MISBAH BOOK 3 CHAPTER 5
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 5
Shi kuwa Deeni ya tsaya yana kallon su, domin
sun zama abin kallo ya lura Bahijja ta iya biye ma
yara da son hakarsu da biye masu duk tsananin
fada da kishin da take yi da Farida bai sa ta nuna
shi a zahiri ba, mace ce mai iya boye kishinta
musamman a gaban mutane, amma shi ya san
tashin hankalin da yake gaban shi, an yi maganar
Farida ma ya aka kare balle gidan, to wai shin me www.dailynovels.com.ng
ya kawo ta garin Lagos kodai sabon salon son daga
masa hankali da wargatsa masa hankali ne?
Tabbas shi kadai ya san tashin hankalin da za
su shiga shi da Misbah, tana ta iya daga masa kafa
a kan komai amma banda magana a kan Farida,
tana da matukar rauni a wurin. Yana cikin wannan
tunanim sai ga Farida ta katse shi ta ce,
“Sannun ku
da dawowa uncle Deeni,
tana dariya ta ce,
“tun
dazu jira muke amma shiru.”
Bahijja ta ce, “ke ma kamar yaran uncle Deeni,
koda yake haka din yake.
Nan ta yi murmushi ta
ce, ya hanya? da fatan kun iso lafiya, amma
ma’aikatan gidan sun muku kyakkyawar tarba
kamar yadda muka kware wajen tarbar manyan baki na gida.
Ai kuwa Faridan ta amsa “Duk da mu ma din nan
kamar gida yake wurin mu.”
Misbah ta yi murmushi ta ce,
“Yeah, kamar
gida, Hausar ma akwai bambanci, sai dai duk da
haka mu ba mu wasa da baki a gidan nan, mu
karasa ciki in ga irin tarbar da akai maku, ta isa ko
ta yi kadan.
Duk yadda Farida ta so yin maganar
Deeni sai Misbah ta ta ari bakinsa ta amsa.
“Ikon
Allah,
ya ce,
“wannan miskilar in abubuwanta
suka motsa sai Allah.” Tare suka kutsa cikin falon
suka tarar Baba Audi da Baba zulai masu aikin
gida, suka ga an kammala komai, kayan abinci da
na sha kala-kala suka gabatar masu, Misbah ta kalli
Baba Audi ta ce, www.dailynovels.com.ng
“sannun ku, da fatan kun ba su
masauki mai kyau ko?”
Baba Audi ta ce,
“eh, na
kai su can sashen baki na gida amma ta ce,
“dakinki za ta sauka, to, abinki da ‘yan gida ba baki
ba, ban yi mata musu ba.
“A’a, Baba Audi kin kyauta da ba ki yi mata
musu ba, amma mu gidan nan Alhamdu lillah,
Allah ya mana wadata, ba takura kowa ya zo ya
sauka zai sake ya ji dadi,” «ina zuwa, zan je na
shirya wa Deeni bayi yanzu ya yi wanka.
Nan ta
yi ciki, har ya juya zai bi ta sai Farida ta kira shi.
“‘Uncle Deeni ya ko gaisuwa mai kyau ba mu yi
ba balle na fada maka me ya kowa mu
Gaba daya ya rude ya rasa me yake ciki, Bahijja
tana jin su amma ta daure ta yi ciki ta kyale su.
Ya ce,
“ya su mama?”
“Da ma Jamb na zo rubutawa
Ya ce,
“Jamb tun daga Kaduna har Lagos, kin
yanke hukunchin komawa karatun ke nan, amma
tabbas kin yi ma kan ki gata.
Ta ce,
“Eh, dalilin da ya sa na yi register a nan
saboda ya zo da hutun yara kuma suna son zuwa
Lagos hutu, ka ga ni ma in na yi jarrabawa sai na
huta, na samu canjin yanayi, can gidan su mama
kuwa ba kowa, ba za mu ji dadin zama ba shi ya sa
muka taho nan ko ba komai za ka debe wa yara
kewar babansu.
*My dear, bathroom is ready,
Misbah ta iSO
falon tana fadi, ka san yau gajiyar da muka kwasa
daban ce, kana bukatar wanka da kwanciya da
wuri, don samun hutu, nan ta ja hannunsa suka
fice.
Farida ranta ya mummunan baci, ta ji tamkar ta www.dailynovels.com.ng
rufe Bahijja da mari, wai ita waye da ta isa ta shiga
tsakaninta da Deeni, wai ta san ya suke da Deeni
kuwa, tsintacciyar mage mara asali za ta nemi nuna
mata gadara.
“Baki isa ba Bahijja sai na kwato matsayina da
kika kwace a gurin iyayen Deeni, ‘yan’uwansa da
kuma zuri’ar Deeni, dukkansu nawa ne ba naki ba,
za ki koma inda kika fito, na yi maki wannan
alkawarin.”
Nan da nan ta nufi kujera ta harde kafa daya kan
daya, zuciyarta na huci tana tafasa, yara ko suna ta
tsalle-tsallensu, in sun gaji su kalli cartoon, Baba
Audi nata hidima da su, duk abin da suka nema ta
kawo masu, da ma ita gwana ce wurin harkar yara,
Bahijja ce ta leko ta kwala wa Zulai Kira, ta taho
kayan su Farida, ta ce ta dauka su nufi
bangaren baki, wanda kwata-kwata ba hade yake
da bangarensu ba ma. Zulai na rike da kayan
Farida, Bahijja kuwa da na su Deeni karami ta ce,
“Yara ku zo mu je inda za ku kalli cartoon, yadda
kuke so, don a nan in uncle Deeni ya fito, kashewa
zai yi, ya kunna labaru, can kuwa inda kuke so nan
za ku kalla, kun san akwai chocolate, ice-cream
kala-kala da biscuit a wurin specially for you yara
irinku irinku in sun z0.
Yee! Suka tashi suna
tsalle. Suka bi ta, ta kalli Farida ta yi mumushi ta
ce.
” Aunty Farida ko, za mu je ki ga masaukinku, in
ya so sai ki dawo, in Kina da bukatar hira a nan,
murmushin dole ta yi ta mike.
Ta bi ta bangaren da ta kai su, wuri ne mai
kyau, ba abin da babu a ciki na jin dadin rayuwa, www.dailynovels.com.ng
masaukin baki ne na musamman, saboda ba Farida
ba ma Bahijja a tsarinta bata yarda, wani ko wata
su yi masauki a bangarenta da Deeni ba, saboda
tana ga wannan sirrinsu ne, wurin da suke gudanar
da rayuwa daga ita sai shi, wannan tsarinsu ne,
tunda Allah ya azurta su da in da za su ajiye wasu.
Kuma duk abin da suke bukata akwai shi wurin,
gida daya ne amma sai an fita daga wannan
bangaren sannan a je wancan.
Lokacin da suka isa Bahijja ta kai wa Farida
kayanta daya dakin, yayin da na su Deeni karami,
daya dakin wanda suna ko kallon juna kowane daki
da bayinsa ciki, sai falo mai matsakaicin girma,
hatta kicin akwai a wurin. Bahijja ta kalli Farida ta
ce,
“‘ina ga kamar za ki fi sakewa ku huta da kyau a
nan, saboda sirri yana da dadi privacy musamman
macen da ta yi zama a gidan aure, gidan kanta,
wani kaddaran ya raba ta da auren, to ina ga zama
tare da wasu ko dakin wasu in ba ya zama dole ba,
zai zame mata matsi da takura, amma kin ga a nan
za ki sake tamkar yadda kike da bangarenki a
Kaduna.” www.dailynovels.com.ng
“Haka yara ma zabin ki ne ki kasance da su ko
ki bar su a nasu dakin duk abin da kuke so kuke
bukata za ku same shi. in hira ce ma kuna iya zuwa
ciki in muna nan ayi hira in an watse kowa ya
koma masaukinsa, na ji kin zo rubuta Jamb ko?
Allah bada sa’a, na ga dare ya yi, ina ga da ma
kuna bukatar hutun kamar yadda muke bukata, don
haka sai da safe.
Faridan ta yi murmushin yake wanda ya fi kuka
ciwo, tace na gode da addu’arki da karramawarki
gaskiya ne zan fi son zama a nawa dakin da
bangaren fiye da naki.”
nan suka kalli juna ido
cikin ido, alamar dukkansu sun fahimci sakon da
suke ba wa juna a fakaice. Farida ta fahimci
Bahijja na son nesanta ta da mijinta ko ta halin
kaka, yayin da Bahijja ta fahimci tana son shigowa
cikin gidanta da rayuwar mijinta kota halin kaka.
wanda lokaci ne zai muna, mai nasara cikinsu, Nan
suka yi wa juna sai da safe, Bahijja ta juya ta fita,
Farida ta bi ta da kallo ta ce,
“kwarai bangarena da
dakina nake nema da kuma masoyina da kika
kwace min matsayin mijina.
Bahijja ta samu Deeni a bayi kwance cikin
Jacuzzi idonsa rufe duk da yana jin dadim ruwan
yadda yake ratsa shi, yana gasa shi da tausar jikinsa www.dailynovels.com.ng
amma wanna bai ba shi kwanciyar hankali da natsuwar da yake bukata ba, abubuwa da yawa ke
yaw cikin kwakwalwarsa.
Shin taya zai soma bullo wa wannan sabuwar
fitinar da tashin hankalin da suka kunno cikin
gidansa da rayuwarsa, ya san halin Bahijja zai
share a komai a gunta amma banda wannan, dan
zai iya kiran wanna karon shi ne tashin hankali da
sabani mai tsanani tsakaninsu tun aurensu, kansa
ya dau zafi sosai, ya ji motsin shigowar Bahijja
tana daure da towel ta tufke gashin kanta, ya zura
mata ido yana kallonta cike da so da sha’ awa, tana
tafiya tana yauki takun isa da jin a daidai take,
jikinta sai kadawa yake kamar reshe, tana juya
manyan idanunta dake kunshe da abubuwa kala-
kala sai da ta iso daf da shi ya dage idonsa da kansa
daga gareta.
Zama tayi gefensa yayinda ta sa hannayenta
cikin ruwan tare da shafar bayansa da masa matsa
da tattausan yatsunta bata ce mai kala ba, sai
lumshe ido ya yi yana jin dadin hakan da wani irin
sukuni a zuciyarsa da jikinsa gaba daya, hakika ya
yarda Bahijja ita ce farin cikinsa da kwanciyar
hankalinsa da duk wani sukuni nashi, Bahijja
natsuwa ce sosai a tare da shi. Can ya ji ta shigo
cikin ruwan ita ma ta kwanta a jikinshi suna gogar
juna ta kwantar da kanta bisa kirjinsa, ta ji sonsa na
ratsa zuciyarta, da ruhinta yayin da take jin bazata
taba iya rayuwa da wani namiji ba sai shi, haka nan
tsananin kishin Farida ta ji yana cin ta a ranta cikin
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE
www.dailynovels.com.ng