MISBAH BOOK 3 CHAPTER 34 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 34 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

 

 

Shi Ke nan mu je nan suka koma cikin gidan

Mai gari inda masaukinsu yake daki ne aka basu babba ginin laka wanda yasa dabe da siminti,nan* suka basu domin suna kwana a ciki.

Kwance take a dakin tá wanda ya zama mallakarta a yanzu yau kwana biyu Ke nan Alhaji Umar bai sake waiwayar kauyen, ba har ta fara tunanin anya ba za su je kotu ba domin basu san shirin da yake yi akansu ba.

Bata gama tunanin ta ba sai ga Yafendo ta leko tana sanar da ita cewa Mai gari yana son ganin ta Alhaji Umaru ya zo.

Cikin sauri ta mike ta zari hijabinta ta fito don taje taji dame yazo kuma.tana fitowa ta hange shi jikin motarsa inda ya saba tsayawa nan ta nufi gurin Mai gari don amsa kiran da yayi mata.

Guri ta samu ta zauna yana ganin ta zauna ya baro jikin motarsa ya nufo inda suke nan ta tambayi mai gari ya suka yi da shi,ya ce mata ke ya bukaci a fara kira tukunna.

Yana rufe baki ya karaso gurin ya zauna bayan yayi musu sallama fuskar Bahijja daure ta amsa sallamar, ganin yadda yanayin fuskarta ya nuna shi ma sai yayi amfani da abin da ya gani amma cikin zuciyarta fushin nata na gaira babu dalili yana burgeshi.

Gyara murya yayi sannan ya ce kun jini shiru kwana biyu wallahi wani UZURI ne ya tsayar dani amma tunani na yana nan sai yau na samu kai na shi ne nazo mu yi ta ta kare cikin sauki kauyenku ko kama sawa a bugu muku shi har yanza kuna da dama ta karshe da zan baku kamar a baya.

Taurin kai ko ja dani da nuna isa babu abin da zai janyo muku idan ba wahala ba ni mutunne fitacce mai alfarma ta ko ina ga kudi ga power bana taba neman abu na rasa kada ku ga ina ta fadin zan yi abu ina fasawa ku yi tunanin bazan iya ba don haka nazo da baku UMARNI matukar kuna son kauyen ku to ku saka baki tayi min abin da nake so idan ba haka kuma.

nan ya daga kai suka kalli juna shi da Bahijia ido cikin ido.

Nan tayi saurin karasawa da cewa “idan ba haka ba kuma me? Ka karasa abin da zaka fada mana ka tsaya kana kallo na,Mallam bari na fada maka kada ka ganmu yan kauye kayi tunanin ba mu san yancin mu ba ko ba mu da damar ja da kai ko kai wanene a kasar nan baki daya baka da right din da zaka hanamu yin abin da da zamu yi mu karbi hakkin mu da kake kokarin danne mana I don’t care how more Connection da kake da shi da wani power da kake magana da shi sam duk wannan baya gabana abu daya na sani mu yan kasa ne kamar kowa muna da ikon makaka ako wane kotu dan mu nemi hakkinmu a gurin ka.

Kuma baka da wani right a kai na da zaka ce dole nayi maka abin da kake so baka isa ba babu wannan batun a tare da kai kaje kawai ba zamu yi maka abin da kake so ba kawai mu hadu a kotu yadda kowa zai gane matsayinsa kaje kayi aiki da power da Connection dinka mu zuba da kai mu kuma zamu baje gaskiyarmu da mu da kai maga wanda zai yi nasara a tsakaninmu.”

Maimakon ya nuna fushi da damuwar irin wannan kalman da tayi masa sai kawai ya. ga ta kara burge shi yaji yana da interest sosai akan ta kallonta yayi sosai ya kura mata ido yana mamkin yadda take daukar zafi haka.nan ya kada harshe ya ce

Shi ke nan tunda baka kika fada ni zan wuçe zan kuma turo a rushe kauyen naku idan ya so kema sai ki yi amfani da power din ki yadda zaki ji dadin make ni a kotu,idan kun ga dama to ku fara tattara kayanku a yau domin gobe da sanyin safiya kauyanku zai zama jeji.”

Yana gama fadin haka haka ya daga kai ya kalli jama’ar da ke gurin don yaga yadda yanayinsu yake,bai gama tunanin haka ba wani daga cikin jama’ar cikin zafin zuciya ya ce, “Ai ba mu amince da haka ba dole kiyi masa abin da yake so,idan dai har da gaske kike na cewa zaki taimaka mana iya karfin ki to yau ga ranar da zaki taimaka mana ta zo matukar ba yaudararmu zaki yi ba ina ganin kawai ki amince ba don komai ba sai don mu zauna cikin kwanciyar hankali mu huta da fargabar da kullum muke kwana muke tashi acikin ta amma idan baki yi mana haka ba to kin nuna cewa dama can ba taimaka mana zaki yi ba kin yi ne kawai domin ki hana mu zaman lafiyar,idan kina so mu yarda da abin da kika fada mana to kawai ki karbi abin da ya zo maki da shi.”

Yana gama fadin haka nan Kuwa guri ya kaure da surutu da hayaniya kowa na cewa Jauro muna bayanka lallai abin da ka fada haka nan nan -dai gurin ya yamutse kowa da irin abin da yake fada.

Wani irin kallo yayiwa Bahijja sannan ya saki murmushin mugunta domin ‘alamu ya nuna tun a nan zai yi nasara, wani irin kallon tsana da haushi tayi masa batace da shi kalla ba nan cikin dakakkiyar murya ya dakatar da su.kowa yayi tsit nan ya mike ya ce zan dan yi nesa kadan da ku dan na baku dama ta karshe kafin gobe domin komai na iya faru a goben kuyi shawara ku tsayar da magana daya ina sauraanku idan kun tsayar da magana ina. cikin motata.”

-Yana gama fadin haka ko kallan inda Babijja take bayyiba ya juya ya tafi haka ya dinga jinsa cikin’ wani sabon nishadi yana jin nasara a jikinsa lokacin samun saukin Muhammad dinsa yayi.

Shiru Bahijja tayi tana sauraron dukkan hayaniyar jama’ ar kauyen da har yanzu basu dai na hayaniya ba. Mai gari ya ce ‘yata wane shawara” kika tsayar kin dai ji abin da da jama”a suka fada meye mafita ni dai tabbas na yarda da duk abin da kika fada zaki yi, zaki iya ne yasa kika fadi hakan amma yanzu gashi komai yana daf da kure mana muna kan damarmu ta karshe ni dai yanzu bani da wani abu da zan ce muna ga Allah muna gareki-komai kika fada ina bayanki sai dai ki kuma duba masalahar jama’a da kuma abin da suke so.”Ranka ya dade ban samu goyan bayar da nake nema wajan jama’a ba amma duk da haka zan yi abin da kake so na so abarni mu je ga kotu badan komai ba sai don na nunawa jama’ ar kauyen nan cewa su san “yancinsu ko dan gaba domin ko a can birni akwai irin azzaluman masu kudi da suke takama da dukiyar da Allah ya basu don su danne hakkin wani,amma da zarar anje kotu sai Allah ya taimake su su yi nasara akan haka,amma shi nan yazo ya tsorata ku yana muku barazana har sai da yagama jefa ku cikin tsoro.

Na sani ba abu ne mai sauki ba raba mutum da inda yake rayuwa lokaci guda wannan kadai zan duba nayiwa kowa UZURI don haka ranka ya dade zan yi abin da kake so da kuma wanda jama’ ar kauye ke bukata insha Allah yadda nayi alkawarin zan taimaka muku zan yi farin cikin ku shi ne nawa don haka na amince zan masa abin da yake so amma fa ba dan na ji tsoran furucinsa a’ ah nayi ne don ganin hankalin kowa ya dawo jikinsa saboda wanda suke ganin kamar bazan yi abin da na fadaba don haka na amince.”

Nan da nan guri ya cika da sowa kowa ya shiga murna da kyar Mai gari ya dagatar dasu.sannan

Bahijja ta ce kuje ku kirawo shi amma da sharadin da zan bashi idan ya yarda zan amince idan kuma yaki ni ma a gobe zan makashi a kotu,a yi masa magana yazo yaji nawa dokokin.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE