MISBAH BOOK 4 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Binta yayi da kallo yana nazarin kalamanta

cikin ransa yana cewa Bahijja baki da

wannan right din na fita daga cikin

rayuwarmu ni da Muhammad, muna mutukar

bukatarki cikin rayuwar® mu duk wuya duk runtsi

ba zamu taba barinki kiyi nisa da rayuwarmu ba

kin shigota Kenan ba zaki taba fita daga cikin ta ba

HAR ABADA.

Kullum kwanan duniya cikin dake jikin Bahijja

kara bayyana yake yi tun tana boyewa har ya fara

bayana kansa kowa ya kalle ta yanzu zai ga mai

ciki. tun lokacin da Farouk ya fuskanci ciki ne da

ita hankalinsa ya tashi domin yana son sanin ita

matar aure ce Kenan wanda da a tunaninsa

bazawara ce amma ganin cikin dake jikinta yasa

gaba daya burinsa da tunaninsa sun rushe.

Gashi yana son yayi mata tambaya amma ya tuna

cewa cikin sharadinda ta kawo bata son tambaya

akan komai da ya shafi rayuwarta, cikin ransa yace

lallai Bahijja mace mai hikima tasan wannan rana

zata zo yasa ta gindaya masa ita cikin sharadin

yarjejeniyarsu.

Tabbas bashi da bakin Magana akan hakan

domin hakikanin gaskiya yana ganin mutukar

cigaba akan lafiyar da Muhammad yake samu zai

cigaba da juriya. akan duk wani abu da zai gani a

tare da ita, domin yasan duk abinda zata yi da biyu

take masa zai jure ya shanye komai a ransa har

zuwa lokacin da zai kai yasan komai na rayuwarta. Bashi da inda zai je yaji komai nata Mai gari ne kawai zai iya fada musu komai na game da labarinta domin dai koma daga ina take itan ba a kauye ta rayu ba akwai wani boyayyan al’ amari a tare da ita, kuma ba shi da ikon zuwa wajan mai gari don tambayarsa wani abu a tare da ita domin a gabansa aka yi wannan alkawarin kuma a yadda yake ganin Bahijja mutukar ya karya alkawarin da yayi mata tana iya ajie Therapy din da take ma yaronsa tayi gaba domin ya fuskance ta akwai wani abu da yake damunta akasan zuciyarta da ba kowa bane ya sani sai ita da zuciyarta da suke rayuwa tare tsawan lokaci zaune a gurin yana zancen yaci daga nan ya mike ya shiga ciki.

A hankali Bahija ta gama gano wane Farouk mutum ne mai kirki da son taimakawa jama’a marasa shi, domin kullum gidan cike yake da mutane masu son ganinsa, kullum da safe kafin ya fita office sai ya ga mutane ya taimaka musu haka idan ya dawo sai ya sake ganin wasu mabukata wannan haka yake cikin tsarinsa.

Yawan kirkinsa da ganin yadda yake hidimtawa jama’a abin ya daure mata kai har take tunanin dama shi ba mugu bane kamar yadda take masa kallon haka tun farko to mai yasa su yake son raba jama’ar kauyen nan da garinsu, kuma meye tunaninsa na yin haka. Tun daga nan ta fara raga masa sai dai kuma bata barin wata mu’ amala da ban ta shiga tsakaninsu. haka ta dinga jin ta fara rage jin zafinsa da take akan baya can da ta dauke shi mugu mai son yin amfani da power ya cuci talakawa.

Don haka tuni ta barshi cikin wasu

sahun maza masu wani irin tunani daban.

Rayuwar Bahija da Baba Audi a kauyen tayi musu dadi haka Baba Audi ta samu dattijai irinta suna zama suna hirarsu gwanin dadi, ita ma Bahijja ta samu abinda take so kullum idan ta zo gurin Muhammad haka zata dawo ta samu gidanta cike da marasa lafiya nan ta dinga jin farin cikinta na shigarta har ta fara jin damuwarta tana raguwa dama ita burinta ta dinga kasancewa tare da marasa lafiya hakan yana making dinta company.

A hankali son Bahija mai tsanani ya kama

Farouk sai dai bashi da wata hanya da ya isa ya tunkareta da maganar son nata mata, bata taba bashi fuska ko wata daman suyi Magana matukar ba abin da ya shafi kan lalurar Muhammad ba shima baya wuce a yi kaza kada a yi kaza idan ka ga ta sake tayi hira da wani cikin gidan to Hajiya ce.

.Ita-kanta Hajiyar ta fuskanci halin da danta yake ciki akan Bahijja ta kuma gane akwai abinda yake saka shi shakka akan ya furta mata nan ta saka shi gaba lokaci yayi akan ya fito da matar da zai aura zamansa haka ya fara damunta tayi haka ne don ta ji mai zai ce mata game da tsakaninsu da Bahijja.

Nan ya nuna mata fa shi har yanzu a cikin ransa bai ji ya fara jin yana son kara aure ba ta bashi lokaci kamar yadda ta bashi a baya idan lokacin yayi da kansa zai fada mata ya ga wacce yake so amma ba

yanzu ba.

Ba haka ta so ji daga gare shi ba amma dole ta rabu dashi domin ta san ba ko wane namiji ne ke iya sake aure da wuri ba idan matarsa ta rasu bare kuma shi yadda suka shaku suka kaunaci juna da wani irin tsananin SABO DA JUNA da suka yi lokaci guda mutuwa ta zo ta raba su lokacin da suke tsaka da bukatar juna.

Hajiya ce ta fito ta iske su zaune a falo ita da Muhammad nan tayi musu sallama ta fadada murmushin ta bayan Bahilia ta amsa ta samu guri ta zauna, tace “Bahijja ina son mu yi Magana da ke.”

“To Hajiya ke nake sauraro.”

Nan Hajiya ta gyara zama tace Bahiiia wani abu ne nake gami a tare da ke na jima ina son yin magana amma Allah bai nufe ni da yin haka baba tun yau baga dai tsakanin ki da dan gidan ki Muhammad amma sai naga har yanzu kina nuna rashin son ya kira ki da Mamansa na jima ina jin rashin dadin hakan da kike masa, amma idan na duba yadda kaunarku da shakuwarku yake sai na ji ban damu ba domin kowa ya ganki yasan kina son Muhammad.

Sai dai kuma tun da muke da ke baki taba tunanin ki ji labarin mahaifiyar Muhammad duk kuwa da yadda yake a gare ki, Bahijja ina da wani buri akan ki amma na rasa ta yadda zan yi na fara tunkararki da maganar, sai dai yau na yanke shawarar zuwar miki da ita yau amma kafin nan ina son na sanar da ke ko wane Umar Farouk da matarsa Maryam kafin

na kai ga gaya miki burina a akanki.

Umar Farouk shine dana na biyu bayan yayarsa da take aure a can masar mahaifinsu ya rasu shekaru bakwai da suka wuce su biyu ne yarana shi da yayarsa mai suna Zainab da Allah ya bani su a duniya.

Umar Farouk ya taso mutum mai tausayi da son taimakawa masu karamin garfi kamar yadda ya ga mahaifin su yake shi ma yasa haka a ransa zai yi.

A gida Nigeria ya gama karatunsa na primary da nagaba da primary daga nan ya tafi England anan yayi Degree na daya dana biyu duk akan fannin kasuwanci.

Tun kafin ya tafi karatu kauna da shakuwa da kanwarsa Maryam ya shiga tsakaninsu wanda ya rikide ya koma soyayya. Maryam yar kanwata ce uwarmu daya uban mu daya haka mahaifinta kuma suke ciki da ya da mahaifin Farouk, tunda na dakkota yaye bata koma gidansu ba a gurina ta girma har na aurar da ita.

Farouk da Maryam sun so junansu kamar me babu wanda bai san irin tsananin kaunar da suke yiwa junansu ba kuma kowa babu wanda bai so

ganin kasancewar auransu ba.

Lokacin da farouk ya gama karatunsa ya dawo ita kuma tana shekararta ta uku a jami’ a, nan iyayen su suka dage akan a yi auran ko bata gamaba ashe

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE