MISBAH BOOK 4 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Farouk ne zaune a dakinsa ya rasa yadda zaiyi da tunaninsa domin ya gaji da wannan halin na Bahijja taki ta sake da shi taki ta bari ya san ainihin labarin ta iya dai juriya yanzu yayi don haka a yanzu a shire yake ya fara gwada kwanjinsa akan nuna mata abin da yake nufi akanta domin dai a yanzu Aisha ta fara wayo sosai yana kuma da damar bayyana kansa a gareta domin ya fito cikin zawarawanta.

Domin yanzu ya gama gano shakuwarta da

Muhammad ba zata taba yin nisa da rayuwarsa ba yadda take jin tana son shi ga kuma yadda Allah yake kara taimakawa ya fara dawowa dai dai kamar kowane yaro domin yanzu babu abinda baya iya furtawa da kan sa da kuma yin abin ba tare da an koya masa yadda zai yi ba.

– Abu daya ne ya ajje a cikin zuciyarsa zai bi wasu hanyoyi don gano meye musabbabin matsalarta don haka karfi da ya ji ya tsiri karance karance

English Novel don ya gano wani abu cikin rayuwarta.

Ranar farko da ta shigo falon ta hange shi rike da lave story book a hannunsa kallo daya tayi ma abin da yake hannunsa ta yi watsi da shi ko gaisawa bata bari sun yi ba wani irin kunci ya dinga gani akan fuskarta.

Nan ta nufi kujerar da zata zauna nan ma ta ga wasu tarin Novels din nan ta kara jin wata damuwa tazo mata. bata san lokacin da tayi watsi dasu ba nan da da nan ta shiga masifa babu gaira babu dalili.

Bai yi mata Magana baya samu ya duka ya dauki kayansa ya koma ya zauna ba tare da ya sake ce mata komai ba.

Binta yayi da kallo ganin yadda duk tabi ta rude kan wanan furucin da ta fita hankalinta. lallai akwai matsala sosai a tare da ita tabbas cikin al’amarinta akwai inda so ya bakanta mata.

Tun daga wannan ranar idan yana son jan

Magana sai yazo inda take zaune da novel daga ranar kuwa ba zata kara kulashi ba. nan ya shiga hanyar da zai bi don jin labarinta,

Yau ma kamar kullam da jin zuwanta ya dauki motarsa ya saci jiki sai kauyensu don zuwa ganin

Aisha data dai na zuwa da ita gidansu kawai don kada wani sabo ya shiga tsakaninsu sai dai ta barta gurin Bába Audi da madararta ta sha yanzu watanninta hudu a duniya.

Baba Audi ne ta fito goye da Aisha a bayanta ta iske shi waje kan tabarma da yake yanzu zuwansa baya damun kowa don idan an gashi tare da Baba Audi an san Aisha yazo gani. Bayan sun gaisa ne yake cewa “Baba Audi nazo gurin kine kan wata bukata har yanzu dai ina nan kan baka nan a burin auran Bahijja amma har yanzu ta hanani damar da zan bi na bayyana mata kai na da abinda nake muradi akan ta.

Baba Audi na rasa yadda zan yina fitar da

Bahija a rai na da da yadda zan yi da tuni na hakurá amma abin ya ci tura, kowa ne hanya na bi sai ta san yadda tayi ta datse ta, shine nazo gurin ki

domin ki taimaka min nasan kin fini sanin halin

Bahijja nesa ba kusa ba ki duba tsawon lokacin da muka dauka da ita amma har yanzu ba ma iya doguwar. Magana ta minti biyu indai ba akan maganin Muhammad ba.

Gyara zama tayi sannan tayi gyaran murya tace

*Umaru idan da ina da yadda zan yin na sanyayar da zaciyar Bahijia ta manta damuarta da tuni ka sami abinda kake so a tare da ita amma ina mikin da aka yiwa Bahija cikin zuciyarta yasa ba zaka samu abinda kake so a tare da ita ba.

Umaru na yarda kana son Bahijja na kuma tabbata har cikin zuciyarka kake sonta da zuciya daya matsalar daya ne Bahijia tuni ta rufe kofar bawa duk wani da namiji zuciyarta duba da abinda ya faru da ita a baya hakan yasa ta tsani maza tsana mai matukar tsanani kai ma da ka samu tana kulaka dole ne yasa a yadda ta tsara rayuwarta babu ita babu wani da namiji.

A yarda na karance ta ta tsani Kalmar so ta tsani dukkan wata DANGANTAKA tsakanin mace da namii idan yawuce na uba da da ko yaya da kanwarsa. Tsanar da tayi wa so yasa ta tsanar kowane namiji da ya furta mata cewa yana sonta a yanda ta fada babu son gaskiya a cikin duniyar nan so karya ne kauna karya ce wannan abu da ta ajje a zaciyarta da shi take kallon ko wane da namiji.

Umar yau zan baka labarin wacece Bahijja meye dalilinta na kin son ji Kalmar so me yasa kullum take ganin foskarta cikin kunci da damuwa zan

fada maka hakan ne badan na tona asirin Bahijia ba don kawai kokarin da kake akanmu da kuma irin tsananin kaunar da kulawar da kake bawa Aisha da mu kanmu, zan fada maka ne domin hankalinka ya kwanta kuma ka daina ganin Bahijja kamar bata da kirki ko ta cika son kanta.

Wani irin farin ciki yaji ya dirar masa a kirjinsa ya dinga jin kamar ya samu Bahijja ta amince da shi Baba Audi ta zayyane masa koma na game da rayuwar Bahijja tun daga zamanta a gidan murgayi Misluhu har kawo yadda suka gama rayuwarsu da

Deeni babu abinda ta boye masa har yadda aka yi suka zo cikin kauyen nan ta kwashe ta fada masa ta kare cikin kuka.

Jikinsa yayi sanyi ya ji wani irin tausayin Bahijja ya kamata yaji kamar ya je ya hada ta a jikinsa yana rarrashinta. hakika ya tausayawa Bahijja sosai da sosai tabbas ba a yi mata adalci ba, dangin Deeni sun yi mata butulci iya butulcisamman ma mahaifiyarsa. sai dai a wani fannin ya ga kuskuren Deeni sosai yadda har ya yiwa Bahijja haka haka ya kasa fahimtarta tabbas a yadda ya ji yadda suka gina kaunarsu a haka da wuya su iya rabuwa duk runtsi amma duba da yayi da kaddara sai a bar abin a nan.

Kukan da Baba Audi take ya daga masa hankali ya shiga bata hakuri akan ta dai na. cikin shashsheka tace barni na yi kuka yau na tuno abin da ya faru karfi da ya ji an canza min halin Bahijja ta komawa kamar ba ita ba mace mai

tausayi da juriya mace da kullum ka kalli fuskarta dauke take da murmushi da nishadi kullum ka ganta kamar bata da wata damuwa da damuwa ta zo mata zata yi yadda zata mayar da ita ba damuwa ba amma yanzu ba abu kadan zaka yi mataka harzuka ta komai mutum zai yi mata duk kirkinsa ba zata yaba ba musamman da namiji wadannan abubuwan idan na tuna suna bakanta min rai.”

Hakuri zaki Baba na ji tausayin Bahijja sosai kuma daga yau na dai na ganin dukkan laifin abinda take yi yi mata akai yasa take yi. sai dai a duniyar nan ban taba ganin mutane masu butulci ba irin dangin

Deeni amma suma duk da haka zan musu UZURI domin ajizanci irin na dan Adam.

Sai dai shima Deeni a zahirance bai kyauta ma

Bahija ba a matsayinsa na namiji bai kamata ya zartar da hukunci cikinfishi ba. sannan ita kanta mahaifiyar Deeni ba ta kyauta ba ki duba irin dawainiyar da tayi da dansu a lokacio da yagama

zautwa.

Baba Audi babu komai zan rike sirrin Bahijja zan boye bazan taba barin wani yaji ba bare a sake goranta mata sannan zan san yadda zan yi na fahimtar da Hajiya kadan daga cikin labarin Bahijja da irin batulcin da aka yi mata don ta kara samun nutsuwa da ita.

Zan jure ko shekaru nawa zan yi da Bahijia ina jiran ta har zuwa ranar da zata bani damar ta amince na aure ta domin na bata damar huce mikin da aka yi mata a cikin zuciyarta, duk da irin son da

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE