MISBAH BOOK 4 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE
da rabon mahaifinsa zai ga auran, shekara daya da auran Allah ya karbi ran mahaifinsa.
Don haka komai ya dawo kansa dukkan kula da harkokin mahaifinsa na nan garin dana sauran gurare kasancewar mahaifinsa fitaccene a garin dama kasar baki daya.
Tun daga nan ya koma
Abuja tunda can yawancin yawan kasuwanci suna can. Shekarunsu hudu da aure Kenan bayan bayan lokacin an haifi Muhammad yana da shekaru biyu akan hanyarsu ta zuwa Gombe daga Abuja a nan ne suka yi hatsari ko cikin garin Abuja basu fita Allah ya kawo hatsarin daga Farouk har Muhammad babu wanda bai ji ciwo ba amma ita Maryam a take rai yayi halinsa.
Bahijja tsayawa baki labarin irin tashin hankalin da muka shiga a wannan ranar ba zai yuwu ba ko mutuwar mahaifinsa bata girgiza shi ba kamar mutuwar Maryam. babu wanda bai zaton Farouk bai zautu ba kowa yaga halin da ya shiga a wannan lokacin sai ya tausaya masa domin sai da muka yi da gaske da addu’o’i da saukar kur’ani sannan muka samu ya nutsu amma tun daga wannan lokacin ya rasa walwala da farin ciki a rayuwarsa.
Da farko da bamu lura da cewa Muhammad yana da lalura ba domin komai mun mayar da hankalinmu ga Farouk sai da muka ga samun nutsuwarsa sannan muka lura Muhammad na da lalura.
Hankalin mu gaba daya ya kara tashi nan fa aka bazama nemar masa magani kasashe da dama mun
kai shi amma dai haka muka yi muka gaji. tun daga wannan lokacin Farouk ya dauki son duniya da kauna na Maryam da wanda yakewa Muhammad duk ya dora masa baya komai sai kula da
Muhammad komai tare suke yi barci tare yawo tare don haka nan wata kauna da shakuwarsu ta kara karuwa.
Tun lokacin da ya tattara ya dawo Gombe bai kara tunanin komawa Abuja ba haka gaba daya ya dawo da harkokinsa gaba daya nan Gombe. bashi da wani buri a rayuwarsa illa ya ga Muhammad ya samu lafiya yadda zai iya yin komai da kasan ya kuma iya furta komai yayiwa kansa komai.
Babu irin tayin da ba a yiwa Farouk akan ya kara aure ba amma yaki akwai lokacin da na taba yi masa Magana akan ya je ya auri Sameera kanwar Maryam kuka ya saka min kamar karamin yaro har yace min shi kam zai iya kara aure ba HAR ABADA ya kuma gode Allah da yasa Maryam ta bar masa abinda zai gani yana tunawa da ita hakan ya isheshi farin ciki idan ana so a ga walwalarsa to kada a kara masa maganar yayi aure.
Babu yadda zan yi dole na rabu da shi tunda ina son ganin nutsuwarsa da kuma farin cikinsa.
Bahija tun bayan rasuwar Maryam ban ga wata mace da naga Farouk yana farin cikin mu’ amala da it ba irin ki don haka yasa neke neman alfarma gurinki ki taimaka min ki tai maki dana da jika ki zamo matarsa shi kuma Muhammad ki zamo mishi uwa yadda zai ji dadin kiranki mamarsa. Ki yi min alfarmar nan domin ko shi kansa
Farouk bai sannan zan yi miki maganar nan ba amma na sani tabbas zai yi farin ciki da wannan abinda na yi masa.
Jin wannan furucin nan da nan tashin hankali ya bayyana akan fuskarta yanayinta ya sauya. cikin kasa boye damuwarta tace “Hajiya hakuri da wannan abu da kika nema a wurinna wallahi ba zan iya ba, bani da burin kara ko wane irin aure a rayuwata.
Nan da na hawaye ya shiga sauka kan fuskarta tana share hawaye tana cewa Hajiya idan ba so kike na bar ku ba to don Allah kada ki kara yi min maganar aure na san so na kike shi yasa kike ma danki da jikanki sha’awar na zauna cikin rayuwarsu, bazan iya ba na roke ki da ki janye wannan maganar idan kika cigaba da yi min ita zaku iya nemana ku rasa kuma idan nayi haka ban cika alkawarin da na daukarwa Farouk ba kuma zan cuci Muhammad ina son ki bar ni yadda kika ganni har zuwa lokacin da zan gama abinda ya kawo ni na koma, amma Hajiya ina son ki gane cewa ba wai ina kin amincewa da abinda kika fada min ba, a’ah kawai auren ne bazan iya ba don Allah ki gafarce ni.”
Ganin hawaye a idanunta nan da nan hakalin
Hajiya ya tashi tace Bahijja ki yafe ni ban yi haka don na daga miki hankali ba nayi hakan ne don kaunar da naga kina nunawa jikana da kuma son na zauna dake na dindindin amma tunda ba kya so insha Allah bazan sake miki maganar ba ban san dalilinki ba ban san damuwar da ta saki kike kin son yi aure ba hasalima nice da laifi da ban tsaya naji damuwarki da ra’ayinki na fada miki abinda da yake rai na kai tsaye na zama mai son kai don Allah kivi hakuri.
“Ba son kai bane Haiya kauna ce ta kai ki ka furta min haka na fahimci nufin ki babu komai har cikin zuciyata nice ma nake ganin ban kyauta miki ba duba da abinda kika umarce ni nayi miki.”
Karki damu Bahiija ni ma guri na ban damu ba tunda kika fada min haka kina da dalilinki na kin yin aure, kuma kina da wani sirri da kike boyewa, na barki da sirrinki domin ban san yi miki dole akan komai na rayuwarki domin lokaci guda na ganki kuma dukkan dan adam yana da sirrinsa da ba kowa ne zai iya fadawa ba, kuma da farko ya kamata na tambaye ki kina da aure ko baki da shi idona ya rufe duba da ga ciki a jikinki ya kamata na fara tunanin a wane matsayi kike mai aure ceke ko Bazawara amma tunda ba ki taba bani wani labari daga gareki ba na barki da sirrin ki ba zan kuma yi miki wata Magana da zata daga miki hankali ba insha Allahu.”
Nagode Hajiya da wanna fahimtar da kika yi min nagode sosai.”
“Nima nagode Bahijja Allah ya bar zumuncin da ke tsakaninmu
“Ameen.” Tsananin rudani da fargaba ne duk suka bi suka tsaya a cikin kwakwalwar Farouk domin yana labe a kofar da za’a shigo falon ya zo da niyar shiga falon nan ya ji dai dai inda Hajiya take fada mata tana son hada auransu da shi da dai nan ya fara sauraron hirar tasu. hankalinsa ya tashi domin ji furucin da Bahijia ta fada na idan aka takura mata da maganar aure za a iya nemanta a rasa.
Shi kuwa da Bahijja tayi nisa da rauwarsu shida
Muhammad gwara su rayu a haka ya boye son da yake mata koda zai mutu da shi maganar gaskiya
Hajiyarsa ta fada tun bayan mutuwar Maryam babu wata mace da ya taba mu’amala da ita kamar
Bahijja kuma baitaba jin son kowa a zuciyarsa ba kamarta.
A yadda yake jin son Bahijja da a kodayaushe yake karuwa cikinsa tabbasa tayi nisa cikin rayuwarsu zai iya rasa dukkan farin cikinsa don haka zai iya yinsa ya boye son da yake mata don su zauna lafiya zai cigaba da rayuwa a haka har ranar da Allah zai saya iya tukarar ta da wannan babbar bukatar tasa dole yana son jin labarin Bahija domin ya tsinci wani abu a tare da ita yadda zai san ta ina zai faro to amma a yanzu babu wata hanya duba da yarjejenivar da sukayi da ita zai kara hakuri har zuwa lokacin da Muhammad zai ji sauki sosai don haka yanzu zai san yadda zai ta qarfi da yaji ya san yadda zai yi ya kara dasa shakuwa a tsakaninsu zai yi biris da ita ya nuna mata sam bata
Hmmm