MISBAH BOOK 3 CHAPTER 31 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 31 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
tashin hankali tana kokarin magana amma basu ma saurare taba sai da maigarin ya dakatar dasu shi ya matso kusa da Bahijia ya ce.
“Me ya kawo ku Alhaji Umar ne ya aikoku?”
Ta girgiza kai tare da fadin “A’ah mu baki ne mota
ta lalace mana muka zo neman wurin kwana zuwa gobe. Amma in bazaka, damu ba zaka iya fada mana meke faruwa? Naga duk hankalinku a tashe.”Ya kalle ta cikin damuwa ya ce,
“Baiwar Allah duk wanda za’a rabasa da gidansa wurin zamansa da sana’arsa an nemi tonamana asiri dole honkalinmu ya tashi.”
Ta kalleshi ban fahimta ba? Lokacin sallah yayi zamu yi maganar bayan isha”a ya kalli matar yace, Laure ku basu wuran sallah da abinci a cikin gidana” daya daga cikin mutanen ya ce, Allah kaine ka yadda dasu daga ganin mutane kasan duniya fa ba yadda” yayi murmushi “karka damu ba macuta bane ni naga gaskiya a tattare dasu Allah ya bani baiwar gane macuci mai cutarwa.
Da wannan maganar suka watse yayinda aka shiga dasu Bahijja gidan mai garin duk inda suka wulga kallonsu ake Bahijja ko zuciyarta, na azalzalarta taji me ke faruwa kwakwalwarta cike da tambaya tuni ta manta damuwarta wannan lokaci ta soma tunanin nasu matsalar da damuwar.Da kuma hanyar da za’a bi a kau da matsalar bata iya tayi barci ba har saida taji meke faruwa daga bakin matan gidan. Harta kwanta ta tashi ta nufi cikin gidan nan ko ta taras dasu dukkansu zaune ba wanda ya runtsa ta isa inda suke sannan ta kalli babbar cikinsu wanda taji suna kira Yafendo ta ce, “Dan Allah ko zaku iya fada min meke faruwa naga hankalinku tashe haka?”Yafendo ta kalle ta cikin harshensu na Fulani ta ce, “Ke dai yarnan ayi sha’ ani kawai ke dai kiyi barci da safe ki kama gabanki.
Nan Bahijja ta dage lallai sai taji me ke faruwa ta ce To tunda kindage zan fada maki duk da ba abin da zaki iyayi.”Bahiija ta zura mata ido ta ce, “Ina jinki matar ta ci gaba ta ce, “Munjima a kauyen nan tun lokacin kakannin mu, wurin tun yana daji mukazo muka gyara muka nome wurin muna shuka muka kafa yan bukkokin mu kasancewar kakanninumu da iyayenmu matafiyane basu da takamammen wurin zama a hankali muka mai da wurin kauyen mu. muka kafa gidajenmu muna kiwon dabbobinmu muna noma har wasu ma suka zo suna kafa nasu bukkokin lokacin guda kauyen nan ya cika yadawo mana gida da wurin sana’armu mu yi noma mu yi kiwo mu sai da nono dasu hura kowa ya kama sana’arsa. muna kaiwa cikin gari da sauran garuruwa kusa mu siyar nan muka yi karfi har ana Zuwa siya daga garuruwa daban daban akan wannan kakanninmu suka rasu suka bar iyayenmu aure muka hayayyafa muna walwala da jin dadin mu da sana’armu. Rana tsaka wani mai kudi yazo mana da wani zance wai kauyenmu filin kakansa ne da ya mutu ya barwa iyayensa gado shi kuma ya gada gun iyayensa dan haka yanzu yana son wurinsa zai gina kamfani ya ba mu wata guda mu tashi har lokaci yayi muka ki tashi shi ne ya hada abin da hukuma suna zuwa suna daga mana hankali ko mu tashi ko su mana barna.
” Kin ga muna cikin tashin hankali ai za’a raba mu da rayuwar mu gidanmu sana’armu cinmu shanmu walwalarmu, yana nan yanzu kuma an nemi a raba mu da. gidajenmu zai tona mana asiri ina zamu shiga damu da yayanmu dabbobinmu ya zamu yi da noma da muke da sauran nan kauyen shi ne rayuwarmu. Ta karasa maganar da sharan hawaye Bahijja ta matukar ‘tausayamasu taji ita dai za ta taimaka musu har iya inda Karfinta yakare. Ta kalli Yafendo ta ce,
“karku damu, insha Allah ba zaku tafi ba ba kuma mai rabaku da gidanku ba wanda ya isa ya rabaku da gidanjenku kwantar da hankalinku.
Yafendo tayi mata kallon, baki san me kikeyi ba. Bahijja tayi murmushi ta ce, “Baki yadda dani bako? Allah ya kaimu gobe yazo.Wata daga gafe ta ce, “ke bakuwa ce, ki kwana da safe ki kama gabanki ba zaki gane halin da muke ciki ba wannan mutumin yana da karfin iko da mulki da kudi.” «Duk kudinsa da mulkinsa ai baifi karkin Allah ba, wanda dukkan Karfi da mulki da komai nasane da wannan maganar suka watse Bahijia ta kwana tana sake sake yayinda Baba Audi ta sa mata ido tana kallonta bata gajiya da mamakinta ta manta da halinda take ciki ta shiga wani matsalar daba nata ba tabbas wannan wani baiwace ta daban Allah ya yi mata ba kowa ne zai iya manta mastalarsa da alamuransa ya shiga na wasu ba, wanda hakan ya mantarda ita kuncin da take ciki. Tashiga tunanin ya za ta tunkari matsalar da warwareta abu daya ne yazo kwakwalwarta, su kaishi koto kafin shiya kai su da wannan ta kwanta wa shegani kuwa suka hadu duka maza da mata a kofar maigari ana ta tataunawa yadda za’ayi in yazo Bahijia ce ta mike ta kallesu duka ta ce Ni zan iya kwatar muku gidajenku amma ina da sharadi duk suka kalle ta kallon mahaukaciya sai maigarin ne, ya ce
“Meye sharadin naki kuma, tana ta yaya zaki kwatar mana gidajenmu.”Ta hanyar kotu”
‘ ta bashi amsa ya kalle ta ke,lauya ce? “‘ah” ta girgiza kai “Amma zamu iya shigar da kara kotu mu dau lauya”Kina ganin zamu iya nasara a kansa yafi mu kudi da matsayi.”
“Kwarai ai Allah ya fushi kuma yana tare da masu gaskiya shawarace. Nan wurin ya karade da hayaniya wasu na fadin su kai kotu, wasu na fadin su bashi hakuri su rokeshi kila ya barsu.
Bahijja ta kallesu ta ce, “hakkin ku ne fa ba sai kun roka ba, nan suka yi caaaa kanta mai gari ne ya tsawatar musu sukayi shiru.
Ya ce su kyaleshi da ita ya kalle ta “Ban san me yasa ba jikina ya bani in yadda dake naga ni a tattare da ke kina nufin abin da kika fadi kinyi niyar taimakon mu zamu baki dama in kinyi nasara Alhamdullahi dan kuwa duk cikin mu nan badan boko ba kuma wanda yayi karatu damu da yaran mu, duka ba mu san harkar kotu ba, ba mu san ya akeyi ba. Zaki iya mana alkawari ba zaki kai mu ki baro mu ba? ma’ana in kin ga abin yafi karkinki mu ne meki mu rasa?”Bahijja tayi murmushin jin dadi tare da fadin
“Inshaa Allah muddin ina numfashi sai inda karfina yakare na gode da wannan dama da, kuka bani.”Mai gari ya kalle ta ya ce,Menene
sharadinki?”Sharadina shi ne zaku bani wurin zama cikin kauyenku saboda ni bakuwa ce zuwa na garin nan ke nan bani da kowa kuma bani da wurin zuwa shigowana kauyen nan na ji ya kwanta min a rai in zaku taimaka ku ba mu wurin zama ni da Baba Audi mu zama daya daga cikin mutanen kauyen nan.”
Hmmm labari fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI gaba da kayawa kudai kuci gaba da kasancewa damu a Koda YAUSHE