MISBAH CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

Sati guda da tafiyar Deeni komai ya mike masa,ya gane yadda wurin yake. Gida guda mahaifinsa ya sama masa kusa da makaranta,bai samu wata matsala ba ya fuskanci abinda ya kawo shi,ya hau karatu gadan-gadan . Ganin ya mike yasa mahaifinsa ya yi sallama da shi ya dawo gida nigeria don fuskantar nasa ayyukan.

 

    Ya dawo hankalinsa kwance,bashi da wata matsala ganin deeni ya mike kuma da gaske yake,wannan ya matukar bashi kwanciyar hankali.

    Duk da Deeni yana matukar kewar farida,amma ya daure bai mata waya ba saboda gudun mai da hannun agogo baya,a duk lokacin da zai ji muryarta dukkan wani kokarinsa zai iya komawa baya,hankalinsa zai tashi yaji yanason komawa ya ganta. Don haka ya daure,ya hora zuciyarsa da rashinta na tsawon lokaci ,sannan ya kirata.

        Da farko ta nuna masa fushinta na kyaleta da ya yi ba waya da kuma tafia da yayi ba tare da ya bari ta masa rakiya ba . Sai da ya jira ta gama mitar sannan ya ja dogon numfashi ya ce.

    “” farida na,farida matar Deeni . Kinsan deeni da irin son da yake miki ,trust me inada da dalilina na yin haka”” 

     ” Na sani Deeni ” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ta fada murya kasa kasa,ta kara da cewa.

    ” ina kewar ka ne kawai Deeni,kasan na saba da kai da soyyyarka ,Deeni ba dadi da baka nan “

          Yi hakuri farida,zai zama tarihi”

Ya canja zancen ta hanyar zolayarta da cewa,

    Nasan duk randa kikazo America kika ga dogon gini rudewa za kiyi ,saboda farida ta yar kauye ce “

   “” Ta turo baki tamkar yana ganinta ,ta ce. 

     “” kai da bamu ga ka rude ba ,saboda kaima dan kauyen ne ai” 

      Yace oho dai ,ni dai yanzu na zama dan birni na barki” 

    Dariya sukayi duka,sun jima suna hira suna bawa juna labarin yanayin da suka shiga da kuma halin da suke ciki. Ya bata labarin yadda yake matukar jin dadin karatun sa a yanzu,,yake kuma ganewa,saboda yadda aka saukaka musu shi,sabanin yadda yake a nigeria. 

   Itama ta bashi labarin makarantar high islam da mahaifinta yasa ta koma,saboda yaki barinta tashiga university sai dai tana karuwa sosai ta fuskar addini a wannan makarantar ,tana kuma ganewa ,tana jin dadin karatun addini. 

     Sunyi sallama da juna ,suna yiwa juna addu’a da fatan alkairi,zuciyoyin su cike da jin dadi da farin cikin magana da juna 

Wasa gaske deeni ya mike da karatu har ya saba da rashin farida ,yana kiranta wani lokaci sau daya a wata ,saboda dagewa da yayi ya fuskanci karatun dake gabansa,soyayyar farida na kara masa karfin gwiwa. Haka itama farida kullum suka yi waya sai ta karfafa masa gwiwa da kara jaddada masa soyayyar da take masa . 

      Itama haka tayi sabo da ba sa waya da deeni sosai sai lokaci lokaci,kuma ta fahimci dalilin sa don haka tayi masa uzuri ta fuskanci nata karatun tare da musu addu’a. 

 *      *       *      *      *

 Zaune yake a falo shi daya yana kallon labarun karfe tara ,Alh umar kenan ya mai da hankalinsa gaba daya kan jin abinda ke faruwa a kasar tamu, lokacin Alh Ahmad ya masa sallama ya shigo falon. 

       Ya mike da sauri yana dariya ya tare shi saboda muhimmancin da yake dashi  a wurinsa,yana matukar girmama shi,da kuma dangantakar su ta makwabtaka. 

         Nan ya nuna masa wurin zama tare da sawa a kawo masa abin sha. Suka sake sabuwar gaisawa,suka dan taba hirarsu data shafi kasuwanci da kuma kasar gaba daya. Tare suma kalli labaran suna sharhi akai www.bankinhausanovels.com.ng 

     Bayan sun gama Alh Ahmad ya kalle shi ya ce .  

 “” ya labarin deeni kuwa ? Duk da dai muna waya da shi amma mun kwana biyu bamuyi waya ba ,yana lafia ko ?

    Alhaji yayi murmushi yace ,lafia kalau,ya maida hankali yana karatu yadda ya kamata. Ina kara maka godia bisa taimako da hadin kai da ka bani “”

     Alh.Ahmad ya yi daria ya ce ,”Ai deeni dana ne,kamar yadda ku ka riki farida kamar ‘yarku haka nima na riki deeni””

       Ya kara kallon sa da kyau yace,,”yanzu ma maganar yaran nan ce ta kawo ni,kan maganar da mukayi kwanaki ,kaga tsahon wata tara kenan da tafiyar deeni,komai ya mike masa ya soma fuskantar karatunsa da gaske,haka nutsuwa tana kara shigar sa,din haka inaga lokaci yayi da zamu fito mu bayyanawa yaran nan da iyayensu mata manufar mu da kuma dalilinmu ,kaga watan sha biyu nakeson auren yaran nan ,kuma har da farida ciki,kaga yanzun wata biyu ya saura ,gara mu sanar dasu su shiryawa maganar auren tun wuri;””

       Alh. Umar ya sauke ajiyar zuciya ,yace. Www.bankinhausanovels.com.ng 

   ” kayi gaskia tamkar ka shiga cikin zuciyata ne,inada shirin maka maganar sai ka rigani ,inaga yanzu abinda za’ayi ,ka kira farida da mahaifiyarta kayi musu bayani,haka nima nan zan kira nawa iyalin nayi musu magana. Abinda nakeso da kai shi ne,mu tabbatar musu da maganar da muke fada UMARNI ne muke basu ,maganar mu doka ce a gare su ,dole su bita ba wai ra’ayin su muke nema ba. In munyi haka zai zo mana da sauki,amma in muku nuna ra’ayinsu muke nema zai sa mu sami matsala ,zai zamana tamkar mun basu damar kin bin abinda muke so ne “

Alh Ahmad yayi dariya,yace,,kayi gaskia ,maganarka abin dubawa ce. Inaga gobe in Allah ya kaimu zan kirasu muyi maganar,zaka ji yadda mukayi da su” Www.bankinhausanovels.com.ng 

      Alh. Umar ya amsa da,nima in Allah ya yarda goben zanyi magana dasu,sai mu duba ranar da ta dace mu tsayar da ranar biki”

     ” To shikenn ,Allah ya kaimu goben ” 

     Da wannan. Maganar suka yi sallama ,tare da yiwa juna sai da safe akan zasu hadu washe gari bayan tashi daga harkokin su da yamma za su hadu……….

SHIN IYAYEN SU SUN YARDA ZAA AURAWA DEENI FARIDA NE KAFIN YA DAWO ????

 WANI IRIN FARIN CIKI DEENI ZAI YI IDAN YA SAMU LABARIN AN DAURA AURENSHI DA FARIDA? 

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 


No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by A/I/S
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE