MISBAH BOOK 3 CHAPTER 32 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 32 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Mai gari ya kalle ta “In dai wannan ne ba matsala sai dai amma ku, ‘yan ina ne daga ina kuke banga kunyi kama dayan kauye ba sai yan, birni me zai sa ku zuwa zaman, kauye?”

Bahijia, tayi murmushi tare da fadin “Wannan sirrin mune zanso ku barmu da sirrin mu.”

Bata kai ga rufe baki ba kuwa suka ga matasa garin sun shigo da gudu sun kawo labarin cewa ga Alhaji yazo, tare da mutanensa basu bata lokaci ba suka, nufi inda yake a mota zaune, a bakin titi yayinda mutanensa, sun fito suna, tsaye daya daga cikinsu ya ce, “Wane hukunci kuka yanke zaku fita ta arziki ko ta tsiya.”

Bahijia ne ta matsa gaba tare da musu wani mugun kallo na rashin muna tsoro ta ce, “Ba. ko daya muna nan a gidajenmu daram.”

Daya daga cikinsu ya kalli mai gari tare da fadin

Wannan shine hukuncin da kuka yanke?”

Ya girgiza kai “kwarai wannan shine hukunci da muka yanke lokacin mutumin dake cikin Bakar (Jeep dinsa ya fito hannunsa rike da wani karamin yaro fuskarsa sanye da bakin glass tare da bakar kwat (cot) farin sol, gashin kansa kwance tamkar na larabawa kana ganinsa kasan kudi da boko sun tsashi hakanan ya bawa Arla’ in baya kana ganinsa kaga kodai bafillatani ko shuwa a rab, Ya kalli, Bahijja da kyau sannan, ya mai da kallonsa kan, mai gari ya ce, Wacece wannan da za, ta yanke muku hukuncin abinda zakuyi ga rayuwarku? Zata kaiku ta baro lokacin da kukaga ana nike muku gidajenku da dukiyoyinku dana sani mara amfani zaizo muku har yanzu kuna da dama da zambaku ku matsa jejin gaba ku gyara ku koma can in gina kamfanina in baku aiki a kamfanin ina biyanku.”Bamu amince ba” Bahijia ta amsa “Gidajenmu da gonakinmu muke so ba zaman dokar daji ba da Albashi da ba zai iya siya mana abinci ba. Yayi mata wani mugun kallo alamar maganarta ya masa zafi ya kalli maigari ya ce Idan wannan shi ne hukuncin da kuka yanke to ku kwana da shirin sanin gobe kauyenku zai zama fili ko ku kwashe dukiyoyinku ko mu hada munike su duka kuma bani da wani sauran dama dazan baku.”• Yana gama fadi yaja hannun yaron zasu shiga motar Bahijja ta daga murya tare da fadin “Mu hadu a kotu.”Cak ya tsaya sannan ya juyo ya kalle ta kallon mamaki ya tare da fadin “Kotu”Ya sake hannun yaron tare da matsowa dab da ita ya ce, “Kotu yarinya kin san, da wa kike?”Ta kafa mishi manyan dara daran idonta tace,Ko ma da wanene( I don’t care) abin da na damu da shi kuma nasani shi ne kotu za ta kwatar mana hakkinmu duk matsayin mutum duk kudinsa.’kallonta kawai yake yana mamakinta ya kasa magana karo na farko ke nan da ya samu wani ya kalleshi ido cikin ido yayi masa magana tun bayan mutuwar matarsa ita kadai ke iya fuskantarsa ta fada masa abin da ke ranta wannan ya tuna masa da marigayiya matarsa da irin rawuwar da suka yi tuni yaji mutuwar yadawo sabuwa ciwon rashin yaji ya kuntata zuciyarsa yaji ya tsinci kansa a wani irin yanayi.

Basu ankaraba sai kukan yaron su kaji nanda nan hankalinsu ya koma kanshi Bahijjane ta nufi gunsa dasauri tare da daga shi yana bin raguna ya fadi ta kalleshi yana hawaye. Yaro ne dan shekara hudu. Ta share masa hawaye tana fadin sorry menene sunanka kallonta yake kawai ba tare da ya amsa ba, lokacin Baban nasa yayi saurin isowa tare da janyoshi ga mamakin sa sai yaga yaron ya koma ya mannewa Bahijja mamaki ya kamashi tsawon shekara biyu ke nan bai taba yadda da kowa ba sai mahaifinsa tun bayan rayuwar mamansa yana tare da kakarsa da sauran yanuwa amma bai taba yadda yaje gurin kowa ba, sai dai shi yana barci a nan ma yana tashi zai fara kuka sai an kai shi wurin Babansa wannan yasa duk inda zai je yake tafiya da shi bude baki yayi yana kallonsu.

Bahijja ta kawoshi jikinta tare dasa hannunta tana massajin gefen kansa tuni ya soma lumshe ido ya kwanta jikinta Bahijja ta maimaita tambayarta meye sunan ka Abbaaa” ya fada

cikin hardewar harshe.Ta ce “Abba Abba good boy ne zaije gun Baba su je gida nan ta dagashi ta nufi gun Babanshi ta mika shi wurin uban da ya bude baki yana musu kallon mamaki tun bayan hatsarin da sukayi mamarsa ta rasu bai taba magana bako sau daya sai a yau.

Sa hannu yayi ya karbeshi yana kallon Bahijja tamkar wata sabuwar halitta ta kelleshi ta ce, “ka kula da shi yana bukatar addu’a da taimako bashi da lafiya yana bukatar (therapy) da (training) (he is a special child). In yana samun, treatment zaiji sauki ‘yan’uwansa. Just find the right treatment kallon mamaki yadinga mata anya wannan ba Aljanabace ya akayi kika san matsalar dana?

Tasan tambaya da yakeyi a zuciyarsa, ta ce, “kar kayi mamaki Profession dina ne nasan, irinsu nasha dealing da irinsu manya da yara. Well mu hadu a kotu zamu shiga garin Gombe da Maigari mu shigar da kara zaka ji sammaci” tana gama fadi ta juya da confidence dinta.

Tuni ya manta da matsalar da ta kawo shi ya shiga tunanin lafiyar dansa, yaga ( hope) na samun lafiyar dansa Allah ya kawo masa dalili da sanadi ya fada a ransa. hartayi nisa ya bita ya ce “Inada offer?

“Eh” ya amsa san nan yaci gaba offer na shi ne, zan iya kyaleku da kauyen ba tare da mun shiga kotu ba amma da sharadin. zaki zama likitan dana har yasa mu lafiya.”

Ta kalleshi da kyau “Waya ce maka ni likita ce?”

“Ke kika fada, abin da kikayi kuma ya tabbatar mani da gaskiyar hakan tsawon shekara biyu bai yi magana ba sai yau bai taba yadda da kowa ba sai ke.”Kwarai ka fadi gaskiya” ta amsa masa zan yi tunani a kai na gani.” ta juya ta tafi.

Ya jima yana yana kallon ta kafin ya shiga mota ya lura dan nasa na kallonta har ta bace shin meye sirrin da yasa Muhammad yadda da ita?

Ya tambayi kansa da wannan tunanin ya isa gida hankalinsa ya karkata gareta zai iya yin komai dan samun lafiyar dansa wanda ba inda bai kai shi badan samun lafiyarsa har ya hakura yau ya ga dama ta samu.

Tunda Bahijja ta koma ciki ta shiga tunani tabbas yaron nan yana bukatar taimakonta ba don mahaifinsa za ta yi ba sai don shi kuma don Allah, Sannan dan mutanen kauyen nan su samu sauki samu dammar kwatar musu yancinsu da hakkinsu cikin sauki hakanan taji yaron ya shiga ranta fiye da tunaninta. Tana cikin wannan tunanin taji muryar Baba Audi tana mata magana cewa mai gari na kiranta ba bata lokaci ta mike ta je don amsa kiran Mai gari nan ta iske shi da tarin jama’arsa ganin yadda kowa yayi jugum sai

duka abin ya bata tausayi nan taji wata irin tsuwa taZo mata damin Allah ya bata damar da za ta taimaka musu cikin sauki.

Tana zuwa tayi sallama aka bata guri ta zauna kowa ya zubo musu ido ita da mai gari ana jiran mai zai ce da ita.nan yayi gyran murya ya ce,

“yata

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI gaba da kayawa kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE