MISBAH CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Kai Babana ne ,ME SONA ,me yanke dukkan wani hukunci na rayuwata saboda ka kawo ni duniya ,ka bani ci da sha, ka kula da lafiyata da karatuna ,ya zamar min dole in maka biyayya.

   Nayi biyayya baba da abinda kayi ,sai dai baba ka taimake ni wannan abinda nakeji baba ban taba jn irinsa ba,baba bana ganinka sosai ,duhu na rufe mun ido,ina jin duniyar na zagawa dani ….

     Kama kansa yayi da karfi,basu ankara ba sai ganinsa sukayi ya fadi ,ya zube kasa a sumeeee………….

Alh Umar ya mugun rudewa ,rabon sa da ya zubar da hawaye har ya manta,amma a wannan lokacin sai da ya zubar da hawaye,hankalin sa ya mugun tashi.ya tsorata da lamarin Deeni,haka shamsu duk jikinsa ya mutu,ya rasa me ke masa dadi,ga halin da Deeni ke ciki ,ga na farida.

       Tare suka nufi asibiti dashi,in da faridan take nan suka je,sai dai ita an dace an shawo kan alamarin ,sai dai tayi barin cikin har an mata wankin ciki tare da bata magunguna da allurai.

     Tana kwance tana hawaye ,mama rungume da ita tana bata baki da nuna mata ta ci gaba da dauriya da cijewa kamar yadda tayi a baya,,zai wuce.

   Umma rike da Deeni karami tana kallonsu,ta kasa fadin komai sai tsabar tausayin ‘yarta da ya kamata,ta shiga halin tsaka mai wuya.

    Nan ta matsa itama tayi mata nata nasihar ,sannan ta ce zata wuce gida da Deeni,sannan zata shirya musu abinda za su ci ta aiko asibitin. Mama kuwa tace zata zauna da ita.

    A nan ta samu damar kwaniciya a cinyar mama tayi kukanta sosai,mama bata hanata ba sai dai bata fasa lallashi da bata baki ba.

     Suna cikin wanann halin shamsu ya iso yana rude ,mama ta kalle shi tace,,,,

 Ka dauki abin nan a hankali,komai ta yi zafi maganinsa Allah.”

     “Mama Deeni yana kwance a emergency tun dazu muna can likitoci a kansa sai yanzu muka samu ya farfado,”

   Hawaye ne ya gangaro masa,ya ce,”Mama Deeni yana cikin wani hali wanda mu ne dalili.” 

    Da sauri mama ta mike ba tare da ta karasa jin me yake fadi ba ta fita wurinsa,Shamsu ya matsa gaban farid yana fadin . “Ban baki kulawa ba lokacin da kike bukata,saboda Deeni yana bukatar kulawata fiye dake. Farida ban kara sanin cewa bamu kyautawa Deeni ba sai yau da naga halin da yake ciki ,halin da ya shiga yana cikin tsanani da firgita tare da zafin zuciya da kwakwalwa””

     Ta fashe da kuka ,”Ya shamsu ba abinda zai samu Deeni ko? Ya shamsu munci amana..”

   Ta fada a lokacin da ta kara fashewa da kuka .

  ‘Ya Shamsu ba zan iya fuskantar Deeni ba har abada,fatana Allah ya bashi lafia,yasa kuma ya manta dani da wannan cin amana da muka masa.”

 

    ” Ba mai sauki bane farida ,tabbas bamu kyauta masa ba ,har ga Allah bamu kyautawa Deeni ba ”  Nan suka lallashi juna ,daga karshe Shamsu ya kama ta suka nufi gurin Deeni a emergency.

      Tana hango shi ko daga nesa ne,hango shi tayi yana kwance idonsa biyu sai dai ya kau da kai hawaye kawai ke zuba masa,ransa a mugun bace,hankalinsa a tashe.

     Tausayinsa da tsohuwar soyayyar sa taji sun taso mata suna tsuma zuciyarta,tayi saurin dafe kirji tana hawaye,ta lura ya kara girma da haske hade da wani irin kyau duk da yana cikin tashin hankali.

    Ta lumshe ido tana jin wani abu mai ciwo da radadi yana ratsata.

    “Ka yafe min Deeni na ci amanar kauna ,sam ko kadan ban yi fighting wa soyayyar mu ba,nayi saurin mika wuya . Na cika makiyarka da nayi sanadin jefa ka a cikin wannan halin,nasa ka dandani wannan zafin zuciyar. Allah ya baka wacce ta fini,ni kam ban dace da kai da rayuwar ka ba da soyayyarka,tunda can ma kila shiyasa Allah ya rabaka dani. Na tabbatar Allah zai baka wacce tafi dacewa da kai,sai dai ka sani Deeni ba zan daina sonka ba ,har abada soyayyar ka zata kasance a cikin karkashin zuciyata. Sai dai zan danne ta in ci gaba da rayuwa ta da mijina gami da faranta masa iyakar iyawa ta..””

    Muryar mama ce ta katse mata maganar zucin da take yi,ta mai da hankalinta kansu.

    Mama ke masa magana cikin kwantar da murya,tana shafar kansa kamar karamin yaro tace,,”” Deeni kayi hakuri ,bani da abinda zan iya baka sai hakuri ,ba wani bayani ko kokarin kare kanmu da zan maka. Magana guda ce ,mun maka laifi duk da muna manya kai kana karami ,amma mun maka laifi,mun zalunce ka,kayi hakuri ka yafe mana,kar kayi fushi damu.”       Deeni yayi murmishin karfin hali yace,”Fushi “” ? Da wa zanyi fushi ? Kuma ni waye da zan yafe muku ? Ku iyayen mu ne,kuna da damar yin yadda ku keso. Da mahaifin farida zanyi fushi don ya zabawa ‘yarsa miji ? Ai bani da hujja.   Da farida zanyi fushi ,masoyiyata ,wacce ta min alkawarin soyayyarta da kanta ,wacce tun muna yan kanana muke wa juna son da bamu san irinsa ba ? Ko da yayana da na bawa amanar masoyiyata ,wanda yasan duk wani sirri da tarihin son da nake wa farida ? Ko da nahaifina da ya yaudare ni ya min karya? Ko da mutumin da na dauke shi tamkar mahaifina yace min ya mun alkawarin bani yarsa har inje in dawo ? Ko da mamana mahaifiyata da ta boye min gaskiyar magana?   Mama da wa zanyi fushi a cikinku ? Kuma meye riba ta in nayi fushi da ku ? Abinda ya faru zai canja ne ? Ya mike cikin zabura da zafin zuciya ,ya ce.

     “Damuwata shine yadda zan share wannan mummunan al’amarin daga kwakwalwata da zuciyata ..””

   Ya kalli likita dake tsaye a kansa tare da mahaifansa ,ya ce

    ” Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala ilminka ya kai inda za’a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka  bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..””

   Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar aka samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.

     Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.

   Mama tana kuka tana tofa masa addu’a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani…………..²⁶

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE