MISBAH BOOK 3 CHAPTER 29 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 29 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

da shuni ne can tana zaune ta hango wata tsaleliyar budurwa ta shigo tana dariya tana yauki tana wani karairaya taci ado tasha kyau ga hutu,yar gata ta iso tana murmushi ta ce

“Ranka ya dade sannu da zuwa”‘ ta kalli Farida sannu da zuwa aunty ya yara?.

Tuni Farida ta sha jinin jikinta taji ta raina

kanta, Deeni yayi murmushi ya ce sannu Gimbiya

yau gani ga uwar gida ya kalli Farida ya ce wannan it ace Salma shekararta ashirin da biyu yar gida ambassador ce tayi karatun likita a kasar india tsawan wata biyu muna nema ina tunanin yi maki kanwa ya ce Salma wannan matata ce gimbiyar gida Farida uwar yayana, Auntynki kuma in kin shigo. Salma dai murmushi tayi tare da fadin ai kuwa nayi murna da ganin Aunty na biyayya kuwa za yi mata ko dan samun matsayi a gurinka saboda girman son da nake maka ni dai burina da fatana na samu matsayi a cikin zuciyarka da gidanka da rayuwarka.yayi murmushi tare da fadin na ji dadin kalamanki in zaki kawo kwanciyar hankali a gidana ai shi nake nema.tayi murmushi ta ce yallabai anyi angama.

Tuni Farida zuciyarta ta kawota karshe ta  murtuke fuska tana mamaki fuuu ta nufi mota zuciyarta cike da bacin rai da tsananin kishi.

Deeni yayi murmushi ya ce Salma zan wuce idan

da akwai• wata magana zaki jini kin san halinku

mata da kishi zan je na lallaba uwar gida.ta kalleshi a darare ta ce ni dai burina na zama amarya a gareka zan yi biyayya ina sonka Deeni.

Deeni ya ce karki damu inda halin haka za’a yi

Salma.nan ya mike ya ta bishi da kallo zuciyarta

cike da damuwa ta jima tana son Deeni amma yaki bata dama tayi nacin tabi amma ya nuna bai da ra’ayi su yi mutunci kawai. A mato ya samu Farida ta cika ta batse tana kuka ta ce dama ka kawo ni nan danka wulakanta ni kaci min mutunci ne abin da ka shirya min ke nan?dama gidan su buduwarka ka kawo ni dama unguwar da zan raka ka ke nan ka kawo ni gidan budurwarka

wannan wane irin cin mutunci ne?wai me yasa ka

tsaneni ne Deeni tsanar har tayi yawa,nasan ban

kyauta maka ba amma duk abin da nayi don ina

sonka ne,sai da tayi kukanta ta koshi ya ce in kin

gama zan yi magana ba wai na zo wulakantaki

bane nazo na nuna maki wani abu ne kuma in

fahimtar da ke shin kina  tunanin duk abubuwan da kike min zai sana canza tunanina? Duba

Salma ki gani komai tana da shi

yarinta,kudi,ilimi da asali komai bayan ita akwai

irinsu da ke bina ina so ki sani ni wannan basu

nake dubawa ba a mace ba ki sani ba tunda na soki Farida tun lokacin da duk baki da wadannan abubuwan so Allah ne ke dasa shi ba da wani dalili ba da kuma halin mutum Farida na so Bahijji na so halinta naso zuciyarta ina son dabi’unta,rayuwarta yadda take tunani da kuma kyakykyawar zuciyarta tana da rauni matsayinta na mace kuma dan-Adam.

Ina son ta haka da rauninta da kyanta da muninta

duk na amshe su ina son ta a haka babu mai canza min wannan gaskiyar kuma ba mai

samun matsayinta muna tare ko bama tare dan haka ki hutar da kanki duk wannan salon da kika tsira idan ina son wannan akwai inda zan samu da yawa.Yana gama fadin haka ya ja mota suka tafi tana ta share hawaye ta rasa meke mata dadi.

Kwance take ta tsurawa yariyar ido tana

kwance gabanta tana ta cillara ihu

maimakon tasa hannu ta dauke ta sai

ta zuba mata ido tana kallonta tana kara karantar

irin halittarta wanda idan ka cire kalar fatarta to

komai ubantane.Baba Audi ne ta shigo tasa hannu ta dauke ta tare da fadin ni dai zan ga ranar da zaki bar sakarcin nan Bahijja ke kullum yarinyar na kuka sai ki mata ido wai ina laifinta,zama cikin

fushi da riko haka.Cikin bacin rai ta mike ni zan tafi Muhammad da Umar Farouk na jira na madarar ta na nan,Baba Audi ta bita da kallo tare da mamakin hali irin na ta.Bahijja ta samu Umar Farouk a mota tare da dansa Muhammad, suna jiranta sallama tayi musu ta shiga motar abba ya amsa yana murmushi sanna suka gaisa fuskarta murtuke sam ba walwala girgiza kai yayi tare da fadada murmushinsa ya ce,Ni dai zanga ranar da zanga walwalar a fuskarki mutum, kullum kamar wanda yayi fada da wani’ kallonsa tayi ta ka da kai bata bashi amsa ba saboda bata son jan zancen ta canza maganar da cewa, Yau ,,,,,,,,

“Masu zuwa daukarki sun shiga wata hidimar ni

na sasu na zaci zazu gama kafin lokacin zuwa

dukar ki to amma sai aka samu akasin haka, ga

mara lafiyan naki yau sai rigima yake bai ganki ba

ya na ta fitina a hanyar zuwan mu nan ya samu

barci ya dauke shi”

Nan ta juya baya ta kalli Muhammad inda yaketa

sharar barci har da ajiyar zuciya kamar yayi kuka ya gaji ta maidoda kallonta, gareshi ta ce,

“Me kuka masa haka.Ya girgiza kai Ba komai yau ya tashi da sabuwar rigima da sabon kalma.

Ta yi murmushi Ana samun ci gaba ke nan da Abba kawa ya iya kira (Therapy) din namu ana samum nasara ke nan tare da taimakon Allah.

Haka ne'” Farouk ya fada cikin jin dadi tare da

fidin Ai ni ba abin da zance maki sai godiya

fatana inga farin ciki, a wannan fuskar taki wannan fushi da ke tattare da ke ki watsar da shi komai dacinsa ko zaki samu sukuni”

Wani irin kallo ta masa sannanta watsar da shi

ya saba ganin haka daga gareta wanda shi kallon

birgeshi yake Allah ya sani wannan mata akwai

(karisma) ta min kwarjini da abin da ke zuciyarta,

duk kuwa jin kaina da isata ta sauke min shi to

waini ta yayazan cire mata wannan fushi da ke

cikinta shin meye sila? Ta yaya zan so ma

tambayarta tarihin rayuwar ta? Shin me yasa bata

da (interest) akan soyayya ko aure Asalima ta tsani maganar soyayya ko labaran soyayya in kana so,kuyi fada dauko littafin soyayya kana karantawa gabanta yanzu za ta tunzura ta nuna jin haushinta a zahiri.hakan ya nuna bacin ranta da fushinta yana da alaka da soyayya.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE