MISBAH BOOK 3 CHAPTER 38 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Yana bada baya kuwa ta dauki magani ta durawa

Muhammad nan kuwa kan kace mai ya fara aiki a jinkinsa sai dawowa yayi ya ganshi kwance a jikinta ya shiga mamaki,tare da tambayarta ba dai maganin kika bashi ba domin nasan ba yanzu ne lokacin barcinsa ba baya barci at this time around.”

“Eh, magani na bashi domin na fuskanta idan na biye masa ba zan tafi ba.”

“Waya baki damar yin haka ko baki ji abin da na fada maki a bayaba zai hana ni barci da daddare.”ya fada cikin nuna isa da dakewa.

“Aiki na ne ya bani damar yin haka domin kai baka isaka hana ni yadda ba ko ka koya min abin da zan yi akan aiki na karka manta am professional Doctor babu wanda zai min shishshigi akan aiki па.”

“Look ko kina bakin aikinki baki isa kiyi min katsalandan a kan yadda nake tsara rayuwar gidana ba karki manta aikin dana kikeyi.”

Ka fara mantawa da alkawarin da muka yi da kai a rubuce ina son ka je ka sake duba takardar da take gurinka hakan zai fi maka saukin fahimtar abin da zan sake fada maka.

Nan tayi kokarin raba Muhammad a jikinta ta kwantar da shi kan kujera ta ce Ni zan wuce ka fadawa wanda suka dakkoni suzo su mayar dani amma kafin nan ina son yin sallama da Hajiaya.”

• Tana magana tana wani in magania shi kam duk wannan abin da yayi mata yayi su ne cikin nishadi domin ko kadan ba inda yaji ransa ya baci shi dai kawai yana neman magana ne yadda za suna canjin yawu, amma ita har ta hasala kamar dama kadan take jira. Ga hanya nan ki wuce ai ke ba bakuwace a gidan ba kibi nan zaki same ta cikin har side dinta.bata saurare shi ba tabi hanyar da ya nuna mata ko magana bata yi baya bita da kallo yana murmushi abinsa.

Tare suka fito da Hajiya bakin motar nan ta iske shi dauke da Muhammad a kafadarsa wani irin kallon yayi mata mai dauke da murmushi a gaban Hajiya ya ce, “Hajiya likitar Muhammad din nan na fuskance ta mai saurin daukar zafi ce.”

Hajiya ta ce to idan ta dauki zafin ai akan aikinta take hala wani iyayi ka kawo mata akan aikinta  ita kuma ta ga bai yi mata ba don ta dauki zafi ai tayi min daidai, Bahijja sai kina hakuri da abin da zaki gani a tare da shi haka yake indai akan Muhammad ne.”

Murmushi tayi ta ce Babu komai hajiya mum saba gain iyaye. irinsu aiki da jama’ a dole sai ka saba da halin kowa bare mu masu hulda da su haka kake  jure kamai.”

Nan ta shiga mota suka ja suka tafi suka shiga daga mata hannu har sai da ta fice.

A hankali Bahijja: ta fara jin dadin duba

Muhammad domin tana ganin yadda abin nata yake gudana yadda take so haka a nan kauye an ware musu gida mai kyau jikin gidan mai gari dakuna biyu ne duk na laka sai katon takar gida,nan Bahijja ta samu damar yadda za ta na duba duk wani mara lafiya a garin da kanta ta shiga cikin garin Gorabe ta siyo allurai da magunguna tana duba su kyauta har karbar haihuwa tana yi.

Cikin kan kanin lokaci ta saba da Muhammad da su Hajiya sai dai shi Farouk din ne ko kadan bata barin yana shiga harkarta domin ta fuskance shi yana son shige mata amma bata bashi fuska haka zai ta shiga noke nokensa.

Kullum Muhammad yana son kiran Bahijja da mama amma sai ta hanashi ta ce yana kiranta da Doctor sosai Therapy din nasu akwai ci gaba sosai sai dai Hajiya kallum tana ganin yadda Bahijja take yiwa Muhammad na rashin son ya kirata mama kullum idan tayi niyar mata magana sai kuma ta faso ganin yadda take bashi kulawa amma ita kawai son tani mai yasa bata son yana kiranta da mama.

Haka shima. Farouk ya fuskanci haka shi dai kasa hakura yayi saida ya yi mata magana. hango su yayi a farajiyar gidan suna ta wasa yana gudu tana binsa Sai dariya yake mata ya je nan bayan sun gama wasan suka zo suka zauna a kan wata resting chair.

Muhammad ne ya fara hango Abban sa tsaye yana nufo gurinsu nan ya ce,

‘mama Abba.”Do sauri ta jayo hijabinta sannan ta janyo Muhammad tace, “Muhammad ka kasa sabawa da abin da na ke fada maka, ni ba mamanka bace ni likitarka ce just kana kira na Doctor ba mama ba.” Turo baki yayi gaba ya tsaya yana kallonta alamun yayi fushi sauri yayi ya karaso gurin ya ce,

“Doctor ina son jin hujjarki ta hana shi ya kira ki

mamansa. Ga huija a bayyane ni ba mamansa ba ne

Therapy na akan aiki na nake yi don haka inada tarin hujja masu yawa akan yin haka.

Na shigo rayuwar Muhammad don na taimaka masa ya samu sauki ne bana shigo ne don ya shaku dani yana kira na da mama ba,bana son wani sabon

Dangantaka da kowa a

rayuwata, lafiyar

Muhammad ake nema ba komai ba kuma na shigo rayuwarsa ne da zanar ya samu lafiya zan tattara na tafi na farshi amma idan na bari ya saba kira na da mama ya shaku dani yadda zai dinga jina tamkar mahaifiyarsa wanda shakuwarsa da Mahaifiyarsa da ya rabu da ita ta kwakwalwarsa bai manta ba a

sanadiyar haka ya samu masala ina ga yau

Muhammad yaji sauki na tafi na bar shi zai iya komawa cikin ciwansa to mai aka yi Ke nan.

Ina son Muhammad sosai cikin rai na ina jin kamar nice na haifeshi amma idan na. tuno cewa aikin da nake yi akansa Contract ne a duk ranar da yaji sauki zan rabu da shina koma inda na fito wannan yasa nake son takaita shakuwar mu da son saba masa da cewa ni likitarsa ce ba mamansa idan ya gama fahimtar haka ya kuma saba da jim haka a tare da ni zai yarda zai bar ni na tafi idan lokacin tafiyar tawa ya zo.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE