Trending

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 33 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 33 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Bahijia mai kika yake akan maganar da kuka yi da

Alhaii Umaru ke muke sauraro ko har yanzu kina kan bakarki na sai mun je kotun.

Gyara zama tayi ta ce,ranka ya dade maganar

Zuwa kotu ta kau tunda har ya zo da wannan maganar ina ganin zamu yi nasara sosai sai dai ina son ku yarda dani ku bani komai a hannuna zan yi duk abin da ya dace ina da wani tunani akan haka amma ina son zan gindaya masa wasu sharadai idan ya amince zan yi masa abin da yake so amma matukar bai yi ba ina ganin zuwa kotun mai zaifi mana komai sauki a yi ta a wuce gurin ni dai abin da kawai nake so a gurinku hadin kanku da kwarin gwiwa idan ku ka bani insha Allahu babu mu babu matsala.”

Wani daga cikin jama’ ar ya ce mun ji mun kuma amince da ke matukar zamu yi nasara akan wannan bawan Allah ko wane irin gudummawa kike so daga garemu zamu baki fatan mu dai kada a Zo a samu matsala idan kuwa aka samu da ke zamu yi kuka.”

Murmushi tayi ta ce, “insha Allah Baba babu wata matsala da za’a samu a tare da ku zuba min ido zan yi iya karkokari na ganin kun dawo cikin kwanciyar hankalinku da barin zullumi da kuke kwana kuke tashi da shi.”

Mai gari ya ce,babu komai Allah ya taimake mu

gaba daya.”duka wurin suka amsa da Amen.

Da wannan tattaunawar suka watse kowa ya koma gurin da zai je. Kai komo ya shiga yi cikin dakin sa yana jinjina kalman Bahijja domin jin komai yayi yana dawo masa cikin kwanyarsa a bayyana ne ya ce

Wacece wannan meye hadinta da wannan kauye sannan me, takeji da shi da har take ikirin za ta kai shi kotu ita shin ta san shi wane da har take masa barazaran kaishi kara nan take wata zuciyarta gargadeshi A’ah Farouk maganar jayayya da jin kai naka a yanzu dole ka zanye shi lafiyar danka ita ce abu mafi muhimmanci fiye da komai a rayuwarka.” A bayyane ya ce, “Gaskiya ne dole na aje komai nayi kokarin ganin lafiyar Muhammad domin ita ce komaina. amma zan nuwa yarinyar nan dole tayi min abin da nake so idan bahaka ba zan rushe kauyen nasu ta karfi da yaji ba zan daga musu kafa ba ko saurara musu ba amma duk da haka zan bi da ita yadda ta so da farko idan taki yarda ni kuma sai nayi amfani da nawa Matsayin da power. haka dai ya shiga zance zuciya ya kulla ya warware.

Misalign karfe bakwai na safiyar ranar ta fito tsaye take jinkin bakin wata bukka tana sauraron dadadan kukun tsintsaye yadda suke rera kukansu gwanin dadi da kuma dadin sauraro gefe guda kuma shanune garke guda sai kai kawo suke suna cin ciyawa gwanin sha’awa ga gilmawar jama’a kowa da abin yakeyi  wasu mata na tsaye bakin shanu suna tatsar nona. Haka kawai taji yanayin safiyar dana garin suna matukar burgeta hade da jefa nishadi cikin zuciyarta.Nan take ta dinga tuno wasu yanayi masu dadi da suka riga suka shude cikin rayuwarta wanda tana jin HAR ABADA ba zasu taba barin kwanyarta ba sai dai taji tunanin Deeni na kokarin yin galaba akanta haka tayi kokarain danne hakan har sai da ta fado kan rayuwarta da margayi Dr. Misluhu nan take ta din ga tuno wasu.

Bahijja a yanzu baki da wani lokaci naki sai na

AL’UMMA ki daure kina kula da rayuwar jama’ ar da kike tare kina yi musu duk abin da da kika san zai sasu farin ciki kada ki dinga nuna gajiyaawarki akan dukkan wata AL’UMMA da zaki rayu da ita ki zage ki ga kin taimaka musu iya karfinki sauran ki barwa Allah, Bahijja na yarda da nagartarki zaki iya rike kanki a duk inda kika samu rayuwarki burina da naki muga muntaimakawa AL’UMMAr da muke tare da ita.

Bahijja mu yi kokari da wannan aikin namu don mutaimakawa duk wani mai bukatar taimakonmu wannan shi ne ribar da zamu samau cikin rayuwar baki daya. Bahijja ke ce rayuwata ke ce farin cikina ina son naga baki farinki a ko da yaushe ban son ganin abin da zai taba maki zuciya sannan ina son ki .. zama jaruma akan komai na rayuwarki nasan ki da iya jure komai na rayuwa komai dacinsa kiyi hakuri da rayuwa da mutanen da suke cikinta.

Duk ban sani baya kaman Hankalinta ya tashi data gama tuno kallaman tsohon mijinta na farko wanda yayi mata wannan maganar daf da zai bar duniya wasu irin hawaye” masu dumi suka zubo mata a bayyane ta fara fadin

Allah sarki Misluhu na Allah yayi maka rahama yasa Aljanna firdousi ce makomarka ka tafi ka bar ni da tarin bakin ciki da wahalar rayuwa kai kadai ne namiji mai gaskiya da alkawari cikin rayuwata nayarda da duk abin da ka fada min kuma zan yi fiye. da yadda kace nayi,nayi rashin gwarzon masoyi MAI SONA mai alkawari da gaskiya halayyarka ta gari ta bika.

Nan take taji son danta Muhammad ya dawo mata sabo taji kewarsa da kaunarsa na damunata yaron da aka rabata da shi tun yana shan nono.

Wayyo Allah Muhammad dina a ina kake yanzu kana raye ko kana mace duk ban sani ya kamanninka suke duk ban sani ba, lallai iyayen Misluhu basu yi min Adalci ba ni da Muhammad haka nan hawaye ya shiga zubo mata duk bata sani ba.

Ji tayi an dafata tayi saurin juyowa sai suka hada ido. da Baba Audi nan ta kalle ta ta ce Bahijja mai yasa ki kuka alkawarin da kika yi min ke nan idan ba kyau tausayin kanki ya kamata kina tausayawa abin da yake tare dake ki tuna bafa ke kadai bace, yawan damuwar da zaki shiga kan iya yiwa abin da ke cikin ki illa, Bahijja ina dauriyarki da shanye bakin cikinki matukar idan baki yi kokarin watsar da tunanin Deeni da rayuwarsa ba to lallai ba zaki taba fita daga cikin damuwar da kike ciki ba,ke musulmace dole ki yarda da kaddara da kuma abin da da kaddararki za ta baki.

Ganin ki cikin damuwa ni ma yana saka ni cikin haka dole ne kiyi kokari kina manta duk abin da ya faru a baya kina hangen abin da zai faru da ke a gaba,ina ganin Wannan kadai shi ne abin da zamu saka a gaba.

  • Cikin jin dadi ta dubi Baba Audi. ta share hawayenta ta ce Baba Audi na gode da kasancewarki uwa ta gari a tare dani na kode da dukkan shawarwarinki sai dai ina son ki sani cewa
  • ko kadan ba tunanin Deeni ne ya sani kuka ba ina tunanin margayi ne da Muhammad dina da aka raba ni da shi wannan na tuna yasa ni zubar da hawaye amma tunda bakya so zan dai na kamar yadda nayi maki alkawari a baya.

kuma ina son ki sani cewa ina yin iya bakin kokarina domin na manta da tunanin Deeni dama rayuwarsa gaba daya domin na samu natsuwa yadda zan ginawa kai na sabuwar rayuwa, don haka ni yanzu baya gabana gaba daya kuma ba zai zamo min wata matsala da za ta dame niba tunda na bar shi na bar shi HAR ABADA.”

Baba Audi ta ce shi Ke nan Bahijja Allah ya ba

‘mu lafiya da tsawan rai ya kuma rabaki lafiya da abin da ke jikin ki,ina gani ki mu koma ciki mu samu mu karya kumallo domin naga sun gama gabatar mana da komai.”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE