MISBAH CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

MISBAH CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yammaci ne mai cike da sanyi hade da ni’ima tare da kamshi irinna damina, dai dai wannan lokacin ta fito daga islamiiya iska na kada hijabinta tare da hura fuskarta yana ratsata.haka nan ta dinga jin soyayyarsa tana bin jikinta, tana ratsata,kewarsa taji tana shigarta.farida kenn matashiyar budurwa da bata wuce sha bakwai ba .

 

  Daga kai tayi ta kalli gate din gidansu data zo wucewa ,haka nan zuciyarta ta bata ta shiga gidan wanda yake makwabtaka da gidansu, haka nan gidan tamkar nasu gidan ne .

    Nan ta tura karamar kofar shiga gidan ta kutsa kai tana tafiya cikin nutsuwa ,zuciyarta na magana tana tunanin wacce dabara zatayai taga NURA ? Da wannan tunanin ta shiga falon gidan ,tayi sallama .

         Mama ce ta amsa mata tana daria ,tace Farida ce ? Yan mata ,an taso daga islamiyya ?

  Ta sunkuyar da kai tana dariya ,ita dai mama ranta nason farida ,yarinya me kunya da tarbiyya .

    Nan ta zauna bisa carpet ta gaida mama ,ta amsa da fara’arta tare da tambayarta karatu na islamiyya dana boko, ta amsa da Alhmdllh .nan tayi mata addu’a tare da fatan alkhairi .

    Tana nan baba ya shigo wanda hakan yasa mama mikewa dan daga tafia ya dawo.faridan ta gaisheshi tare da amsar kayan dake hannunshi tayi kitchen dashi, sannan tadawo ta gaisheshi tare da yimishi ya hanya, yana daria ya mika mata wata leda dake dauke da zannuwa guda biyu masu kyau da tsada , yace to kinga kin tarar da tsarabarki ,ki dauki daya ki bawa Aisha kanwarki daya .

  Tayi murmushi tace ,”nagode baba, Allah ya kara arziki”

Nan ya haura sama ,mama ta bishi .

  Wannan yabawa farida damar zuwa bangaren nura wanda suke kira da DEENI .

Nan ta kwankwasa kofar dakin shuru ,ta kwankwasa ya kai kamar sau uku shuru ba motsin kowa ,hakan yasa ta tura kofar dakin tare da yin salllama. Har yanzun shuru tamkar ba me rai a ciki,sai karar Ac da sanyinta ya ratsata tare da kamshin turaren deeni mai qamshi da dadin gaske .ta lumshe ido tana shaka ,tana jin sonsa a ranta..

  A hankali ta dunga ratsa dakin tana ganin yadda ya tsara dakin ,ta kwantar da kai tana murmushi a ranta tace, “shiyasa nake sonka deeni,daga yanayin yadda ka tsara dakinka ya nuna halayyarka da personality dinka a zahiri ,,wannan yasa banajin akwai namiji irinka a duniya, kai daban ne,kai nawa ne ,kai mallakina ne”

 Nan ta lumshe ido ,ta fada wata duniyar tunanin wadda daga ita se deeni a ciki ,wata rayuwa mafi dadi a cikin rayuwar duniya”

Ta jima a haka sannan ta ware idanu tana neman ina nuran yake ?tunaninta yabata ba ya dakin,, hakan na nufin baya gidan . Nan ta turo baki alamar bataji dadi ba .

Naso ganin deeni yau ,kuma sai ya fadi dalilin da yasa naji shuru kwana biyu ban sashi a idona ba ,sai ya biya pains din danaji a zuciyata na rashin ganinsa da tsada “”

   Har zata juya sai wani haske na daban ya dau hankalinta ,wannan ya tuno mata da study room dinshi dake manne da dakinshi ,nan ta nufi gurin da saurinta .nan ta hangoshi cikin tsakiyar takardu suna zube a gurin , yayin da ta hangoshi fuskarsa mai sauke mata duk wani jin dadi da nishadin a zuciyarta ….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE