MISBAH BOOK 4 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

“Gaskiya ne Muhammad, Babban Yaya bana son wannan zafin yana yawa, wai baka san bana son ana takurawa Mamana ba.”

” ya fada yana dariya.

“Anyi an gama Abba ba za’a sake ba.”

Aisha ne ta iske Farida a falo tana ta faman kallonta a tashar Zeetv tana kallon series. tayi mata sallama tace “Momy zamu fita da Abba sai mun dawo mai zan taho miki da shi.”

Tabe baki tayi tace “na hutar da ke sai kun dawo bana bukatar komai.”To Momy sai mun dawo.”

“Ba zaki tsaya yanzu za’a fara film din naki fa

Tash -ne-ishq.

“Idan na dawo kya bani labari ko na kalli na dare.” tana gama fadi tayi saurin ficewa.

Ta bita da kallo tana murmushi ta cigaba da kallon ta sam yanzu Farida ta dauke hankalinta akan Deeni ta saki ranta tana rayuwarta kamar ba ita babu abinda ya dameta da shi ga yara sun girma sun zama samari har sun shiga jami a.

can baya Deeni haka kullum ya shiga tunanin mai zufi akan Misbah dare da rana kullum damuwarsa rashin haihuwa da ita da bai yi ba da ko bata cikin rayuwarsa yasan zai samu saukin ganin abinda ta haifar masa kullum da wannan tunanin bakin cikin yake kwana yake tashi. Rana tsaka yana zaune sai tunanin Muhammad danta ya fado masa yana kwance sai kawai ya mike _ zaune nan ya fara tunanin ta ina zai bi ya gano danta Muhammad ya dai san tace a kano yake. nan ya fara tunanin ta inda zai fara bi dan ya gano yadda zai je family house din su Marigayi Mislihu. bai yi kasa a gwiwa ba ya bazama neman manyan abokan marigayi Mislihu har Allah ya sa ya dace ya samu wani abokin Doctor Mislihu wanda suka yi aiki da shi tare da yake shima likita ne Deenin bai sha wata wahala ba gurn gano Dr. Bala har gida Deeni yaje ya same shi ya karbe shi hannu bibbiyu.

Nan yace yana so ya bashi full address din gidansu yana son yaje ya ga family dinsa da yaronsa da ya bari domin tsohon likitansa ne ya taimaka masa sosai a rayuwarsa.

Ran Dr. Bala yayi dadi tare da yi masa godiya sosai bai bata lokaci baya bashi cikakken kwatancen gidansu Gadon Kaya. haka suka rabu cikin jin dadi bayan sun gama hirar marigayi har bakin kofar gida ya raka shi ya shiga mota ya tafi.

Washegari kuwa ya bi jirgin safe sai garin kano (ta Dabo cigari yaro ko dame kazo an fika). bai sha wuya baya samu gidan.

Lokacin da ya zo gidan an karbe shi sosai hannu bibbiyu jin cewa daga Lagos yake ya yi musu gaisuwar rashinsa nan yace yana son ganin mahaifiyar DR. Misliu haka kuwa aka kirata da sauran yaranta nan suka gaisa cikin sakin fuska da walwala.

Daga nan ne ya kara musu dadin haske yake shi daga bangaran Bahijja yake ya zo kuma yana son ganin Muhammad ne dan da aka rabata da shi tun yana shan nono.”

Nan da nan ran Hajiya Babba yabaci kamar yadda ya ji suna kiranta. ranta a bace tace “Wace Bahijja a ina take da dangin da har za su iya biyo bayan abinda ta san tuni ya haramta a gareta.

Yarinya yar tsintuwa wadda bata da asali kasan kuwa da ya aka yi na yardaa kayi wannan auren don kawai anfi garfi nane amma ban taba jin ina son Bahijja ba dai dai da rana daya har Allah yaraba ta da dana wanda nayi godiya da basu tara iyalai da shi sosai ba.

Kaddarar Allah da rabon yaron nan yasa aka yi auran har yanzu idan na tuna da wacce dana ya haihu da ita sai nayi takaici.”

“Ya isheki haka! Wannan cin fuskar da batancin bazan jure jin su ba, Ya isa bana son ki kara fada min komai akan Bahija.”

Ba Hajia Babba hatta sauran yaranta da suke gurin sai da suka dan razana da Deeni ganin yadda ídanunsa suka kada suka yi jajur kamar gauta tsabar fishi da jin zafin cin mutuncin da akaiwa

Bahijja a gabansa.

Kowa ya saurara yana kallonsa cikin tsoro a fuskar matan wani daga cikin mazan yace “kai Malam kasan ina zaka je ka yi wannan tsawar amma ba a nan ba kai din wanene.”

Ka fara dakatar da wannan tsohuwar da take cin mutuncin Bahijja a gabana kafin ka dakatar dani, ni din da kake tambaya nine Mijin Bahijja a yanzu kuma na zo ganin Muhammad tunda mun yi iya kara amma babu abinda aka yi mana.”

Hajiya Babba tace “Sannu miji manya ita ta turo ka Kenan ka yi mana rashin kunya, lallai idan ka yi ba laifi ba ne tunda bata da asali zata iya komai tunda bata taso da tarbiyya ba.”

Cikin yaranta wani namiji matashi yace “Haba

Umma wai duk mai yayi zafi haka daga anzo muku gaisuwa sai abu kuma ya zama fiTina sam haka bai kyautu ba.”

„Zaka rufe min baki ko kuwa sai na bugeka

Sulaiman.” ta fada cikin bacin rai shiru yayi abinsa ya tsaya yana kallonsu.

Hajiya baki fahimci wacece Bahijja ba shi yasa kike fadin haka darajar shekarun kina duba shi yasa zan tsaya ina jin wanna batacin amma ba dan haka babu wani mahaluki da zai bata min mata na tsaya ina kallonsa ba tare da na dauki

kwakwkwaran mataki ba don haka mubar Maganar haka yanzu ina son ganin Muhammad kawai tunda muna da ikon ganinsa ko a addinance ne.

Wani irin kallo tayi masa kai tsaye tace “mun mayar da shi can dangin uwarsa duba da su suka fi dacewa da rikonsa ba mu ba.”

Cikin rashin fahimta yace “Hajiya ban gane mai kike fadaba ina ne dangin uwarta sa.”

Murmushin takaici tayi tace “Au ita bata fada maka daga ina take ba har ka aureta, ba kasan danginta ba to bari na fada maka bata da wani dangi da ya wuce gidan marayu a can dana ya ganta ya auro don haka idan kana son ganin dan nata ka iya zuwa can ka ganshi.”Wani irin kallo yayi mata mai cike da tuhuma yace “Hajiya me kike cewa? me kike tunanin kin yi, wannan wane irin son kai ne da rashin tunani, anya kuwa kin yiwa dan ki Misluhu adalci abar batun Bahijja da shi kansa Muhammad.

Yau idan aka ce Mislihu zai dawo duniya yaji abinda mahaifiyarsa tayiwa gudan jininsa bayan ta tabbatar cewa dansa ta hanyar sunna aka haife shi amma saboda kin mahaifiyar yaron tayi masa haka, tabbas zai ji takaici zai yi bakin cikin jin uwar da ta haife shi ne tayi masa haka.

Hajiya ke wace irin uwace wannan mai ya rufe miki idon ki kika ki rungumar jikanki jininki, ina tausayinki na uwa, ina kaunar dake tsakanin kaka da jikanta, meyasa da kinsan ba zaki iya rike yaron nan ba kika rabo shi da mahaifiyarsa tun yana shan 

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE