MISBAH BOOK 3 CHAPTER 27 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 27 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Tuni taji wani irin kishi ya turniketa har taji ta

raina kanta nan take taji hawaye na zubo mata cikin ranta.take cewa. Farida ina kika iya da irin

wannan

HAMSHAKIYAR mace a gidan Deeni da

rayuwarsa shine kike tunanin har yanzu son da

yake maki yana nan mai zai hana Bahijja kwace

maki Deeni maganar gaskiya Allah ne ya duba

Deeni yayi masa sauyi fiye da zabinsa lokacin dana auri Shamsu. Kinyi kuskure kice zaki kori

Bahijja daga rayuwar Deeni zan iya korarta a

gidansa amma banda zuciyarsa tuni kuka ya kubce mata taji duniyar tayi mata zafi, wato dama Bahijja ita ce MISBAH? Nayi tunanin MISBAH namiji ne wato dama kishin da nake da takardunta ba a banza ba,dama za tazo rayuwar Deeni ta kwace min shi ta rabani da

ME SONA,kuka take ba kakkautawa kuma hakan bai hanata ci gaba da bude sauran hotunan ba ta bude wani (Folder) wanda taga ansa NI DA MISBAH’ NA gabanta na tsinkewa ta ci gaba da budewa Deeni ne da Bahijja tare suna

manne da juna,suna cikin tsananin nishadi tare da soyayyar juna hankalinsu kwance kana ganinsu kaga masoya masu matukar son juna da kowa ya gansu sai yayi sha’awarsu in ba dan bakin ciki ba. Tabbas wannan rana taga abinda

yai mummunan daga mata hankali fiye da komai har tayi dana sanin yin binciken da ta masa da bata ga abin da zai daga mata hankali har haka ba, wasu irin kalaman soyayya da yayi amfani dasu masu taba

zuciya da tsuma rai akan irin tsananin son da yake yiwa Bahijja da mahimmancin ta a rayuwarsa yana tsananin ganin girmanta,kimarta da darajarta tare da yin jinjima da kalamai na yabo da daukaka da lambar yabo gun mijinta ita kam,ta gama hawayen duniya da lahira nan ta hada kai da gwiwa tayi kuka,kuka mai isarta.

Duk da haka bata hakura ba ta hau binciken

email dinsa da wasu chat dinsa da suka dau tsawon shekaru wanda tun lokacin da suke tare wanda ko za taji ko ta ga wani abu da zai faranta mata wanda Deeni yayi akanta da farko ta danji sanyi saboda yadda taga hirarrakinsa da jama’a

akanta,yadda yake bawa mutane labarin irin

tsananin sOn da yake mata soyayyarsu

da shakuwarsu, da yadda yake jin bayan ita bazai taba son wata mace haka ba. Wannan ya sanya

farin ciki da nishadi a zuciyarta duk da kasan zuciyarta akwai kuncin MISBAH a ranta amma taji dadin cewa itama ta taka wani matsayi a zuciyarsa,sakonni na gaba da ya daga mata hankali shi ne. Yadda taga messages dinsa

da yammata musamman lokacin da yake kasar waje karatu hakan yana nufin lokacin ma yana tare da ita amma yana neman wasu ‘yammatan ma shine yake jansu da hira yana shige musu ayi ta shiririta irin na saurayi da budurwa.

Numfashinta taji ya soma daukewa wato Deeni

duk da yana tare da ni bai hana shi neman wasu ‘yan matan ba,tuni ta sake fashewa da kuka wiwi

hankalinta ya kuma tashi ga tsananin kishi gajin

zafinsa sannan ga cin amana. Wayyo Allah ashe cin amana bai da dadi, duk da shekarun da yawa sun ja sun wuce amma ina jin zafin cin amanar da Deeni ya min,ya ajiyeni matsayin matar da zai aura yake so sannan yaje yana neman wasu ‘yan mata dan kawai yayi nishadi yaji dadi tare da yin wasu kalamai wanda ni a wannan lokacin bani da wayewar jinsu jikinta a mace a sanyaye hannunta na bari ta rufe ta ajiye

tuni taji wani irin zazzabi da ciwon kai sun

rufeta,zuciyarta ta kuntata har numfashinta na

kokarin kufce mata. Wayyo Allah ni Farida namiji kanin ajali wannan gaskiya ne,nemiji ba abin yadda bane,duk yadda yake sonka yake da gaskiya da dabi’a na kwarai sai yaci amanarka,sai ya nuna halinsa na cewa eh shi

da namiji ne,namiji bashi da amana bashi da

Alkawari,sai dadin baki da Alkawarin karya da

iska in yana nemanka yana nuna maka kafi komai

da kowa muhimmanci,amma a bayan idonka ya

ha’inceka kafin inci amanar Deeni In auri

dan’uwansa shi ya fara cin amanata wayyo ni

Farida ya zan rayu da wanna takaicin haka ta

rarrafa ta nufi bangarenta ta hau gado ta lulluba

tana rawar zazzabi. Karfe takwas na dare Deeni ya shigo gidan yara su ka kaure da ihu da tsalle su na oyoyo, ya daga Aysha sama tare da sumbatarta yana murmushi su na ta yi masa tambayoyi yana ba su amsa hannunsa

cike da tsaraba ya dinga fiddo mu su a mota da yake shi mutum ne me son yara sai da ya gama wasa da su sannan ya ce,ina mamansu? Su ka ba shi amsa”tana daki ta na barci” nan suka nufi dakin nata da gudu tare da nuna mata tsarabar da Baba Deeni ya kawo musu, ta ji ta kara kulewa duk haushinsa take ji ta ce,To maza kuje Kuyi wasa ku bar ni kaina na ciwo,nan su ka nufi bangarensu da gudu.

A Falo Deeni ne yake gaisawa da ma’aikatan

gidan su na masa barka da dawowa shi kuma yana tambayarsu gida da komai lafiya ko ba matsala suna bashi amsa,har yagama da su ya nufi bangarensa Farida ba ta je ko in da ya ke ba ta na kwance dukda zuciyarta na azalzalarta da ta je din amma ta ki zuwa har ya yi wanka yaje ya ci abinci,ka na ganinsa za

ka ga babu fara’a ko kadan a fuskarsa, kawai dai ga shi nan ne ba yabo ba fallasa

nan ya dauko sabuwar ipad din sa da ya dawo da

shi ya bude ya na dubawa tare da danne dannensa da binciken da zai yi har wurin karfe sha biyu sannan ya mike da har zai wuce ya kwanta sai kuma ya tuno hakkinsa ne ya duba yaya ta ke da lafiyarta ya samu tana lullube ya sa hannu yaja bargon ta yi saurin bude ido cike da masifa dama abin da take jira ke nan ta mike tare da masa wani mugun kallo ta ce”ka ga dama ka leko? Ka ga ko ina raye ko ina mace? Bai yi mamakin jin kalamanta ba saboda ya san yadda ya yi biris da ita na tsawon wata shida za ta yi abin da yafi haka,ya kalle ta Farida ina zama da ke da aure ne saboda iyayena da naki,a kullum na kalleki ina ganinki a matsayin wacce ta kawo guguwar bakin ciki rayuwata da rabani da duk wani jin dadi nawa da sukuni na ana so namiji in ya kalli fuskar matarsa ya ji sanyi amma ni ida ina kallonki na kan ji wani bacin rai kina tuna min da duk wani kasawata da rauni na a matsayina na da namiji dan haka bana san wani surutu da tashin hankali,ki bar ni da tashin hankalin zama da ke da yin ido biyu da ke kullum hakan ma ya isheni”Ni kuma me zan ce a akanka”‘ ta fada cikin

kunar zuci sannan ta ci gaba da cewa

“‘ni kuma nayi yaya da nawa tashin hankalin? Wulakancin da kake nuna min yanzu ne zanji da shi ko kuwa cin amanar da kayi min a baya? Ko kuwa sonka da yake cina a zuci wanda duk haushinka da nake ji naka  a zuciyata ni kasan ya nake ji idan nayi ido biyu da kai”‘

In har kana jin kunar zuci idan kaganni mai zai

hana ka sake ni Murmushi yayi ya ce

“‘ tsakaanin mu da ke ai babu saki Farida da dadi da ba dadi haka zaki zauna da ni gwara ki san da wannan” .nan ya juya

zai tafi ta kira shi cikin daga murya ta sha

gabansa ta ce.Deeni mai yasa ka ci amanata shekarun baya da suka wuce? munyi alkawarin aure da kai kaje waje karatu ina nan ina jiranka kana can kana

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE