MISBAH BOOK 3 CHAPTER 37 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

ki zai ta sonki har karshen rayuwar wannan kamshin da nake shaka bashi kadai nake shakaba har da so da kaunarki nake shaka, Misbaha ina son ki da wannan kamshin naki, yadda kike saka ni nishadi da karamin sonki da sha awarki don Allah kada ki gujeni duk runtsi duk wuya zanta nuna maki so da kaunata HAR ABADA nayi maki alkawarin haka Misbah na ina sonki.”

Cikin dakiku tayi wannan tunanin nan da nan ta kori tunanin cikin ranta ta ce Deeni karya kake. tayi kokarin daidai ta •natsuwarta don kada ya gane akwai wani abu da ya taba zuciyarta da yake ita mace mai hikima.

“Barka da zuwa my palace Doctor kin cika alkawari.”

“Barka kadai ya gida,a ni bana karya alkawari matukar na daukarsa don haka kai ma ina mai baka shawara ka zamo mai cika alkawari domin ka zauna lafiya.

“Godiya nake likita da wannan shawara da kika bani zan kokarta naga ni ma na zama mai cika alkawari.”

“Uhmmm” iya abin da ta ce Ke nan. sannan ya ce ki zauna bari na zo maki da patient din naki yana tare da Hajiya dakyar yaje gurin ta.”

• “Babu, laifi ina jiranka.”nan ya juya yayi ciki nan ta samu damar sake shaker kamshi nan taji kamshin yayi mata wani irin rashin dadi taji gaba daya ta tsani kamshin. domin yana tuna mata da rayuwarsu da Deeni ita kuma bata kaunar abin da da zai sa za ta na tuna Deeni da rayuwarsu da ta shude.

Sallamar da yayi yasa tayi sauri dago idannunta

don ta amsa tana cira kai suka yi ido biyu da Yaron

kallon junansu suka yi nan ya tsaya yana mata

kallo na tuno ina ya taba ganinta nan ta saki

murmushi.

Da sauri ya saki hannun mahaifinsa da sauri ya

nufota da gudu yana fadin “mama oyoyo.

sai dai furucinsa baya fita sosai. Itama cikin sauri ta bude hannayenta ta yi kasa daidai tsayinsa ta rugeme

shi.cikin jin dadi ta ce, “oyoyo My Boy Abba kana

lafiya.” Wani dadi yaji ya kama shi tare da wani nishadi

hade da wani irin mamaki da wannan Dangantakar

dake tsakaninsu ya rasa wane irin kauna ne lokaci

gudu ta gudana tsakanin dansa da ita kamar dama

can sun san junan,amma da yayi tunanin Allah

lokaci guda yake yin abu idan ya so hakan ya kasance.

Nan ta raba shi daga jikinsa ta mayar da kallonta

ga mahaifinsa ga mamakinta sai ta ga bashi kadai

bane wata Dattijuwa ce wadda ko ba a fada a fada

maka ba kasan ita ce mahaifiyarsa domin komai

irin nata ne farace ita sosai kana ganinta ka ga

asalin fulanin Gombe kyakykyawa, da ita daga

ganinta kasan tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Cikin girmamawa ta gaida ita ta amsa tana

murmushi ta ce, “*sannun ki yata barka da zuwa.

“Yawwa na gode ya jikin Abban. Cikin rashin fahimta Hajiya ta ce, “Abba kuma wane Abban?”

Cikin murmushi Alhaji Umar ya ce Hajiya tana nufi Muhammad ne kin san bai iya fadin sunan kowa ba daga mama sai Abba a ranar da muka hadu ta tambaye shi sunan sa yace mata Abba shi ne tayi tunanin haka ne sunansa.”

Murmushi ta yi ta ce Allah sarki ai Muhammad sunansa mahaifinsa yake kira da Abba.”

Bahijja ta ce,

“Ayya ai nayi tunanin sunansa ne

haka to Allah ya bashi lafiya.”

Gaba daya suka amsa da “Ameen.”

Hajiya ta ce,

“yata ya sunan naki ne?” ta fada

cikin murmushi tana mai kallon Bahijja.

“Sunana Dr. Bahijja Hajiya.”

“Ni kuma sunana Umar Farouk Sulaiman amma wasu suna kirana da Alhaji Umar amma dai ke zan so kina kira na da Farouk kamar yadda mafi yawan jama’a ke kirana.”

“Ni kuma suna na

Hajiya Salamatu nice mahaifiyarsa.”

Hajiya ai naga alama saboda ga kama nan kowa ya gani ko bai tambaya ba zai san bakan sai dai ban ga maman Muhammad ba ko bata nan ne?”

Nan da nan yanayinsu ya canza bai iya magana ba sai Hajiya ce ta ce, “Allah sarki ai ta rasu yau shekara biyu Ke nan a sanadiyyar hatsari da suka daga hanyar Abuja zuwa Gombe wanda sanadin haka ne Muhammad ya gamu da wannan lalurar da yake tare da ita.” Cikin alhini da nuna tausayawa ta ce Allahu Akbar Allah yayi mata rahama yasa Aljanna makoma da sauran magabatan mu da iyayenmu.”

Gaba daya suka Amma da “Ameen.

Nan ta mai da kallonta gare shi ta ce, “ina maka ta’aziyar matarka Allah ya jikanta.

“Nagode sosai Babijja Allah ya bada lada ya bar zumunci.”Bata ce komai ba ta mai da kallonta kan

Muhammad ta janyo shi fikinta tana shafa masa kai tace,ina son ganin maganin da kuke masa amfani da su domin a kwai abin da nake son dubawa.”

Babu komai bari na kawo ki gansu ya mike cikin sauri shi kuwa Muhammad sai wani narkewa yake a jikinta Hajiya na murmushi ganin yadda

Muhammad yake mata mutumin da bai yarda da kowa ko ita idan ya yarda da ita sai dai idan Babansa ba yana nan amma cikin kankanin lokaci jibi yadda yake shi da ita kamar da can ya rayu da ita.

Hajiya ta ce Dr. Bahijja ina mamakin SABO DA JUNA da kuka yi da Muhammad cikin kankanin lokaci shi da baya yarda da kowa sai mahaifinsa.”

Murmushi tayi ta ce Allah sarki Hajiya ai haduwar jinine ni ma haka nake jinsa a cikin rai na kamar dama can muna tare.”

Hajiya ta ce, “mun gode fa Dakta.” Babu komai Haiiya ai yanayin aikinmu ne haka dole sai mun saba da patient dinmu. Daidai lokacin da Farouk ya karaso falon dauke da tarin recipt na magunguna yana zuwa ya mika mata ya koma gefe ya zauna. har yanzu Muhammad na jikin ta’ kamar wani kuliya domin haka Allah yayi shi da son jiki.

Sai da ta gama duba komai sanuan ta shiga tambayarsa irin matsalolin da yake tare da su tun daga ranar da abin ya faru,haka ya shiga yi mata bayanin komai tana sauraron sa nan ta ware wasu da yawa daga cikin maganin ta ce a dai na masa amfani da su ta kuma rubuta masa wasu da take son a nemo mata yanzu.

“Suna zaune ya buga waya akan a kawo masa duk maganin da ta rubuta masa.

Nan ta shiga yiwa Muhammad gwaje gwaje, tana lura da irin kallon da Farouk ke mata nan ta daure fuska kamar bata gani ba amma shi da yake ya gano manufarta sai abin ya shiga bashi murmushi.

Bata bar gidan ba sai da ta shafe sama da a wa shida a gidan domin da ta shirya tafiya Muhammad zai hau rigima wai dole sai ya bita haka dai aka yi ta fama da shi shi kansa Farouk yau bai leka nan da can ba yanayin dadin kasancewarsa da Bahiiia a gidan domin ko bai ce da ita komai ba kawai kallonta ma yana sa shi wani irin nishadi.

Tayi masa kokarin bashi maganin baci ya hanata ya ce bai son ta bashi da daddare ya hana shi barci,nan ta fuskanci shi ma kamar baya son tafiyarta nan ta ce masa shikenan.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE