MISBAH BOOK 3 CHAPTER 35 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Jin haka da dama jama’ar wurin jikin su yayi sane ba jimawa sai gashi ya dawo tare da yan aiken nan suka hada ido da Bahijja nan ta yi saurin dauke kanta tare da daure fuska.

ya mai da dubansa ga Mai gari ya ce, “Ranka ya dade kun tsayar da mafitar Ke nan to a ina muka tsaya?”

Mai gari ya ce, “gata nan ita ce za ta yi maga bayanin komai.”

Ya ce “Babu komai.” nan ya mai da kallonsa gareta ya ce, “ke nake sauraro. ya fada cikin dakewa da shan kamshi.

“Na ji na jeye shigar da kara kamar yadda nayi furuci abaya,na kuma yardazan zama likitar yaronka amma kafin nan ina da wasu sharadi da zan baka kafin nan idan ka yarda da shi babu matsala saika tsayar da ranar da kake so na fara duba yaronka idan kuma kaki zuwa kutunmu yana nan babu fashi.” Murmushi yayi yace,ke nake sauraro ki fada komai tsaurin abin da zaki fada bana jin zanki amincewa ki fada na ji.

•Sharadi na farko siri ne bana son ka shiga rayuwata ko yi min shishigi akan duk wani abu da zaka gani a tare dani,ka barni nayi aikina na matsayin likitar danka babu ruwanka da rayuwata.

Sai na biyu ya zama dole a rubuta takarda na yarjejeniyar ka janye batun korarmu daga kauyenmu idan har na zama likitar danka babu magana biyu da zarar yaronka ya samu lafiya babu wata Dangantaka a tsakaninmu da kai babu wani abu da zai sake shiga tsakaninmu bayan offer dinka ta gama aiki.”

Sai na uku shi ne zamu rubuta kasaka hannu ni ma na saka haka shi ma ranka ya dade zaka je ka bugu copy uku ka dauki dayani ma na dauka shi ma ya rike nashi,ina ganin idan ka karbi wannan tsarin to kawai ka fadi ranar da kake so na fara duba yaronka ni a shirye nake ka ji wannan sune ka’ idojina idan ka yarda, to shi Ke nan idan kuma harka saba daya daga ciki ina janyewa na kaika kotu domin ni bana hada hanya da dukkan mutumin da yake karya alkawari.

Ta gama fadin haka cikin daurewar fuska.shi kuwa sai abin ya bashi dariya domin duk abin da da ta fada babu wani abu da zai sa yaji ba zai amince ba domin shi ko kadan bai ga wani abu mai wuya ba cikin sharadin data gindaya masa ba.

Mikewa yayi ya ce bani minti biyu ina zuwa nan jim kadan yaje ya dawo dauke da wani file da wasu tarin takarku ya dakko wani plain pepar ya fara rubutu duk gurin aka tsit kamar kurame nan yagama rubutu abinsa ya mika mata ta fara dubawa.

Duk abin da ta fada babu wanda ya manta komai ya rubuta nan ta dago kai ta kalleshi ta ce, “yayi bani pen mu saka hannu.”

Nan ya mika mata ta karba ta saka hannu sannan ta mikawa mai gari tare da nuna masa inda zai saka hannu nan ta mika masa ta ce gashi kai muke sauraro kaje ka kawo mana namu copies din sai mu tsayar da rana.”Babu damuwa ki bani nan bada jimawa ba,zan kawo muku.”yana gama fadin haka bai bata lokaci ba yayi sallama dasu ya mike ya tafi zuciyarsa cike da nishadin samun masarar da yayi tare da jinjina wannan kaifin basira na wanna baiwar Allah da bai sannan sunan ta ba koma dai meye shi dai yana ganin shi ne ya fisu cin riba da wannan tunanin ya karasa motarsa ya ja ya tafi.

Bayan tafiyarsa nan kowa ya shiga munar tare da jerowa Bahija godiya da yi mata fatan alheri cikin rayuwarta.wani irin farin ciki ya shiga ratsa mata zuciya domin kowa ta daga ido ta gani sai ta ga tarin farin ciki akan fuskarsa haka itama ta dinga jin nata farin cikin yana karuwa taji ta tamkar bata da wani damuwa domin yau burin ta ya cika ta ta cikawa tarin jama’ ar kauyen burin su.

Kai tsaye ta nufi cikin gida ta iske Baba Audi na kishingide tana jan carbi tana ganin ta cikin farin ciki tayi saurin mikewa ta ce,Yau wane albishir

-Bahijja na ta zo min da shi yau naga wani irin annuri akan fuskarta wanda na dade ban ban gani ba mai ya faru ne dake.Cikin walwala da fara’a ta ce Baba Audi ina farin cikine yau na cika alkawarin da nayiwa yan kauyen nan yau nayi nasara akan wannan azzalumin mai kudin da yake kokarin korarsu a mahaifarsu. Baba Audi yau nayi nasara na karbe musu kauyen su a hannun su na saka su farin ciki na fitar dasu daga cikin alhini da tashin hankali hade da fargabar da suke ciki kullum.

Yau naga tarin farin ciki a tare da suna godewa

Allah da yasa nice nayi sanadiyar kwanciyar hankalin su babban farin ciki na shi ne na cika alkawarin da na daukar mu su, Baba Audi yau ina ji na kamar bani da wani damuwa tunda na cika alkawari.

Dama haka mutum yake ji idan ya cika alkawarin da ya daukarwa mutum amma shi ne wasu ba sa ba shi muhimmanci haka, hakika duk mutumin da yayi alkawari bai cika ba to tabbas yana cikin takaici da damuwa.

Don haka zan ci gaba da cika dukkan alkawarin da na daukarwa kai na da wasu ma da nayi mu su.nan taji wasu hawaye sun zubo mata domin famin abin da yake cikin zuciyarta, nan ta ce

“Baba Audi ina matukar jin takaicin yadda Deeni bai cika min alkawarin da ya daukar min ya manta da komai ya ci amanata duk da tarin alkawarurukan da yayi min ya manta da su ya take da kafarsa sai da ya ga ya kassara min rayuwa ta da farin cikin da muka dade muna ginawa,

Baba Audi yaushe zan manta da haka a rayuwa ta yaushe zan manta, Deeni kaci amanata.” nan ta fashe da kuka.

Da sauri Baba Audi tayi saurin hadata da jinkinta tana cewa haba Bahijja ban sanki da haka ba ina dauriyarki da danganarki Deeni bai kassara maki rayuwa ba, ya dai doraki akan hanyar da zaki bi ki kara karantar ya rayuwa take a baki darasi mai tarin yawa ya baki wani illimi mai tarin yawa wanda ke da kanki zaki koyar da wasu wannan ilimin kumazai yi musu amma fani,na sani sosai abin da Deeni yayi maki bai kyauta ba amma har kullum kina tunanin cewa kaddara ce ta baki hakan ba wai shi ne ba a’ ah idan kina duba haka zaki yi saurin manta hakan cikin zuciyarki nan da nan.

“Gaskiya ne Baba Audi lallai kaddara ce ta bani haka KADDARATA KADDARA CE mai girma da ta tashi zuwa gare ni sai tazomin da fadi yadda ba zan taba mantawa ba.Zaki manta Bahijja ki yi kokarin hakan ki gani zaki ga kin manta har abin ya zo ya daina damun ki amma idan kina barin duk farin cikin da zaki shiga zaki na tuna baya to lallai haka zaki yi ta rusa farin cikin ki amma idan kina manta komai zaki ga komai zai ta wucewa har ma ki manta kin taba shiga wani tashin hankali ki gwada hakan ki gani.”

Zan gwada Baba. Audi amma kina taya ni da addu’a domin manta Deeni da abin da yayi min a rayuwata ba karami bane har gobe ina jin hakan cikin rai na amma zan dage naga nayi abin da kika ce.” nan ta shiga share hawayen da yake zubo mata Baba Audi ta shiga bata baki tare da bata kwarin gwiwa na ta cigaa ba da juriya da hakuri komai zai

Hmmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE