MISBAH CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
MISBAH CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Tunda deeni yadawo daya masallaci bayan sallar isha ya zubawa wannan littafin na MISBAH ido,wanda farida tayi wurgi dashi ,labarin ya taba zuciyar sa da tunaninsa,yanason sanin ya aka kare amma kuma alkwari yayi ,haka nan farida na gaba da wannan labarin . Www.bankinhausanovels.com.ng
Yasa hannu ya dauki littafin yasa shaida a inda ya tsaya ,ya rufe yana kallon littafin har yasa shi cikin wata karamar drower ya rufe ,yana tunanin kalmar nan ta sauyin SHAUKI anya kuwa ?change of emotions gaskia hakan bai yiwuwa ba,gashi shi yakan gasgata duk wani labaran MISBAH ,yana da yakinin duk wani abinda ya fada yana iya faruwa,infact yana ma faruwa ,to amma wannan karon yana da ja ,sabida bai taba yadda shauki yana canjawa ba ,musamman ma shauki irin nasa,shauki na gaske ,shaukin da ya jima yana gina shi gini me karfi da tushe ,rushe shi abune da bazai taba yiwuwa ba balle a akai ga canji ..
Nan ya yi saurin canja tunani ya dakko littafin sa yana karantawa ,amma fa karatun babu abinda yake tunawa sai littafin . Tuni haushin kansa ya kama shi , ya ma zaayi ya bari haka ta faru dashi ,?
Zuciyarsh yaji tana zafi ,,deeni akwai dan banzan zuciya,tuni yaji tana hawa. Rufe ido yayi yana addua cikin zuciyarshi,sannan yayi saurin mikewa yabar study room din ,ya nufi cikin dakinsa ya dakko laptop dinsa yana kallon hotunan farida yana murmushi,,wasu hotunan nata tun tana jairirya,wasu kuwa tana yarinya ,,wasu kuwa suna tare tun suna yara har zuwa girmansu..
Waya ya dauko ya buga mata ta dauka tana murmushi tare da kashe murya tana mishi kalaman soyayyar da yake so,wanda suke kara haukata zuciyar sa da soyayyarta.
Lumshe ido kawai yayi yanajin kaunarta na bin jikinsa,yana ratsawa tare da hango su suna gudanar da wata rayuwa me tattare da tsananin so da kauna,,tare da farin ciki mara iyaka.
Bayan sun gama wayar ne ya turawa MISBAH labarinsa kamar yadda ya saba ta email dinsa,yana yawan sharing feelings dinsa da kuma experience dinsa akan soyayyarsa da rayuwarsa ,da tarin tunaninsa da kuma hangensa, harma yayi challengn sabon labarin sa da ya rubutu na CHANGE OF EMOTIONS .
Duk da MISBAH bai taba bashi amsar emails dinsa ba bai sa ya fasa rubuta masa ba ,,saboda yasan ba dole ne saiya karanta ba,kuma in ya karanta din ma ba dole ne yabashi amsa ba. Irin su misbah dole za suyi jin kai da miskilanci,duk littattafansa yana nuna illar girman kai,,don kuwa Allah ke bada daukakar da mutum zai yi takama dashi,in yaga dama zai iya kwacewa dare daya,wanda a wannan lokacin matsalarshi da mutane zai iya taimakonsa,sai Allah sai dai yasan akwai mutane dayawa da suke da bambanci a rubutunsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rashin amsar da misbah baya bashi be damshi ko ya bashi mamaki ba ,saboda dama ya zaci haka daga gareshi. Yasha masa tambayoyi amma shuru ,dan haka ma wannan karan yana gama tura masa email din ma ya rufe . yasamu karatun ya fara shiga yana fahimta kadan kadan har bacci ya dauke shi .
Deen matashin saurayi ne dogo ba baki ba,kyakkyawan gaske . Ba kyanshi zai sa kasoshi ba se halayyarshi ,yana da shiga zuciya . Matashi ne da yake da kula da addininsa sosai,ya yarda cewa Allah zai taimakeshi a rayuwa,zai cika masa burinsa na samun mace saliha,kamila ta gari…
Bayan bautar ubangiji da biyayya ma iyaye deeni bashi da wani buri da wuce yayi aure ,rayuwar cikin aure da yadda ya tsara zai yi shi,rayuwa ce me cike da soyayya da kuma ibada irin wadda annabin mu (SAW )ya yi da matansa,dan haka kullum adduarshi Allah ya cika masa wannan burin nasa tare da farida.
Duk wani abu dayake fata da so da tunani a mace to farida na da shi,ga kuma soyayyar da sukewa juna mai tsanani wanda wannan shi zai taimaka su gina rayuwar auren da suke da buri. Saboda idan akwai so da kauna ana iya jure dukkan wani tsanani da jarrabawar rayuwa.
Duk da karancin shekaru irin na deeni shi da auren nan yakeso,bashi da wani dogon buri illa ya kara girma yayi dogon karatu da kudi,ya mallaki abin duniya kafin yayi aure,saboda a fadinsa rayuwar sa ba a hannunsa take ba ,bai so ta Allah ta kasance akansa batare da ya cika burinsa ba .
Haka nan ta bangaren farida ,tunda tayi wayo,ta girma tasan kanta ,to deeni shine abokinta ,kuma masoyinta ,bata sauraron wani namjij balle ta bashi fuskar soyayya. Asali ma dai tun kafin wani ya tunkareta labarin ta da shakuwar su da deeni zai riske shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Gata mace me kyau da tsari ,ga tarbiyya ,abin so da sha’awa ga kowanne namiji,sai daifa nan gani nan bari ,saboda ita jinta take tamtar matar deeni,bambancin ta da matar aure kadan ne a cewarta.saboda a tunaninta tsayawa ma ta yi magana da wani namiji tamkar tayi cin amana ne ga deeni …
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG