MISBAH CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari bayan sun gama breakfast ,Alh. Umar tare da shamsu da likman duk sunyi shirin fita office yayin da lukman makaranta zai tafi.

       Alhaji ya kalli shamsu dake shirin mikewa yace ,

    ” ka zauna ina da maganar da nakeso muyi da kai da mahaifiyarka ,kai kuma lukman kaje driver ya ajiyeka a makaranta”” 

     Nan ya mmike ya fita ,yayin da shamsu ya bar dining table din ya nufi tsakiyar falon kamar yadda yaga mahaifinsa yayi yana tunanin to wacce magana Alhaji zai yi da shi haka?

   Mama ta iso cikin falon ta zauna a kujerar da ke kallon tashi , tace .

   ” *Alhaji muna sauraronka ,wace magana ce haka?

  Ya gyara zama yace,inaso ku saurare ni da kyau da kunne basira,kwanakin baya kafin deeni ya tafi karatu munyi wani shirri ni da mahaifin farida. Maganar gaskia bamu shirya maganar auren deeni da farida ba  ,sai shamsuddeen da farida ,haka kuwa bazai yiwu ba har sai deeni ya tafi karatu ya bar kasar nan,tafiyarsa kuwa abu ne mai wuya in ba har yaji za a aura masa farida ba.

      Maganar gaskia mahaifin farida bai yarda da barin ‘yarsa tayi jiran shekaru biyar ba,ni kuma ban yarda da aurawa deeni mace ba tare da ya gama karatu ya mallaki hankalin kansa,yasan ciwon kansa ba daga farida har deeni soyayyar yarinta ce ke damun su,dukkan su basu san ciwon kansu ba ,ba yadda za’ayi mu hadasu aure da deeni .

   Sai dai maganar ta mana amfani , na sami deeni ya nutsu yana karatu,kafin shekara biyar din nan zai shiga ruwan hankalinsa,ya nutsu ,zai mance farida idan yaji dan uwansa ya aureta ya fara sabuwar rayuwa. Itama kafin nan zata gane shamsu shi ne wabda ya dace da ita.

    Babban dalilin kulla wannan aure shi ne ,na farko dacewar farida da shamsu,tana dai dai lokacin aure shima haka. Sannan Nuraddeen ya bata mata lokaci ,tun tana karama bata bawa wani saurayi dama ba sai deeni,ba zan so yanzu da ta tashi aure ya zama tamkar deeni ya yaudar ta ba. Yanzu bata da wani,haka bazan so kuma mahaifinta ya aurar da ita ga wani wanda bai dace da ita ba ,wanda bazai bata kulawar da jindadin da ya dace da ita ba . Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Farida tamkar diyar cikina na dauke ta ,shiyasa zan damka amabarta ga dana wanda na yadda dashi ,na amince masa. Inada tabbacin shamsuddeen zai bata duk wata kulawa da kauna matsayin mijinta. Sannan burina da naki zai cika na ganin farida ta zama surukar mu,zamu hada jini da zuri’a dasu ,zata haifa mana yan jikoki. Da Shamsuddeen da Nuraddeen duk abu daya ne a wurin mu,don haka mun yanke hukunci a watan sha biyu za muyi auren su december ,sai ku soma shiri.” 

     Yana gama fadi ya mike zai fita,,hajia tayi saurin mikewa cikin girgiza da firgitar jin maganganunsa hade da mamaki,yayin da shamsuddeen kansa na sunkuye,maganar mahaifinshi ta mugun kadashi da bashi tsoro. A kullum yana yiwa mahaifinshi abinda yake so,amma wannan karan zasuyi tsiya irin wadda basu taba yiba ,don kuwa ba zai taba auren macen da kaninsa,jininsa,dan uwansa ke ciwon so ba.

        Hajiya ta sha gabansa,ta tsare shi da ido ,ta ce

     ” wacce irin magana kake ne me kama da ta yara? Ba na tsammanin deeni da farida yara ne ,sai dai kai da mahaifin farida ne tunaninku irin na yara. Kuna nufin kuce min kun yaudari yaran ku kenan? Kun yiwa yaranku karya kuna iyayensu ? Kana son fada mun zaku wargaza rayuwar yaranku da hannun ku ? 

    Na yarda na amince ina son farida matsayin sirika ,haka kuma babu bambanci tsakain shamsu da nuraddeen a wurinmu. Sai dai fa inaso kasani akwai bambanci tsakanin deeni da shamsudden a wajen farida . Zuciyarta da ruhinta gaba daya deeni suke so,deeni suke muradi.

Wannan maganar da ka kawo bata wasa bace,kanason haddasa gaba tsakanin yaranka ,ka dauki abinda daya take matukar so kabawa daya? Shamsu yace maka yanason farida ne ko ita faridan ta fada maka zata amince ta auri shamsu ? Kasan ko yawan soyayyar da ke tsakanin farida da deeni?

        Wannan ba damuwa ta bace ” ya fada cikin daga murya da bacin rai,ya ce 

   ” karki zata maganganunki zasu canja min niyyata da ra’ayi na,ba shawararki nake nema ba ,ina fada muku ne dake da danki ku soma shirye shiryen biki,banason sake jin wani raayi naki ko na wani musu akan maganar nan “” ya kalle shamsu da kansa yake sunkuye , ya kira sunansa. 

   ” Kai shamsudden ,dago kai ka kalleni nan ” yayi saurin dago kai cikun tashin hankali da kuma tsorata da yanayin mahaifin nasa, yace . Www.bankinhausanovels.com.ng 

Na maka zabin mata matsayina na mahaifinka ,ina fata ba zaka bani kunya ba idan har na isa da kai,kuma na taba maka wani alfarma a duniya a matsayina na uban da ya kawo ka duniya,to ina so kayi biyayya ga maganata ka auri farida, ka rike ta hannu bibbiyu da amana . Ni nan mahaifinka nina baka amanar farida kanaji na ? In kuma kana ja to inji “

 Ya sunkuyar da kai muryarsa na kyarma yace ,,naji baba ,na amince,na maka biyayya,bani da ja ,”

     Mahaifin nasa yayi murmushi , ya ce naji dadi ,Allah ya maka albarka ,Allah yasa ka gama da duniya lafia,Allah yasa ‘ya’yanka su maka biyayya kamar yadda ka mun “”

    Ya kalli mama cikin bacin rai ,ya ce.

 Saura wani yayi garajen sanar da deeni abinda ke faruwa,ko ma waye ne zai fuskanci mummunan fushi daga gare ni””

   Yana gama fada ya juya ya fita,ya bar mama da shamsu cikin balain tashin hankali.

    Hada kai yayi da gwiwa tamkar wani karamin yaro yana kuka ,hankalinsa ya mummunan tashi . Duk yadda ya kai ga kin auren masoyiyyar dan uwansa bai isa ya ki bin umarnin mahaifinsa ba,bashi da karfin gwiwar kin yiwa mahaifinsa biyayya ,ya zama dole ya bi umarnin mahaifin sa kamar yadda ya ke masa tun yana dan kankaninsa. 

    Mama ta tsinci kanta cikin rashin hankali da kaduwar da itama tana bukatar mai lallashinta balle ta lallashi shamsu.

       Sai dai shamsu ya kasa jurewa har sai da ya matsa gabanta yana kuka yana fadin .

      Mama ki taimake ni kiyiwa baba magana ,ya za ayi in auri farida yarinyar dana shaida soyayyarsu da kanina da nake matukar so ? Tun suna yara ni na san irin soyayyar sa sukewa juna ,mama ya za ayi in jefa kannena biyu cikin tashin hankali da bakin cikin rabuwa da juna? Ya za ayi in raba su ta hanyar auren farida ? Mama da wane ido zan kalli Deeni? 

   Kasa magana tayi saboda bata da abinda zata iya fada masa illa ta taya shi kuka ,hawaye taji yana gudu a fuskarta,tausayin yaran nata duka biyun ya kamata.shin mahaifin su bashi da zuciya ne da bai tausayinsu ? Ko baya hangen cewa zai hada gaba da fitina a tsakanin yaransa? 

     Da kyar ta iya budar baki tana lallashin sa tare da bashi hakuri cewa basu da yadda suka iya ,saboda mahaifinsu yafi karfin su duka . Www.bankinhausanovels.com.ng 

      ” ka dage da addu’a in haka shi ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar ,in kuma ba alkairi Allah ya warware shi.

     Mama ina alkairi a auren cin amana ? Mama kin tuma har deeni ya shiga jirgi yana bani amanar farida ? Mama yaya deeni zai dauke ni in yaji na ci amana na auri macen da take rayuwar sa,farin ckin sa,koman sa ? 

 Tayi murmishin karfin hali tace, kar ka damu ,Allah na nan ,kayi kokarin mai da al’amarin ka gare shi,haka nan deeni ya san halin mahaifinku,zai fahimci ba kayi auren ne da niyyar cin amana ba . Www.bankinhausanovels.com.ng 

     Shamsu ,yana da kyau ka  kwantar da hankalinka ,kasawa kanka auren farida ko baka so,ka tursasawa kanka da zuciyarka,saboda tun da mahaifinka ya lashi takobi sai ka auri farida to ba makawa saika aureta ,sai wani ikon Allah,,””

Nan ta shige ciki ta barshi a wurin a durkushe ,abin duniya ya masa zafi. Daga karshe ya mike ya koma dakinsa,office din da bai fita ba kenan. Ranar mahaifinsa ya masa wannan uzurin ,don yasan halin da ya tsinci kansa . Ya bashi dama yaji da kansa da zuciyar sa.

    Haka mama ta koma daki hankalinta tashe ,idonta rufe tana addu’a da fatan kar wanan abu ya zama sanadin wargaza kan ‘ya’yanta ,yayin da tausayin farida da deeni ya cika mata zuciya . Tabbass zasu fuskanci tashin hankali,sai dai zata taya su da addu’a Allah ya basu juriya……¹⁵

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE