki da duk abin da zai kuntata wa rayuwata sannan dama ni bani da wani sauran
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe