MISBAH BOOK 3 CHAPTER 36 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

zamo kamar ba a taba yi ba,da wannan ban bakin suka wanzu a haka.

Bayan kamar awa guda da tafiyar Alhaji Umar ya dawo dauke da copies din takardun yarjejeniyarsu, yana zuwa aka nemo Bahijja ya mika mata ta karba ta ce komai yayi daidai don haka yanzu yaushe ka shirya zan fara zuwa wa yaronka Therapy domin na fison na fara cika alkawarin dana dauka cikin gaggawa.”

Murmushi yayi ya ce ni idan tani ne yau ma ki fara idan ba zaki damu ba amma duba da kamar baki shirya ban zanyi maki UZURI zuwa gobe sai ki shirya zan turo masu daukarki zuwa cikin gari domin ki fara aikin ki, da fatan zaki bani hadin kai.” Ta cira kai ta dube shi tace batun hadin kai kuwa ai tuni muka gama tunda komai mun yi shi a rubuce ka cika min alkawari nani ma na yi maka naka don haka karka damu Allah ya nuna mana goben ina nan ina jiranka ni zan koma sai goben.” Bata jira ta ji mai zai ce ba.bin ta yayi da kallo yana mamakin yadda take yin maganarta komai a takaice kuma duk abin da za ta fada tana da point akansa, lallai itan mai tsarice da bin doka haka yaji komai nata yana burge shi haka ya dinga jin wani irin abu a tare da shi kamar dama can akwai wani correction a tsakanin su,take yaji wani nishadi yana ta dirar masa cikin zuciya ya dingajin tamkar Muhammad dinsa yagama jin sauki domin a yanzu bashi da wani abu da yake da muhimmancin son gani sama da lafiyar Muhamma”DANNA DOMIN CI GABA” 

[expander_maker id=”2″ more=”Read more” less=”Read less”]Read more hidden text

Kowa na cikin kauyen ya samu natsuwa tun bayan da mai gari sa aka yi shela kowa ya fito aka taru nan ya sanar da su cewa komai ya daidai ta babu batun korarsu daga kauye tunda sun tsayar da magana anyi komai a rubuce Bahijja za ta kula da lafiyar yaronsa har zuwa lokacin da Allai zai bashi sauki don haka sai ku mu dukufa sakata cikin addu’a kun ga dai domin ta ga yadda muka koma cikin farin ciki da kowa ka ganshi yana cikin zulumi.”

Nan fa guri ya rude kowa da irin addu’ar da yake yiwa Bahijja da fatan nema mata dacewa cikin rayuwarta haka dai. taro ya waste Bahuja ta koma ciki zuciyarta fal da nishadi da farin ciki ganin yadda kowa yanzu yake cikin walwala sabanin da da kowa ka ganshi cikin rudani. Hakan taji itama wani irin farin ciki na ratsata gain kowa domin ita yake farin ciki nan taji son kauyen da kaunar mutanan cikinsa.

Ta saka a ranta za ta yi musu duk abin da zai saka su jin dadi da kuma kawo musu ci gaba a cikin rayuwarsu baki daya.

Washegari ta gama shirinta tsaf shi kawai take jira zata ji ya turo masu daukar nata kamar yadda ya . fada jiyan gefe guda zuciyarta cike da dokin son ganin yaron nan domin haka kawai taji ya shiga ranta tana so kuma ta ganshi.

Goma daidai na safiyar ranar aka aiko daga gurin mai gari idan ta shirya ta fito ga masu daukarta sun zo,babu bata lokaci ba ta zari hijabinta kamar yadda

kowa ya sani dama can Bahijja ba ma’ abociyar kwalliya ba ce a da can barema yazu da komai na rayuwar baya birgeta kawai tana yin rayuwar ne ba don farin ciki ba domin duk wani abu da za tayi farin ciki a kansa yanzu tayi nesa da shi.

Nan tayi sallama da Baba Audi da sauran mutan gidan suka yi mata addu’ a akan Allah yasa a fara a sa’a,sannan ta fito gurin Mai gari albarka ya saka mata sannan yayi mata fatan alheri haka taji tsohon na burgeta yadda ya mayar daita kamar yar cikinsa don haka ita take bashi girma kamar mahaifinta.

Haka ta nufo motar mota ce rantsatsiya ta zamani domin ba da ita Albaji Umar ke zuwa ba,suna ganin ta suka yi sauri fitowa daga cikin motar mutane su biyu suka gaisar da ita cikin girmamawa sannan daya ya bude mata motar ta shiga baya ta amsa sannan ta yi masa godiya.suka ja suka tafi.

Tunda suka shiga cikin garin Gombe ta fara jin wani irin dadi da nishadi na ratsata sukowar jama’ ar da ta dinga gani kowa na ta kai komo abin ya dinga burgeta ga kuma wani irin ci gaba da garin ya samu sosai yawan ginegine da kuma manyan titi ta ko ina duk da garin ba cukoso ne da shi da yawa ba amma ta yaba da garin sosai.[expander_maker id=”1″ more=”DANNA DOMIN CI GABA” ]Read more hidden text[/expander_maker]

Tafiya suke tayi tana ta yin kallon ta haka ta din gajin zuciyarta na yi mata sanyi. unguwar da suka shigo GRA ne unguwar tayi masifar burgeta kasancewar garin yana hills and Belly mana’ a tudu da kwari nan zaka hango wasu gida a zaman wasu kuma a kasa kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ne sai ka ganka kamar a wata kasar gidaje ne na gani na fada duk anyi su akan tsari dole wanda ya je ya gani abin ya burge shi.

Unguwar da suka shigo haka take shiny gida ne manya manya a cikin unguwara kowa yana gani kamar nasa yafi na dayan kai da kallon gidajen kasan bakarya wanda suka mallaki gidajen ba kananan masu dukiya ba negida ne manya guda biyua a unguwar wanda suka fi sauran girma da tsaruwa nan ta ga sun muf dayan suna kara sowa kuwa geta a bude bayau.

Gate na budewa ta fara hango kawatuwar gidan hakika mutumin nan mai kudine nagaske abin da Bahijja ta fada cikin ranta sannan ta ci gaba da fadi cikin ranta dole ya ji kai da isa ya kuma nuna cewa yana da power domin duk mutumin da ya mallaki gida irin wannan ba a garinsa ba kawai har cikin kasar dole yana da conection da manya don haka dole ya zama mugu yadda zai dinga danne hakin masu karamin karfi. Katon gida ne sama da kasa sai guda biyu masu kama da juna sun katuwa iya kawatuwa daga can gefe kuwa wani karami ne flat ga kuma shuke shuke ta ko ina cikin gidan domin har raund about ne karami cikin gidan tsakiyarsa ruwa ne ke feshi ga manyan tattabaru na turawa sai shawagi suke tayi cikin gidan irin manyan nan farare tas irin na turawa.can gefe parking space ne motoci gasu nan birjik kai tsayawa fadar yadda tsarin gidan yake ma bata lokacine domin komai tsarin gidan abin birgewa ne kamar ba a kasar nan ba ku ayyana komai da kanku amma dai gidan yayi iya yi.[expander_maker id=”1″ more=”DANNA DOMIN CI GABA” ]Read more hidden text[/expander_maker]

Duk cikin yan sakanni kadan Bahijia ta gama hararo iya abin da ta gani tana cikin motar.don haka tana fitowa daga cikin motar kanta kasa bata tsaya wani kalle kalle kalle ba bare wani ya ganta ya ce tayi kauyanci. Tana daga idanunta can ta hango shi tsaye ta saman bene ya sako mata ido yana kallonta duk da yake daga nesa yake ta gano ita yake kallo nan tayi saurin kau da kai kamar bata ganshi ba.

“Haka suka taho yana gaba tana binsa a baya kanta kasa cikin natsuwa dama kowa yasan da haka.suna isowa falon yana sakkowa, falon kam babu magana abu daya ne ya fadar mata da gabanta da ta shigo falon yadda tashi sak irin kamshin room freshner da suke amfani da shi a gidansu kuma zabin Deeni ne yana matukar son shi domin shi ne ya sa mata son kanshinsa haka ita ma taji duk duniya bata da Room freshner da take so sama da shi.

Nan ta tuno wani lokaci da Deeni ya dawo daga asibiti ya shigo cikin dakinsa ya same shi tsaf ga gamshin room freshner na tashi nan ya rutse ido yana shakarsa yana bude ido sai ya ga Bahijja a gabansa nan yayi saurin bude hanyayensa ta zo ta fada jikinsa ya ce, “Misbah na kinyi abinda mijin

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE