MISBAH CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

MISBAH CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Naso ganin deeni yau ,kuma sai ya fadi dalilin da yasa naji shuru kwana biyu ban sashi a idona ba ,sai ya biya pains din danaji a zuciyata na rashin ganinsa da tsada “”


   Har zata juya sai wani haske na daban ya dau hankalinta ,wannan ya tuno mata da study room dinshi dake manne da dakinshi ,nan ta nufi gurin da saurinta .nan ta hangoshi cikin tsakiyar takardu suna zube a gurin , yayin da ta hangoshi fuskarsa mai sauke mata duk wani jin dadi da nishadin a zuciyarta ….

Cikin nutsuwa yana karatu ya mai da hankalinsa sosai kan littafin, duk wanda yaganshi yasan yana karanta wani abu mai matukar mahimmanci da motsa kwakwalw da tunani.

      Ta jima tana tsaye kansa amma ko alamarta be ji ba ,,sai data kalleshi iya san ranta sannan tayi mishi uzuri data tuno gagarumar jarrabawar da ke gabansa,,haka nan tasan naci ne kawai ba wai dan yansan karatun ba ne sai yayi dagaske yake iya fahimtar karatun, sabida wannan bashi ne ra’ayinsa ba ,ra’ayine na mahaifinsa ya bi don ya faranta masa rai..

     A yadda tasan deeni mutum ne wanda baya son karatu me tsanani ko me zafi ,,deeni yanason abubuwa masu sauki haka rayuwarsa da tunaninsa duk masu sauki ne ,duk da tafito daga gida da yake cike da mutane masu zafi ,mutane ne masu matsayi,,rayuwarsu me tsada ce,tunaninsu mai girma ne,yayin da shi kadai ya bambanta..

        Deeni masoyin abubuwa masu sauki ne ,farin cikinsa yanaga abubuwa masu sauki..

   Deeni masoyin tsuntsayene ,dabbobi da duk wani abu da bai da bakin magana. Abu uku ke tsananin sanyashi farin ciki a rayuwa ,karance karance game da rayuwar wasu mutane daban da bai sani ba ,mutum ne me son karatu da bincike sai swimming pool wanda yana matukar sashi nishadi ,sai zama cikin tsuntsaye da dabbobi yana karantarsu,yana fahimtarsu tare da connecting kansa da su,sai kuma soyayyar farida data zame masa wani haske a rayuwar. Don haka a study room dinsa cime yake da takardu kala kala tun daga kan na larabci ,hausa dana turanci,na tarihi dana addini. Sai kuma takardunsa na makaranta da suka zame masa dole badan son ranshi ba sai don mahaifinsa.

       Duk da farida tasanshi da son karance karance yadda hankalinsa ya tafi akan littafin har beji motsinta ba yabata mamaki,mutumin dake fahimtar tana guri tun kafin ta iso  inda yake shine yau ta iso har gabanshi amma be san tana gun ba ,hakan yasa ta sunkuya dan taga wani irin littafi ne haka daya dauke mishi hankali har fiye da ita ?nan idanunta suka hango mata abu daya data tsani gani ,suna daya data rsani gani ba dan ta tsani me sunan ba sai dan yadda wannan marubucin ya ke dauke hankalin masoyinta akanta,,duk kuwa yawan son dayake mata..Tayi tsaki tarw da fisge littafin ,bai ankara ba ta galla masa harara tarw da turo baki ,cikin tsiwa ta ce “SAUYIN SHAUKI ko? The change of emotions) shi ne abinda zakaje ka rubuta a exams din ko ? Na tsani marubucin nan l just hate wannan writer din,saboda kai na tsani wannan MISBAH din “

     Tayi wurgi da littafin ta fita tana mita ,ya mike da sauri ya bita hankalinsa tashe ya sosa ran farin cikin rayuwarsa.

“” haba farida na,,kinsan fa bani da kamarki a duniyar nan”

   Nan ta dalla masa harara,”ai naga alama ,shiyasa har nashigo nagama tsayiwata a dakin baka san inayi ba ,naga yawan son da kake mun . Wannan banzan liffafin MISBAH din yafini muhimmanci” 

  “Oh oh !!  Haba farida na ya kike hada kanki dawani writer daban,ai darajarki ya wuce haka a gurina ,ni fa i have nothing to do with MISBAH ,damuwata shi ne brains dinsa,da intelegent dinsa” hakan ya kara kular da ita tace “to ai sai kaje kayi soyayya da brains dinsa da labaransa ,kaje ka  rayuwa da labaransa,dama new version na littafinsa ya fito shi yasa kwana biyu ban ganka ba ,na zata karatun exams kake ashe kaba nan kana wai abun daban ,to nafasa soyayyar ma “

“Haba farida na ,ai bazan iya rayuwa ba ke ba ,kema kin sani kece macen kadai da deeni zai iya rayuwa da ita,kece kadai macen da zata iya jan ragamar rayuwata ,in ba farida ai ba deeni”

 Ta turo baki ,ni dai gaskia ban yarda ba farida ta fada”

  Farida kalle ni mana “ya fada cikin murya me kashe jijiyar jiki ,ba shiri ta juyo tana kallonshi. 

 Ya harde hannu tare da zuba mata idanunshi masu rikira zuciya da kwakwalwarta,yana mata murmushi me kwantar da hankali da dauka bacin rai.

Yace tama ki yarda dani farid,trust me you re d most important person in my life,kece macen da tafi komai muhimmancin a rayuwata,my love ,my wife, my friend .

    Tuni jikinta ya mutu,taji wani irin sonsa me karfi yana tsuma ta ,ta dinga jin tamkar ta rungume shi,ra zauna a jikinsa har abada.

   Ta kwantar da kai tana masa kallon kauna tace ,,”  deeni kamin alkawari as long as ina rayuwarka bazaka sake karanta littafin MISBAH ba ,komai koyarwarsa ,komai ilimin dake cikinsa ,saboda littattafan MISBAH sun zama kishiyoyina ,shi ne abu na farko dana taba gani yana kokarin janye hankalinka a gare ni. Deeni bana son ganin abinda zai janye hankalinka daga kaina…. 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE