MISBAH BOOK 4 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Haka ta dinga jin rashin nutsuwa na kara shigarta ta ji ranta yayi mummunan baci kan abinda ta fada masa. a cikin wannan halin Aisha ta zo ta sameta rike da rigata daya a hannunta tana ganin babu motar Abbanta nan fa ta shiga kuka sosai.

Nan taji tausayin Aisha ya kamata ta ja hannunta tana rarrashinta suka koma ciki tana ta kukanta.

Ganin kamar damuwa zata yi mata yawa yasa tayi saurin watsi da tunaninsa don a yanzu taiwa kanta alkawarin ba zata kara barin wani abu ya tashi hankalinta mutukar tana raye.

Washegari sai gashi ya dawo tayi murna lokacin

Aisha nabarci bare har ta daga mata hankali qarfi da yaji har cikin ranta bata taba tunanin zai dawo a cikin kawanakinnan duba da yadda ya barta cikin fishi shin anya kuwa mutumin nan yana da zuciya a kirjinsa duk irin abinda da zata yi masa baya fishi kuma ko yayi zai huce.Sallama tayi masa ya amsa amma taki shiga motar ta tsaya a waje tana jiran taji da mai yazo kuma wanna karan. suna gaisawa ta wani hada rai.

Shima bai saki tasa fuskar ba kawai ya mika mata key.

Ta wani kalleshi tace wannan kuma na menene?”

Cikin dakewa yace “Key din gida ne na kama muka haya ina son daga yau zuwa gobe nake son ku koma can da zama don haka ki yiwa Baba Audi Magana kuzo mu je gidan ku ga tsarinsa ko yayi muku domin an saka komai da komai a ciki.”

Sake kallon shi tayi cike da mamaki tace

“Farouk wai wannan iko da gadarar da kake nunawa akai na. Meye haka ni yarka ce ko me ka dauke ni? Menene na nuna damuwarka akan rayuwar da muke a kauyen nan an fada maka gurin zama na rasa ko ina neman taimako ne a gurin wani.”

Duk yadda kika fada haka ne ni dai nagama magana, ki yiwa Baba Audi ki zo mu tafi idan kina da abin cewa idan mun je can ki yi, a bakin aiki nake na fito don haka bana son mu bata wa junan mu lokaci mu yi abinda zamu yi kawai mu wuce wajan.

Don haka kudi na saka na biya gida komai da komai babu mutumin da zai sa nayi asara.”

“Dole kuwa kayi a sara domin kuwa ba kowa ya saka kaba kai kasa kanka.”

“Asara bata ta so ba dole ne ki yi abinda yake so, a wannan karan Bahijja bazan zuba miki ido ba kina ta yin abinda kike so ban taba sa muku baki ba maza karbi mukullin gidan ki saka masa albarka.” cewar Baba Audi. ta juyo ta kalleta ta bata iya cewa da ita komai ba, nan Baba Audi ta cigaba da

cewa. Haba Bahijia wai me yasa kike haka ne,

ya same ni yayi min bayanin komai dazu kafin ya ganki na kuma yarda don haka ya zama dole mu tattara mu koma can duba da UZURIn da ya bani akai.”

Bata yi Magana ba tayi shiru domin ba zata taba musu da Baba Audi ba yadda take kallon ta tamkar mahaifiyarta.Baba Audi ina son idan da hali kuzo muje ku ga gidan idan yayi muku to idan bai muku ba sai ya canza min wani wanda kuke so. Cikin damuwa tace “Baba Audi ni dai ba inda zani, ina zan iya zuwa nayi rayuwa bayan nan ina son kauyen nan ina son kawo musu cigaba sai yanzu da na fara kokari na za’a ce na bar garin, Baba Audi na rokeki ki bashi wata dama amma banda wannan, na yardazan yi amma fita ta cikin kauyen nan ba zai taba yuwa ba.

Bahijja nayi miki alkawarin taimaka miki ki bawa wannnan kauye naku dukkan gudummawa ta ko wane irin cigaba kike so yayi wannan alkawari na dauka.”

Zata yi magana Baba Audi tayi saurin cewa

“karka damu Umaru zamu je yanzu mu gani bari na dakko Aisha tana barci sai mu wuce mu gani.” bata jira mai Bahijja zata fadaba ta juya tayi ciki abin ta. har taje ta dawo Bahijia bata ce da shi kalaba ya sani haushin abin da yayi mata take ji, gudun kada ya takalo wani rigimar yasa yayi gum da bakinsa amma cikin zuciyarsa dadi ya kama shi yasan yayi nasara akanta. Lokacin da suka fito tuni Aisha ta farka daga barci zuwansu ne ya kawar da dongo shirun da suka yi. Aisha na ganinsa ta shiga murna da doki nan yayi saurin daukarta ya dawo da ita gabansa. tabbas Farouk yagama mata illa ta ko ina yadda yake mutukar kaunar Aisha. Farouk mai kirki ne kuma har cikin zuciyarsa yake son Aisha ta fuskanta duk abin da zata yi masa ba zai taba nuna fishi ba.

Nan suka kama hanya tunda suke tafiya babu wanda suke Magana daga Farouk sai Aishansa ban da kayan shirmenta babu abinda take yi. ya sata a gaban mota takarkare wai ita ne ke tuki komai tayi biye mata yake yi. Ko wannan kadai ya kamata zuciyarta ya sakko akan matakin da take dauka akansa domin dai duk wani gata da kulawa na uba Aisha na samu a gurinsa nan ta kara jin sam bata kyauta masa da tayi niyar yi masa wani abu da zai saya ji dadi ko farin ciki da ta tuna abinda Deeni yayi mata sai ta ji sam ba zata iya ba.Sun shigo cikin gari sai dai ba hanyar unguwarsa ya nufa da itaba nan ma wata unguwace mai kyan tsari.

Wani gida ne karami madaidaici mai kyan tsari yana da gate nan suka yi parking. gaba daya suka fito suka shiga ciki shi ya karbi key din. nan suka shiga ko ina na gidan yayi mutaka kyau da tsari dakuna uku ne da falo, ga kuma karamin parking space, komai da komai an saka daki daya da yafi komai kawatuwa da alama na Aisha ne domin Toys ne sosai an tsara su ga kuma kara min gadonta komai na ciki kalar pink.

Sauran dakin daga gani kasan na Bahijja da Baba Audi ne yadda aka tsara daki matar gida dana dattijuwa. murna ta kama Baba Audi nan ta shiga yi masa godiya da sanya masa albarka.

Bahijja kuwa kasa magana tayi domin tsabar mamaki gidan yayi mutukar burgeta komai ya tsaru mu samman kitchen din yayi mata sai dai tarin dukiyar da aka kashe shi ya daga mata hankali iya falon gidan zaka san gaskiya ba karamin dukiya aka kashema wajan.ba Nan Aisha ta fara guje gujenta. Bahijja ta numfasa tace “Farouk yayi kyau da tsari sosai da sosai sai dai maganar gaskiya yayi yawa a yadda nake son rayuwata na karasa ta wannan gidan yayi min yawa da girma tun farko na fada maka bana bukatar taimako a gurin kowa don haka da taimakon nayi ba zaka bani wannan gida mai tsada haka ba.” har Baba Audi tayi niyar maganar yayi saurin dakatar da ita yace.

“Baba Audi na jima da sanin halin Bahijja bata bukatar taimakon wani ko wata haka yasa nayi amfani da damar Bahijja kin san dai ni dan kasuwa ne na kuma san hanyoyin samun kudi ko kina tunani zan iya baki gidan nan kyauta ne sam kudi na saka na kama miki hayazan baki dama har zuwa ranar da zaki iya bani kudina.Sannan zaki bani duk takardunki zan nema maki aiki a MINISTRY OF HEALTH idan ta fara

Hmmm

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE