MISBAH BOOK 3 CHAPTER 24 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 24 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
kin mai da ni da banza daya ne a gurinki, na
tsaneki Bahijja tsana mai tsanani. Zuba masa ido tayi tana kallonsa ko kadan
kalamansa basu bata mamaki ba don ta zaci fiye da haka bata taba tsammatawa kanta wani sauki ko wani abu na farin ciki daga Deeni ba a tun lokacin da rikici ya fara tsakaninsu.Ta CE Ka gama fada min iya abin da yawan tsanar da kayi min?wannan kalaman da ka fada ni ya kamata na fada maka amma ban fada maka ba
saboda kai namiji ne amma da yake namiji namiji ne an haifeshi da son kai sai gashi kana juye minsu to idan kagama wannan mu ci gaba ido a tsaye zuciyarta a bushe take wannan maganar. wanda ya Kara tunzurashi.
Ya kale ta ido cikin ido zuciyarsa kamar ana hura wuta don azabar zafi ya ce”‘Kije na yanke igiyar aure dake tsakanina dake ni Deeni na saki matata Bahijja saki daya halattaccen sakì” Duk da dama tasan abin da zaì fadi amma sai da taji gabanta ya fadì zuciyarta ta mata zafi zufa ya dinga keto mata idonta yayi jawur taji jikinta na rawa ta
zura masa ido tana tuno tun daga ranar
haduwar su na farko da abubuwan da suka yi ta gudana a tsakaninsu har zuwa yau din nan wani mummunan bacin rai da zogin zuciya tare da dana sanin sanin Deeni da tayi a rayuwarta da haduwa da tayi da shi a rayuwarta ya zo mata duk yadda
idanunta suka kada zuciyarta yayì rauni sai da tayi namijin kokari ta tsaida hawayenta tare da sake ware idunawanta tàna kallonsa tace”‘Nagode Deeni wannan shi me (prize) din dana biya na auranka wannan shine kimar auranka ban taba tunanin zan biya auranka da nayi da tsada haka mai tsanani haka ba da harka talautani talauci mai muni duk wani abu da nasiya ko na koya ko na ilimantu da
shi yau ka talautani talauci mai muni duk wani abin dana taba sani ko na koya, ko na ilimintu da shi yau ka talautani banì da shi, duk abin da na koya ya tsawan rayuwata da abin da na koyawa Wasa ,yau na rasa shi ka talautani da ban sira da komai ba duk wani abu da na yadda da shi na karanta da wanda aka koya min da wanda na koya da kai na da wanda rayuwa ta koya koya min da wanda na koyar (believe) din da na rayu da shi,na yarda da shi nake ganin haka yake yau ka talautani
ta hanyar sani rasa wadannan abubuwan.
Soyayya karya ce Alkawari karya ne,Amana
karya ne komai a rayuwar nan da duk abin da na taba sani na rayuwa akai duk karya ne, wannan mammunan talanci da ka daura nì akai bana yiwa wani ko wata fatan fadawa cikin irinsa. Sai dai Alhamdulillah duk da talautani da kayi yau ka bani wani sabon darasi wanda ni a gurina sabon jarine da zan fara dorawa na sake daga farko har in kuma yin wani arzikin da yafi na da in har
Allah ya yardar min saboda ka bani jari mai tsokar gaske da insha Allah zan iya sake kafa kai na, inyi kwari tun daga tushe. Iya zamana da muka yi ina neman yafiya daga gareka kuma ni ma na yafe maka ka mance a
rayuwarka Ka taba sanin wata Bahijja balle
MISBAH. haka nan daga yau yanzu zan manta dana taba auran wani wai shi Deeni sai dai darasin daka koya min a rayuwa ba zai
taba barin kwakwalwata da zuciyata ba koda da second daya” Tanagama fadin haka ta juya ta tafi ya bita da kallo zuciyarsa cike da fushi da tsanarta tare da fadin gaskiya kika fadi musamman a Kalmar soyayya sai fitina da bala’I da bacin rai,Farida da nayi soyayya da ita a rayuwata ta jifa rayuwata cikin bala”I da bacin rai har nayi dana sanin soyayyar na tsani soyayyar na tsaneta na cire ta a raina.
Ke da na so har nake jin ban taba son wata irinki ba na ji ashe da shirme nake ba son Farida nake ba MISBAH itace so na,ita ce SHAUKI, MISBAH itace rayuwata amma daga karshe sai da kika kuntataMa rayuwata.
Farida ta rusa rayuwata saboda son kanta ke kuma kika min rashin fahimta kika
bata dama kuka hadu da maihaifiyata da nake so kuka kuntata rayuwata ba tausayi ko kadan a zuciyarku kowa sai son kansa Allah kuma ya hana kowa irin wannan soyayya taku.
Taji abin da ya ce ta bata saurare shi ba ta wace ta samu Baba Audi ta ce’
“Tashi mu harhada kaya yanzu zamu bar garin nan.bata yi mata musu ba ko wata tambaya ba saboda duk abin da suke yi a kunnenta dan haka shiru tayi kawai.suka shiga
hada kayansu yayin da Deeni ya dau motarsa
motarsa ya bar garin cikin bacin rai ko ina ya nufa shi kansa bai sani ba.
Haka Bahijja suka tafi ba tare da sun yiwa
kowa sallama ba sai Airport sun yi sa’ar samun jirgin Lagos.Haka Deeni har Bahijja suka bar garin Kaduna cikin mummunan bacin rai tsakanin fushi tare da haushin juna da tsanar juna. ‘
Tunda Bahijja suka isa Lagos ta kasa
zaune da tsaye aiki ma ya gagareta ba abinda take ji a ranta da zuciyarta illa ta nesanta kanta da Deeni da duk wani abu da zai tuna mata da shi. Asibiti da marasa lafiya suna tuna mata da shi haduwar su yadda suka shigo rayuwar juna, wanda
hakan ba karamin kona mata rai da zuciya yake ba a wannan lokacin hankalinta da tunaninta baya tare da ita tsananin fushi da bacin rai ya maye gurbinsu don haka ta ci gaba da aiki dasu maimakon
tunaninta kafin su Deeni su dawo ta kwashe
kayanta na sawa da wasu yan kananan
abubuwanta na amfani ta koma gidan ta hakan bai bata kwanciyar hankali ba har sai da taji ta yanke shawarar barin garin
duk yadda ta kai ga son Asibitinta da aikinta
ya gagareta duk da tana kokarin nuna karfin hali da nuna jarumta wannan lokacin shine mafi rauni a rauwarta.Wanda har sai da tsanar kanta da tsananin fushi da kanta ya kamata duk fadan da fushin haushin da
tsanar duk ta mai da shi kanta saboda laifinta ne ita ta jawowa kanta ba kowa ba da bata saki zuciyarta Deeni ya shiga ba da bai kai ga auranta ba balle har hakan ya faru shaukin so da dadin baki na da namiji ya kwasheta ta rusa rayuwarta tunda take a rayuwa bata taba kasancewa cikin tashin hankali da
kunci da ukuba ba sai a gidan Deeni amma duk da haka abu daya tayi imani da shi kaddaranta ne wanda baza ta tsallake ba.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe