MISBAH BOOK 3 CHAPTER 26 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 26 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
hankali ita ta taimaka masa mu kanmu
Iyayenmu, mu saddakar da zai sake samun walwala a rayuwa. Ki tuno da jajircewa da yarinyar nan tayi akansa ki duba yadda sukayi rayuwarsu tana tare da shi da
dadi ba dadi auren Farida da Deeni yayi ina da
tabbas a dole yayi saboda ke ta yaya muka
zamo,me kuntata rayuwar danmu fiye da faranta
masa? Ta kalleshi ta ce” Alhaji yaron nan na son Farida aurenta ba zai zamo kunci ba kuma ita Bahijjar wacece da baza ai mata kishiya ba? Kin shiga zuciyarsa kin gani ko kina da tabbas din har yanzu yana son ta? Shin fuskarsa da idanunsa bai isa ya ganar dake gaskiyar zuciyarsa ba?
Rayuwar nan fa komai na iya canzawa an fada
maki zai tabbata da son Farida ne kamar yadda
yanzu son da kike yiwa Bahijja da yanzun ya rikide ya dawo tsana, haka komai yake a rayuwar nan baida tabbas,amma kin yi nisa bazaki gane ba,yana gama fadin haka ya fice ba tare da ya saurari me za ta ceba haka ta dinga kaiwa da komowa tana nanata maganganunsa akwakwalwarta da zuciyarta gaskiyar Alhaji Farida ta yiwa Deeni shishshigi da yawa a rayuwarsa nan ta rintse ido tana tuno irin
kaunar da takewa Bahijja tabbas in haka ne dole
rabuwa da ita ya kuntata rayuwarsa, Oh! Allah
meke faruwa ne Allah ka bani ikon gyara auransu ka dawowa da dana farin cikinsa
Watan su Farida guda da dawowa Lagos amma
Deeni bai dawo ba wannan abu yayi matukar
bata mata rai tare da jefa zuciyarta cikin tunani da zargi kala-kala anya kuwa Deeni ba Bahijjar ya
dauka ba suka bar kasar ba? Wayarsa Laptop dinsa da sauran kayan aikinsa duk ya barsu a gida babu ta yadda za ta iya kiransama,sai shi ya yake kiranta,shi din ma sau daya a rana ko da daddare shi ma daga gaisuwa yaji ya suke ya yara sai ya kashe wayar ba tare da ya bata
damar yin wata magana ba balle tayi masa wasu
tambayoyi. Haka nan boye number yake yi in zai kirata balle tabi ta kirashi wannan abu yana matukar kona mata rai,nan da nan ta tsinci kanta da rayuwarta cikin kunci yadda take zato da tunani ba haka bane ba,tayi zato in suka yi aure da Deeni tana tuna masa irin soyayya da rayuwar da sukayi tun yarinta irin shakuwa da kusanci dake tsakaninsu,sai taga abin yazo mata a yaddda baza ta ba.
Bahijja ta shiga zuciya da rayuwar Deeni wanda
ya share nata memories din,daga zuciyarsa Deeni
ya daina so na? wasu hawaye masu dumi suka zubo mata yanzu duk kokarina da shiga da fitar da nakeyi don sama wa kai na matsayi a gurin Deeni yan’uwansa,mahaifansa ya tashi a banza.
Soyayyar da nake buri da mafarkin samu
gidan Deeni babu shi nan ta hade kai da gwiwa tana kuka, kuka sosai nan da nan tayi kewar shamsu tunaninsa da rayuwar da
suka yi yadda yake nuna mata kauna da tausayawa sam baya barinta cikin damuwa ya mantar da ita soyayyar Deeni ya sanya ta cikin farin ciki bayan rasuwarsa komai ya dawo mata sabo,soyayyar Deeni ta dawo mata danye a zuciyarta a lokacin da Deeni shi yayi nisa da son wata Bahijja,duk yadda zakiyi ba zan bariki raba ni da Deeni ba,ko ta tsiya ko ta arzikisai na dawo da soyayyar da yake min a zuciyarsa.
Nan ta share hawayenta ta mike ta shiga bayi ta
wanke fuskarta sannan ta shirya ta tafi makaranta tare da shirya zuwa gidan malam dan ayi mata addu ‘a kan Deeni kuma ta karbi taimakon mallaka wanda kawarta ta taba yi mata tayi amma taki tana ganin kamar son da ta Deeni yake mata da kissa da kisisinarta ma ya isa ya kwace mata Deeni sai yanzu ta fahimci abin ba haka ba yake ba dole ta mike ta nemi taimako.
Lokacin da Deeni ya dawo Lagos zaman gidan
da garin yayi masa kunci komai baya masa dadi
rayuwarsa ta kuntata sun gina rayuwa mai dadi da tsafta shi da Bahijja su yi wasa dariya su yi fada su shirya ba wanda ya taba jin su,ba inda zai ya wulga ko ya shiga a gidan wanda baya dauke da (memories) din Bahijja. Bai taba tunanin
zai shiga irin wannan mummunan kuncin ba idan ba ta nan,dan haka ya yankewa kansa hukuncin nisanta gidan na wani lokaci wanda hakan ba zai yuwu ba sai dai idan baya kasar.tabbas yasan yana son Bahijja so mai tsanani amma saboda shakuwar da suka yi yafi wahalar da shi fiye da komai da har yasa ya kasa
jurewa.Lokacin da Farida taje gidan malam neman taimako ya tabbatar mata da za ta mallake Deeni iya son ranta ya dakko wani magani ya bata ya ce tayi matsi da shi idan sun zo kwanciya muddin ya sadu da ita anyi an gama zai manta da ko wacce diya mace a duniya sai ita sai kuma yadda tayi da shi. Ta dawo gida cike da tsananim murna da fari ciki mara musaltuwa tana Allah Allah Deeni ya dawo ta aiwatar da kudirinta akansa ta shirya makaman
yakinta tsaf don kwato Deeni ya dawo gareta sai
yadda tayi da shi sai kuma yadda ta so wasa gaske Deeni bai dawo ba har tsawan wata shida a nan hakurinta yakare hankalita yayi mummunan tashi.lokacin da yayi mata waya kamar yadda ya saba a kowa ne dare ta fashe masa da kuka kuka sosai.Ta ce”‘Deeni in ba ka so nane ka tafi ka bar ni kaje kana rayuwa da Bahijja to maye amfanin
kyaleni da kayi da igiyar auranka idan ci ne da sha da kuma sittira duk ina samu a gidanmu gurin
iyayena,meye amfani na zuwa gidanka ka manta
kana da hakkin debe min kewa sanya ni farin ciki
da nishadi idan baka so nane ka sake ni ka huta” Bai ce mata uffan ba har sai da ta gama
maganarta sannan ya ce mata Ina nan dawowa
nan da kwana uku.Bai saurari mai za ta ce baya kasha wayar nan da nan dadi ya cikata ta hau gyare gyaren gida har sababbin dinki tayi na taran mai gida, hatta yara saida ta siya musu sabbin kaya tuni gida ya dauki
kamshi da haske cikin kwanaki uku.
A ranar da zai dawo ta shiga dakinsa ta hau
gyara baji ba gani gyara na musamman wanda yafi ko ina jin gyara a cikin gidan.
Bayan ta gama har ta zo za ta fita idanunta ya
fada kan ipad dinsa, haka nan taji a ranta tana so
budewa tayi masa bincike.ipad din ta
dauka ta soma shiga inda hotunansa suke wani file idonta ya kai inda ta ga an rubuta MISBAH NA
zuciyarta taji tayi mummunan tsikewa MISBAH’
ta maimaita sunan ba bata lokaci ta soma budewa nan kuwa taci karo da hotunan
Bahijja da suka yi matukar tada mata da hankali da razana ta hotunan ne ratata babu iyaka a wuri daban daban wanimma bata san an dauke su ba
hankalinta ne ya tashi ta ga Bahijja ta yi mata
matukar kwarjini shegiyar mata kyau kamar Aljana ga wani irin wayewa da karisma a tattare da ita macece mai Confidence tare da fuskantar duk wani abu da ya zo gabanta babu tsoro ko shakka a tare da ita.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe