MISBAH BOOK 4 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Rufe bakin ta ke da wuya sai ga shina tare da Hajiya dauke da tarin ledoji a hannunsu. Wanda hakan ya hana Bahijja bawa Baba Audi masar abinda ta fada mata.

Bakinsa bude yana murmushi yace “Samunku da hutawa ya Baby?”

Wani irin kallo tayi masa nan da nan suka hada ido da ita batace da shi komai ba ta amsa sannun da Hajiya tayi mata. Baba Audi tace Alhaji ga Babyn taka yanzu ta motsa tana jin shigowarka.” ta karasa fadi tana dariya nan ta mika mishi ita.

Cikin sauri ya karbeta ya sake sumbatarta sennan ya rungumeta. ga mamakin Bahijja sai ta ga kamar Deeni ne yake gabanta ya dauki diyarsa, tabbas da bai rusa musu farin cikinsu da tasan yau itace ranar da zai fi komai farin ciki a ravuwarsa a ganin Misbah dinsa ta Haifa masa baby girl abinda yake fata da burin samu daga gare ta amma yau rashin cika alkawarin da ya dauka ya nisanta shi ga ganin wannan farin cikin.

Muryar Baba Audi ne yayi saurin dawo da ita daga tunanin ta ta tafi.

“Bahijia baki ji mai Hajiya tace da ke bane.” nan da nan ta lattara tunaninta tace “Na’am ban jiba wallahi.”

Cewa tayi ga kayan jarirai nan sun kawo mata.”

“To Allah ya saka da alheri.” nan ta mayar da kallonta ga Farouk tace Farouk nagode sosai da jin abinda kayi min Baba Audi ta fada min Allah ya biya ka kai da Hajiya nagode sosai, sai dai ya kamata ka bar komai haka ya isa.”

Ran Baba Audi yayi dadi jin kalamai masu dadi da suka fito daga bakin Bahija tabbas da bata taka mata burki ba babu abinda da zai sa ta kasa fada masa abin da ta kudirci fada masa.

Doctor bana bukatar godiya daga gare ki duk wani abu da zan yi miki kin cancanta nayi miki ne nakan yiwa wasu ma bare ke.”

“Juyowa yayi ya kalli Baba Audi yace “Baba ina ganin a can gida zamu wuce da ku kuzauna madadin ace a wuce kauye dan kula da ita kwana biyu a nan ko ya kika gani.”

Hajiya tace “Ai dama a nan zasu zauna tayi jegonta mu kula da ita sosai.”

Cikin sauri tun kafin Baba Audi tayi Magana Bahiija tace “A’ah a yau zan wuce inda muke babu wani guri da zani can ma zasu kula dani mun gode da kulawar da kuka ba mu.”

Baba Audi ta bita da kallo tace Bahiiia babu inda zamu sai kin zauna a nan bayan kwana biyu sai mu koma nagama Magana bana kuma son naji kin kara komai akai.”

Wani irin takaici ya kamata to amma babu yadda zata yi ta musa Baba Audi domin tafi karfin komai a tare da ita babu wata alfarma da zata nema bata yi mata ba. nan ta ji dole tace wani abu domin har yanzu an hanata fadin wani abu.

Tace “Baba Audi yanzu idan muka yi haka an kyauta Mai gari da iyalansa babu wanda yasan mai ake ciki kawai sai muzo nan mu zauna, Haba Baba Audi ki duba ki gani.”

Karaf Farouk ya tsomo baki yace “Idan da wannan ne kadai zai saki damuwa to ni da kai na yauzu zanje na dakko shina kawo su su zo su dubs ki.”

Sallamar da aka yi aka turo kofa nan suka juya don suga mai sallamar driver ne da hadiman gidar kana kuma Muhammad. Bahijja tana gainsa ta saki murmushi. nan ta mika masa hannu yaso yaki yayi mata nuni da jinin da ya gani jinta.

Dariya aka yi masa da dabara ya zo gurin daga baya ne aka nuna masa kanwarsa nan ya shiga murna aka mika masa ya fara ja mata hanci nan suka dinga dariya.

Hajiya bata bata lokaci ba ta janyo manyan Food flask ta fara hadama Bahijja farfesun zabbi da tace a hada akawo mata asibiti nan ta nan ta bata ta kuma zubawa Baba Audi.

Gabaki daya suka hadu suka taho gida bayan an sallame mu bargare guda aka ware musu ita da Baba Audi kowa da dakinsa. kamar yadda yayi alkawari da kansa yaje kauyen ya dakko mai gari da matansa biyu Yafendo da abokiyar zamanta da wasu dattawa biyu.

Bahijia taji dadin ganinsu nan ta shiga murna da zasu koma Farouk yayi musu sha tara ta arziki bayan hidimar da aka yi musu ta cimaka da aka tarbe su da ita. da kansa ya mayar da su. Zaune take gefen gado ta kurawa ma yarinyar

¡danu tsanamin kama da mahaifinta dada bayyana yake a tare da ita yau kwananta biyu Kenan a duniya. Baba Audi tayi sallama dakin nan ta iske Bahijja tana kallon diyarta. murmushi ta zo gurin tace “Maïjego sannu da hutawa.”

Ta cira kai ta dubeta tayi murmushi yawwa

“Baba Audi kin gani ina kallon yarmyar nan kamanninta da mahaifinta kara bayyana yake yi, na yanke shawarar zan cika ma Deeni wani alkawari da muka yi a bayana da ya taba fada min idan na Haifarmasa diya mace yana son saka sunan Mahaifiyarsa nayi masa wannan alkawari don haka na saka sunan yarinya Aisha, nayi hakan ne ba don farin cikin Deeni ba don kawai alkawarin da na daukar masa a baya shi kuma alkawari ko da wa kayi shi komai dadewasa idan ka cika shi lokacin ka yi Free, Baba Audi ya na kara cika ma Deeni alkawari na karshe tsakaninmu da shi bashi da wani bashin alkawari a kai na.”

Murmushi Baba Audi tayi ta dauki Aisha ta rugume tana mata addu’ a Allah ya fata halin mai sunan ta na alhihi. sannan ta kara da cewa “Bahijia sau da yawa kina kara birgeni yadda kike mutunta alkawari komai girmansa da kankantarsa da za’a samu AL’UMMA suna koyi da haka da an zauna a duniya lafiya da samun fari ciki. sun jima suna hirarsu a nan Hajiya ta shigo ta same su.

Farouk ya yi mutukar kokari ko shine mahaifin

Aisha iya kokarin da zai yi Kenan kayan barka da ya tarama Aisha akwati yakai uku ko kadan baibi ta kan Bahijja ba duk da mita da ta dinga yi masa akan bata son wannan abinda yake mata. cikin

Gadara da iko yace babu ruwanta tsakaninsa da yarsa ne idan ita bata son ya mata komai bata isa ta hana shi yayiwa Aisha abuba.

Ganin yawan shishigin da yake mata nan ta tada borin barin gidan babu yadda Baba Audi bata yi da ita ba amma ta kafe kai da kafa dole sai sun koma kauye.

Kwanansu takawas gidan Farouk suka tattara suka dawo kauyen sai dai bai wani nuna damuwa domin dai yasan kullum zata zo gidansa kuma zai ganta ya fuskanci wannan zafin da take dauka tana da wani dalili amma yasan duk abinda yake mataba wani wanda zai sata bacin rai ba ne, ganin

Hajiyarsa ta nuna rashin jin dadin abinda tayi nan ya shiga bata hakuri yana cewa ayi mata UZURI tana da dalilin yin duk abinda aka ga tayi da haka

Hajiya zuciyarta ta sanyi.

Yau kwanan su biyu da dawo kauye sai yanzu

Bahija ta fara jin dadin rayuwa da walwala yadda mutane suke kai komo wurin ta tana kuma duba marasa lafiya. Aisha kuwa gaba daya tana gurin Baba Audi babu abin da yake hadata da ita sai zata bata Nono.

Karfi da yaji idan zata tafi duba Muhammad sai tana barin Aisha a gida da kuma madarar shanu. tun Hajiya nayi mata mita har ta gaji ta dai na ita kadai ta san dalilin haka. Yau ma kamar kullum shine yaje dakkota dalilin masu zuwa daukanta basa nan sai daya aje su cikin gida ita da Muhammad sannan ya juya ya tafi aikinsa. zuciyarsa cike da tunanin wannan kuncin da yake yawn ganinsa a fuskarta wanda abin ya gama damunsa yake son ya kore shi gaba daya ko shima zai ji dadin tashi rayuwarsa.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE