MISBAH BOOK 4 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

nake mata zan iya jurewa zan hakura na cigaba da kare mata mutuncin, na tausaya mata sosai Baba Audi ban san haka tayi irin wannan ravuwar mai tsanani da tarin bakin ciki wanda idan aka duba bacin rai da bakin cikin data dandana yafi farin cikinta yawa a cikin duniyar nan.

Baba Audi nay miki alkawarin sanya Bahiija farin ciki har kanshen rayuwarta duk wani abu da nasan zai saka Bahijja farin ciki zan yi shi komai wuya komai rintsi don kawai ta yarda akwai so na gaskiya a cikin duniyar nan zan yi iya kokarina naga ko ban Jawo mata da farin cikinta duka ba zan kokarin dawo mata da rabi ko fiye da rabin zan yi iya kokari na naga na kori wannan tarin kuncin da na tsani ganinsa akan fuskarta amma fa Baba Audi kema sai kin taimaka min.”Zan taimaka maka Umaru zan yi iya bakin kokari na insha Allahu kuma sai Allah ya mallaka maka Bahija matsayin uwar yayanka domin Bahijja macece da kowane da namiji zai yi alfahari da samun nagartacceyar mace kamarta don haka insha

Allahu daga yau duk sallar da zan yi sai na saka wannan niyar taka a ciki Allah ya dafa mana baki daya’.

Cikin jin dadi yayi murmushi yace “Allahumma

Ameen Baba na gode sosai.”

A lokacin da ya samu Hajiyarsa da zan can tayi mutakar tausayawa Bahijja har sai data zubar mata da hawaye ta kuma yi alkawarin ba zata taba nuna mata sunsan wani abu a cikin rayuwarta ba.

haka taji tana kara jin kaunarta aranta ta shiga yi ma danta fatan Allah ya mallaka masa ita a mazaunin matarsa uwar yayansa domin yanzu babu abinda Hajiya take son gani kamar ace yau danta ya yi aure domin tun mutuwar matarsa bai kara marmarin kara wani auran ba amma tunda Bahijia ta shigo rayuwarsa ta ga hankalinsa gaba daya ya karkarata da son aure don haka zasu bi Babijja yadda take so har lokacin da zata amince.

Hankalin Bahijja yanzu ya fara dowawo jikinta domin domin a yanzu tayi iya yita na ganin ta fitar da Tunanin Deeni ta tsaya ta samawa kanta sauki da kuma gina sabuwar rayuwa da sabbin mutanen da take rayuwa da su tana kuma samun farin ciki yadda take son samu domin a yanzu tuni

Muhammad ya ji sauki sosai domin har ya shiga makaranta yayin da a yanzu Aisha ta shiga shekarunta na uku.

Tunda take bata taba ganin mutum mai naci ba kamar Farouk duk abinda da zata yi masa akan

Aisha baya iya yin fishi ya kan yi ganinta ta hana shi ganinta ita dai kawai bata son wani sabo da.

A lokacin Muhammad ya ji sauki Bahijja tayi kokarin tattara komai nata don ta dawo gida ta kuma gama aikinta. Ba Farouk kadai ba hatta Hajiya sai da hankalinta ya tashi domin bata son rabuwa da Bahijja nan ta shiga rokon ta data daure kada ta tafi tana zuwar musu kamar yadda ta saba karfi da yaji ta basu hakuri akan ba zata iya ba

alkawari suka yi kuma ya cika. kwana biyu da faruwar haka Muhammad ya shiga tashin hankali.

Nan da nan ya birkice musu domin wuni yayi kuka har sai da wani irin zazzafan zazzafi ya kama shi babu shiri Bahijja ta dawo domin yadda take jin Muhammad a ranta zata iya yin komai don ta ga yayi farin ciki.

Domin ta samu abinda zai kara sata yana debe mata kewa a cikin garin kauyen wanda kuma zai sa

Farouk ya barta ta huta tunda offer din da ya bata aikin yakare yasa ta bude makaranta tana koyar da manya da kuma yara karatu da rubutu domin kawai ta kawo cigaba a cikin kauyen wanda tayi hakan ne domin Farouk ya ga aiki yayi mata yawa ya saukaka mata ya kuma sabarma da Muhammad rashinta a cikin rayuwarta.

Haka ta raba lokacinta wajan uku da safe ta yiwa yara maza da yanmata da yamma kuma iyayansu ga kuma duba marasa lafiya da take yi a cikin karamin clinic a cikin gidanta hakan da take yi ta dinga jin dadi da nishadi yana shigar ta ji tana rasa dukkan damuwarta.

•Kamar yadda tayiwa su mai gari alkawarin zata kawo musu cigaba sosai a rayuwarsu don haka suma suke bata dukkan wani taimako da take so.

Matsala ta farko da ta fara fuskanta a cikin kauyen tun zuwan ta bata da wani da yake bata matsala komai tana yi ana kuma bata gudumawa ta zamana komai za’a yi cikin kauyen sai an nemi shawarta nan take wani a garin shi kadai SC yake

da karatu cikin garin da ya jima da fita neman ilimi

don ya zo ya taimaki kauyensa.

Amma sai ya ga Bahijia ta kawo wannan cigaban wanda hakan yayi mutukar kona masa rai amma ya ajje komai a ransa ya kara fita neman wani illimin wanda yasa a ransa sai ya rusa dukkan wani kokarinta da kuma bata dangantakar da kaunar da mutanen kauyen ya ajje hakan a ransa sai dai bai gayanawa kowa ba amma yana mutukar yin kishi da ita ganin yadda ta samu daukaka a kauyen fiye da shi domin ya zamansa ma babu wanda yake bi ta kansa.

Don haka ya shiga addu’ar neman samun wata hanya da zai bata Bahijja ya kuma samu shima damar da ta samu koma fiye da wadda ta samu haka ya ajje wannan tunani nashi babu wanda ya sani dama haka rayuwa take kana yin rayuwarka baka damu da wani bashi kuwa yana can gefe yana ci maka dunduniya Allah kayi mana tsari da makiyi

a ko ina yake a rayuwar nan ta mu,

Tunda gari yawaye Aisha take mata rigima wai ita gurin Abbanta ranta yayi mutukar baci da fitinar kukanta haka ta sa mata ido tana kallonta karfi dai da yaji yarinyar tana son nuna cewa tafi son Farouk da ita domin idan zata yi kwana uku bata ganta ba idan tana tare da shi ba zata taba yin kuka akai ta wurin taba shakuwar su da SOBO DA

JUNA da suka yi Wannan take gudu yasa take hana shi daukarta da take yi ta shayi mai kashe din idan ya dauketa ya dawo da ita a ranar amma sai yaki idan ya tafi da ita sai tayi kwana uku hudu ba tare da ta damu da rashinta sai daí idan yayi niya ya dawo da ita zuwansa na karshe da ya dauketa sati guda tayi a can ranar da ya dawo da ita ya ga mutukar bacin ranta domin masifa ta shiga yi masa da yake yasan shine mai laifi hakuri kawai ya bata ya kama hanya ya tafi a lokacin ma sai da Aisha tayi rigimar binsa amma ta hanata. Sai da yazo ganin ta sau uku tana hana shi ganinta har yayi fishi bai kara zuwa ba amma abinka da abin da kake so da kauna ga kuma yadda yake jin son Aisha a ransa kamar shine mahaifinta yasa dai ya jure yana zuwa baya ganinta sai ya koma.

Rashin ganinsa kwana biyu yasa ta shiga rigima wai ita Abba zata je hakan ya bata haushi tayi rarrashin tayi ban bakin amma ina Aisha tace bata san zance ba hakan ya bata haushi ta zuba mata. ido tana kallonta.

Baba Audi ne tazo ta iske ta tana ta faman kuka da yake ta dan fita cikin gari gurin aminanta da tayi cikin kauyen, nan tayi sallama ta tambayi mai Aisha take so ne take rigima haka ita kuma ta kasa rarrashinta ta saka mata ido tana kallonta. daga nan ta fara tarrashin ta ta dakko sweet ta bata tace yi shira Aisha na rabu da Mama sha alawanki, nan tayi shiru ta karba ta samu jikin Baba Audi ta kwanta abinta.

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE