MISBAH BOOK 3 CHAPTER 30 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 30 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE


“‘mama Muryar Muhammad ya katse masa

zancen zuci da ya keyi, nan suka mai da hankalin

su duka kan Muhammad wanda tuni ya mike yayi

wurin Bahijja da sauri tare da kankameta yana

kiran mama nan ta gyara masa zama ta ajiyeshi

bisa cinyarta suna kallon juna ta masa murmushi

tare da fadin Ba mamaa ba likita”ya girgi “mamaa Itama ta girgiza kai “Likita ni sunnana Dr. Bahijja, likitar Muhammad ba mamansa ba.”

Fashe mata yayi da kuka yana fadin mama tare

da bugunta tayi saurin rike hannushi ne.

“Yau ni zaka bigeni, me na koya maka?” Sauke kai yayi tare da turo baki yana ajiyar zuciya.

“Daga yau in ka sake min bore ko kuwa

mutanen gida ko Abba ka zan tafi in kyaleka, ba

zan sake, zuwa gidan ku ba kuma ba ruwana da kai ba zan sake maka magana ba zaka sake?”

Ido cike da hawaye ya dago kai ya kalle ta tare da

girgiza kai alamar bazai sake ba nan ta masa

murmushi tare da fadin.Good Boy,.” sannan ta rungume shi. Farouk ya kalle ta ya ce

“Kina ban mamaki ko kunyar idona ba kyaji kike yiwa dana tsawa da fada.Ta dago manya manyan dara daran idanunta ta masa wani irin kallo da sai da gabansa ya fadi ta ce,KO zaka rama masa ne?”Yayi murmushi ya ce,Ni na isa? Na warware

alkawarin mu da kwangilarmu? “Ka isa mana ai ra’ayine alkawari kuwa ai suma ne abaki kawai mutane ke yinsa don dadin, bakinsu

kawai da dadin zance don asamu biyan bukata”

‘”To ni bana daga cikinsu, nasan muhimmancin

alkawari kuma ina cika dukkan alkawarin da na

dauka bana fata in tashi a sahun munafukai ranar

alkiyama.”Tabbas kayiwa kanka gata in da gaske kake, Nidai kambana taba yadda da alkawarin da wani mahaluki zai min wanda in ya karya zai zama cutarwa a gareni in ma ka karya, alkawarin da kayi ba cutuwa, ne agareni ba sai a gareka.”

maganarta ya sosa masa rai amma sai ya basar ya tabbatar da matsala tare da damuwa a tattare da ita wanda yayi alkawari sai ya gano ko menene

watarana da haka hirar tasu tazo karshe har suka isa gida ya ajiyeta suka sauka tare da Muhammad shi kuma ya juya ya tafi.

Jirgin, gombe su Bahijja suka samu lokacin

saukar su a Abuja daga Lagos bata lokaci ba suka sayi (tiket) haka nan taji zuciyarta ya dan so garin tayi tsaki data tuno asalin su Deeni Gombe ne to amma ina ruwa na da shi da zuriarsa duka.

Hakika Bahijja tana cike da haushin Deeni da

tsananin fushi da shi tare da tsanarsa a zuciyarta

maci amana me karya alkawari tayi tsaki har ya fito fili har jama’ar da ke gefenta suka juyo suna

kallonta. Baba Audi ta fahimci halin da take ciki ta dafa ta kiyi hauri Bahijja ki daure ki manta abin da ya faru ki yafe masa sai ki samu sauki a zuciyarki da rayuwarki gaba daya Ta kalli Baba Audi ido ciki da fushi ta ce, “Na manta da shi bana lissafinsa a rayuwata bare maganar yafiya kaina na kasa yafewa in haushin kaina nake, da na bari na kuma bawa wani dama ya bata min rayuwa ya cutar dani na nayi wauta nayi rashin wayo na yaudari kai na.Ya isa Bahijja inji Baba Audi sannan ta ci gaba da cewa Akwai wanda ya isa ya canza

kaddarsa ko abin da Allah ya rubuta masa ki dauka a matsayin kaddararki kiyi hakuri ki danne ki mance kici gaba da Addu’a Allah ya huci

zuciyarki ya mantar dake wannan bacin rai da

kunci da kike ciki. Da ire iren wannan magaganun na, kwantar da hankali Baba Audi ke mata har suka sauka a Airport na Gombe, hakika Baba Audi ta amsa sunanta uwa tagari yadda ta, dinga tausar Bahijja tare da bata baki da lallashi saboda ta fahimci halin da take ciki tana bukatar lallashi duk da, juriya da dauri ya irin nata amma abin da ya faru tsakaninta da Deeni ba karamin taba mata zuciya tare da tsananin raunata ta.

Bayan sun sauka suka samu taxi na airport suka

nufi cikin gombe ba tare da sanin ina suka nufaba

saidai niyarta suna isa sunemi hotel su sauka.

A hanyarsu ta shiga gombe taxi din nasu ta

lalace gashi yamma ce lis haka suka fito suma

zaune bakin titi lokaci guda Bahija taji cikinta ya kamata hankalinta a tashe, suka dan ratsa cikin jeji gindin wata bashiya a nan suka lura wani kauye ne a ciki nan ta nemi taimakon ruwa ta bawa Bahijja ta kuskure bakinta tare da wanke fuska. Tsawon minti shabiyar suka dauka Bahijja na hutawa sannan suka mike zuwa gun mai taxi din nan ya sanar dasu cewa sai dai su nemi wani motar shi ma wani mota zai nema yaje cikin gari yasamo maigyara kuma zai iya kaiwa gobe anan ya rufe motar da sauke musu kaya ya wuce.

Nan fa Baba Audi hankalinta ya tashi ganin ga

dare yayi Bahijja tayi murmushin karfin hali ta ce,

“karki damu ba zamu rasa yadda zamu yi ba, nan ta juya bayanta ta ce,Baba Audi ai mu Allah ya

mana gata da yasa bama Jeji muke ba taho mu

shiga cikin kauyen nan mu nemi wurin kwana

zuwa gobe.Hakan ko aka yi basu bata lokaci ba suka mufi cikin kauyen rike da kayayyakinsu duk da duhun dare ya fara yi bai hana Bahijja ganin yanayin kauyen ba wanda tafiya birgeta zuciyarta ya nutsu da kauyen gonaki da dabbobi da ta gani ya tabbatar mata da za’ a samu albarka a wurin ga koramai na ruwa ga ‘yan bukkokinsu da gineginensu mai ban sha’awa da alamar suna rayuwa su a saukake kuma cikin jin dadi.

Ga abubuwan kiwo kala kala tuni taji ranta na son

zaman wurin tayi sha’awar kauyen matuka haka ta dinga waige wage tana kallon taji saukin kuncin

dake zuciyarta tayi nisa cikin kallon wurin bata Ankara ba sai ta tsinkayi muryar Baba Audi tana

magana da wasu mutane.Tana rokon su su barsu su kwana dare daya kawai tana tare da mara lafiya daya matar ceta amsa mata cikin harshen su na Fulani kuma jan kauye ta ce,

“Bai war Allah muna cikin fargaba muma kwana dayan shi ya rage mana a kauyen nan da yake rayuwar mu na shekara da shekaru.ta

fada cikin tashin hankali wanda yaja hankalin

Bahijja ta matso garesu tare da gaishesu sannan ta tambayi me ke faruwa? Basu bata amsa ba sai cewa sukayi su zo su je gun mai gari in ya amince. basu bata lokaci ba suka dunguma gidan mai gari wanda yake ginin laka madaidaici wanda yafi sauran gidajen wurin girma sun samu mazan, kauyen a cike a kofar gidan yayinda

maigarin, na zaume a tsakiyarsu suna

tattaunawa, alamar hankalin su a tashe yake duka sallamar dasu Bahijja su kayi yaja hankalinsu yayinda suka kurawa Bahijja ido kamar sun ga sabuwar halitta nan take suka mike suka yi kanta yayinda suka mata ca’a a kai suna fadin «Yanzu kuma, ke ya turo?

“To bari in fada muku, bamai raba mu da

gidajenmu da dukiyoyinmu dan baku da imani ku

rasa wanda zaku cutar sai mutanen kauye da basu da komai sai rufin asiri noma da kiwo shi ne

rayuwar mu, kuke son raba mu da shi?’

Bahijja dai ta saki baki tana kallonsu suna ta

fada mata, magana cikin zafin zuciya da kuma

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE