MISBAH CHAPTER 1 BOOK 2 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 1 BOOK 2 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Doctor Mislihu da Doctor Bahijja sun yi aure tsawon shekaru goma da suka wuce, Bahijja ta kasance marainiya wacce bata da kowa a duniya.
Dr. Mislihu ya hadu da Bahijja ne a gidan marayu da ke Kano, asalin su mutanen Kano ne. Mahaifinsa na da arzikin sa dai dai gwargwado, kamar yadda ya tashi ya ga mahaifinsa cikin taimakon al’umma, shima sai ya mike da haka, da wannan burin. Duk abinda zai yi ya samu lada yana zuba dukiyar sa a wurin, wato sadakatul jariya. Mahaifin Mislihu ya rasu yana da ajin farko na jami’a, lokacin da ya fara karatun likitancin sa. Mahaifiyar sa da sauran ‘yan uuwansa suka tsaya masa har sai da ya gama karatun sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
A lokacin da yake ajin Karshe a Mauduguri, lokacin Bahijja na da aji biyu wanda mahaifinsa ne dama ya dau nauyin karatun ta na (secondery), tana daya daga cikin marayun da ya tallafawa..
Lokacin rasuwar sa komai ya ja baya, komai ya shiga gado, bata da halin shiga (University). Sai dai Bahijja ba mace ce mai zama haka ba, don haka ta dage da sana’a, tun daga kan dinki da kuma yin kananun ayyuka da kasuwanci, ta samawa kanta hanyar shiga jami’a.
Haduwar ta da Mislihu ya cigaba da tallafa mata ta fuskar karatu da kuma kudi lokaci-lokaci, saboda sai ya zama dole Bahijja ke karbar kudi daga hannun wasu.
Mislihu ya jima da sanin Bahijja, lokacin da suke kai ziyara da mahaifinsa gidan marayu, tun yana (secondary) amma bai taba tunanin soyayya da ita ba balle aure sai da suka hadu a jami’a, inda anan halayyarta da dabi’arta mai kyau ya ja hanlkalinsa.
Mace ce mai kyan gaske, amma bata taba nuna wani alfahari da shi ba, balle jin kai. Asali ma bata taba bawa wannan muhimmanci ba. Sannan ra’ayinsu da tunanin su ya zo daya,
mace ce mai burin son ta ga ta taimakawa
al’umma, ta ba da gudunmawarta ga (society)al’umma. Sam abin duniya ko duniyar ba sa gabanta, mace ce mai zafin nema da kuma zafin zuciya, tana da kishin kanta da na al’umma, ba karamin abu ke iya rankwafar da ita ba. Bata da karaya bata (giving up), mace ce mai faduwa tana tashi da karfinta.
Hankalinta da tunaninta da ra’ayin su ya zo daya da Mislihu, har suka fara soyayya, soyayya ta sosai. Nan suka shirya yadda za suyi aure suyi rayuwar su tare da burin su da (Ambition) dinsu da yardar Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da Mislihu ya jewa ‘yan uwansa da maganar auren Bahijja fafur mahaifiyar sa taki amincewa, hankalinsa ya tashi saboda yana matukar son Bahijja, haka nan bai son aurenta ba tare da amincewar mahaifiyar su ba. Itama Bahijja ta ce masa yayi ta lallashin mahaifiyar sa har ta amince.
To da hakan da lallashi ya dinga binta, ya dinga bin kan ‘yan uwanta da nasa da yasan tana jin maganar su, suka bita da lallashi har ta amince, amma ba don tana so ba Mislihu da Bahijja suka yi aure.Lokacin da ta gama karatunta na likita ta soma aiki a Kano tare da mijinta a asibitin Aminu Kano Teaching Hospital, daga bisani Doctor Mislihu ya samu fita waje karo ilimi har ya samu (license) na zama cikakken (Physiotherapist).
Bayan ya dawo ya jima yana (trainning) a (Teaching Hospital) dake Lagos, daga bisani ya samu babban matsayi, (Psychiatric clinic) yayin da Bahjja ma ta bi sawunsa suka zama (Professionals) a abu guda.
Bayan ta gama nata karatun itama ta same shi a Lagos, inda suka hadu suna aiki tare. Kowa na jin dadin aikinsu da zama da su, saboda kwarewar su da kuma aiki tsakani da Allah.
A hankali suka samu bude nasu asibitin ya zama (Rehabilitation center) suna taimakawa mutane sosai, musamman matasa da kuma mata da yara, saboda ganin yadda matsalolin su ya cika al’umma a zamanin yanzu. Mutum baya iya daukan (Pressure) wata damuwa ko kaddara, sai su fada wani hali daban, daga karshe ya koma ga ɓata musu kwakwalwa wanda da yawa kunci ke jefa su a wannan hali.Abu na farko da Bahijja ta lura shi ne da rashin addini a cikin al’amarin, don haka ta bawa Mislihu shawara da su hada da addini da magunguna na Musulunci. Haka ya zama ka’ida, duk wanda zai zo asibitin su to yasan suna aiki da addini ne. Ba za su hana wanda ba Musulmi ba, amma yabi dokar su. Don haka suka dage suka ci gaba da (research) akan magungunan Musulunci, wanda yasa suka fita suka yi wani (course) na tsawon shekara biyu a Saudi Arabia kan magungunan Musulunci da kuma cuta da maganinsa a Musulunce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sun dawo ne suka sayi babban fili a Festac cikin garin Lagos suka sake fadada asibitin su tare da gina gidansu a hade a ciki, har da makaranta suka bude ciki na yara da manya, inda ake (counseling) marasa lafiya manya ko yara akan abinda ya taba musu kwakwalwa ko zuciya. Sun dauki manyan malamai masu ilmi suna kula da wannan bangaren.
Kafin akai ga fara na asibiti sai anyi wannan sannan a dinga hadawa bibbiyu, da ikon Allah ana samun waraka.Lokaci guda asibtin su ya yi suna, Allah Ya daukaka su har kasar waje an san da zaman asibitin. Haka manyan masu kudi suka dinga kawo musu gudunmawa daga ko wane bangare na kasar, musamman wadanda suka kawo yaran su suka sami waraka.
Allah Ya daukaka su da su da aikinsu, saboda aikin da suke yi don Allah ne Allah kuma kadai Yasan iya yawan marayun da suka dau nauyin su. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bahijja tana samun ciki amma yana ɓarewa, sai dai bata taba damuwa ba daga ita har mijinta, saboda sun san basu da matsala, lokacin zaman cikin ne bai yi ba.
Bahijja da Mislihu aikinsu ba sana’ar su bane kadai, tamkar (passion) din dake ciki yana basu nutsuwa da farin ciki da kwanciyar hankali.
Hakika ba abinda ya fi taimakawa wanda suke bukatar taimako farin ciki, a duk lokacin da suka dafawa mai bukata suna tsintar kansu cikin tsananin farin ciki da nutsuwa.
Mislihu ya zama shi ne komai na Bahijja, haka itama. Suka gina rayuwar su da duniyar su

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE