MISBAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
MISBAH BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
tsakaninsa da Misbah ba ko da kuwa Farida ne,
Misbah sirrinsa ce, haka kuma shi sirrinta ne* ba mutum na uku da zai taba shigowa tsakaninsu ya san wannan sirrin.
Wucewa ya yi kai tsaye dakin ya murda kofar yaji ta a garkame, tabbas ya san akwai tsiya
tsakaninsa da Bahijja. Kyaleta ya yi ya ba ta lokaci
zuwa wayewar gari, idan ta huce zai mata bayani
su fahimci juna, wannan ne dare na farko da suka
taba raba wurin kwana, a wannan daren dukkansu
sun kwana da zugin zuciya. Deeni
ya dinga
mamaki da tunanin irin yadda Farida ta sáuya
wadda sam da ba hakan take ba, tana son kutsowa;
cikin rayuwarsa,
ta wargaza masa
gida• da kwanciyar hankalin da ya samu, ta fi kowa sanin
cewa shi mata biyu ba ra’ ayinsa ba ne, mace dayan
nan ta ishe shi rayuwar aure, Bahijja kuwa it ce
abokiyar rayuwar da Allah ya zaba masa wadda
rayuwarsu da tunaninsu suka zo daya, Allah ya
masa sauyi na alkhairi.
“Haka nan yadda Bahijja
ta rike nida
muhimmanci da amana, ta sadaukar da rayuwarta,a
kaina, ta rike ni ta kula dani, ta fahimce ni, ta
fahimci yanayin rayuwata da tunannina, ta bani
goyon baya, ta ba ni nitsuwa da kwanciyar hankali
har na samu abin da nake so a rayuwa, na sha shiga
hakkinta da lokacinta saboda burina da ayyukana* a
rayuwa, akwai kyakkyawar fahimta da sadaukarwa
a tsakaninmu, ina alfahari da mace irinta kuma zan
kare mata hakkinta da mutuncinta da farin cikinta,
na fahimci kishinta ga Farida shi ya sa ma banga
laifinta ba, saboda wannan ne karo na farko da
muka samu mummunan rashin fahimta, amma
insha Allah komai zai daidaita kamar kullum
please Bahijja yanzu ma ki fahimce ni
Da irin wannan tunane-tunanen ya kwana har
asuba, ya nufi masallaci, ya dawo amma har yanzu
ba ta bude kofar ba, ya buga ya yi magana shiru har
ya ji ransa ya fara baci, wannan zuciyar ya ji tana
taso masa amma ya yi kokarin danne taya nufi
dakinsa ya dauki ¡pad dinsa yana latse-latse, amma
abin ya gagara, bacin ransa sai karuwa yake,
zuciyarsa nata saka masa tsiya da arziki duka.
A bangaren Bahijja kuwa har yanzun tana cikin
zafi, ba ta so su yi ido biyu da Deeni, su yi sa in-sa
da, zai sa su tunzura juna har ya jawo wani
mummunan fada tsakanin su, zbacin ran miji ga matarsa ba karamin
masifa ne a gareta ba, da haka ta gwammace su bawa juna lokaci.
Farida kuwa ba sallama ba shiri ta tattara
yaranta ta tafi, sai da ta zo shiga jirgi tayi wa
Deeni text cewa ta tafi a yanzu, amma domin tadawo gaba daya, ya fada wa Bahijja kar tayi dogon
farin ciki, tana nan dawowa gaba daya, idan na dawo gidanka a matsayin matarka Deeni, zan cire
maka aljannun Bahijja da suka mantar da kai
shaukinmu da soyayyarmu, zan tado maka da
tsohuwar soyayya da tsohon alkawarin da ke
tsakaninmu zai cika
Tsaki yayi ya kashe wayar, yayi wurgi da
wayar, ya tashi ya yi wanka, duk da Lahadi ne bai
zuwa gidan gonarsa, sai bayan azahar ko da
yamma, yakan zauna da Misbah su tattauna
matsalolinsu, su kasance tare da juna a wannan
ranaku na Asabar da Lahadi, sai dai fa in lokacin
Fitarsa gidan, dan haka a tsarinsa Asabar da Lahadi
Yana fita ne tsakanin azahar zuwa la’ asar, amma a
wannan haka ya fita da safe ba shiri, dan a can ne
Yake ga zai iya samun sukuni da natsuwa. Jin
fitarsa ya sa Bahijja ta tashi ta yi wanka ta sa wani
abu a cikinta, ta shirya ta duba agogo karfe goma
na safè ta fito ta yi tunanin za ta samu su Farida sai
ta tarar ba sa nan, Baba Andi ke Fada mata sun tafi
tun karfe bakwai na safe, ta yi shiru na dan gajeren
lokaci, sannan ta ce,
“Baba Audi zan wuce asibiti,
ni ma zan leka ban jin dadin jikina, in na fita ina ga
zan dan warware, sai ku shirya abincin rana kafin
in dawo, sai mu yi na maigidan tare.” “To Hajiya,
ta amsa ta yi ciki. Har ta fita sai ta dawo ta leka
bangarensa, daki da falon ta tattara ta gyara tar da
wanke masa bayi, duk da ba wani datti amma
ka^ida ne kullum sai ta wanke, ta jima tana tsaye
tana kallon dakin, irin rayuwar da suke gudanarwa
ciki mai dadi da marar dadi, ba su taba raba kwana
ba, wannan ne karo na farko, haka ta ji abin yana
matukar mata ciwo, zuciyarta na mata zali, tayi
saurin fita ta rufe wurin ta nufi asibiti, ta bi tana
leka marasa lafiya sama-sama ita ma dai Lahadin
bata fita sai da yamma bayan litar Deeni, in ba dai
emergency ba ne.
Su kansu ma’aikatan sunyi mamakin ganinta a
lokacin da ba su saba ganin ta ba, saboda sun san rayuwar
Dr. Bahijja akwai ka ida,
duk iya
kokarinta ta samun sukuni ta kasa, dan haka ta bar
cikin asibitin ta nufi gidanta dake wurin ta bude ta
shiga ta nufi Study room dinta kai tsaye tare da
dauko wasu littatafai da take ganin in ta karanta za
ta samu sauki do ‘Not be Sad shine littafin da
kullum take karantawa inta tsinci kanta a cikin
wanna yanayi wanda wani shahararren malamin
Addini dake Saudi Arabia ya rubuta shi, inda ya ba
da misaliai da hadisai da ayoyi tare da rayuwar
magabata annabawa da sahabbai
Tabbas wannan littafi ba karamin kore mata
kewa da damuwa yake ba, ta nutsu sosai cikin
karatun, duk da ta gama littafin, amma kullum in
tana karanta shi sabo yake zama mata, tayi nisa
sosai, tana ji yana ratsa ta ba ta ankara ba sai ji ta yi
an waino kujeran da take zaune, an juyo da ita,
Deeni gaban ta, ya sa kafa ya take kujeran ya
sunkuya gabanta ya ce,
“Ganin matar nawa ko sai
na yanki ticket ne an ba ni lasisin ganinta? Nan tayi kokarin danne zuciyarta ta yi murmushin dake
kara wa fuskarta kyau tace,
“wa ya isa ya yanka
wa miji ticket din ganin matarsa? ai wannan
mallakina ne Allah ya ba shi, halak malak, sai
yadda ya yi da ita.
Ya zuba mata ido “ban ga alamar haka daga
tawa matar ba
“Anya kuwa Deeni ka sake ware idanu ka duba
da kyau, matarka ba ta taba sanya hijabi a
tsakaninku, bata ta ba ba wa wani abu muhimmanci fiye da mijinta ba, in ba bautar Ubangijinta ba.Shi ya sa jiya kika rufe min kofa? Ko mai hakan
yake nufi?”
Ta kau da kai tare da fadin “Rufe kofar yafi
bude ta alkhairi saboda idan na bude ina cikin zafin
zuciya da bacin rai komai na iya fadi wanda hakan
zai iya jawo min fushin Mahaliccina.”
“Kina tsammanin matakin da kika dauka na rufe
wa mijinki kofa Allah ba zai yi fushi da ke ba?”
Ta mike tana kallon shi yana kallon ta, ta ce,
“na ji, nayi laifi, ina neman ka yafe min laifin da
na yi maka.” Tana fadi ta wuce ta fara tafiya, ya kira sunan ta
“Bahijja. Ta tsaya, can ya sha gabanta
tare da harde hannun, zuciyarsa na masa zafi ya ce,
“‘wai me kike ji da shine? me kika dauki kanki? na lura da wasu halayye da kika fitar da su wanda ba haka na sanki da su ba,
” ta ba shi amsa da cewa,
“kamar yadda ka dinga fitar min da wasu halayya
da ban san ka da su ba, ko ni ba mutum ba ce? ko
ni ba ni da zuciya ba ni da feelings din da zan ji
zafi? Kina nufin yayan Yaya Shamsu ko Farida basu isa su zo gidana ba, ban isa in yi magana da Farida ba saboda ke ba kya so? to, ni ba na daya
daga cikin mazajen da matayensu ke juyawa,
komai kuwa son da nake maki ba za ki sa in
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE