MISBAH CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI
Kwani tashi deeni ya tattara ya koma zaria,suka fara jarrabawa. Haka nan ra bangarwn farida ma suka fara jarrabawar kammala secondry,hakan yasa sukayi besa da juna . Haka nan yawan mu’amalar su ya ragu sabida karatu da kuma karancin lokaci,sai dai duk da haka rana bata fitowa ta fadi batarw da sunyi magana da juna ba na tsawon lokaci tare da mafarkin tsara rayuwarsu tare..
Deeni ya rigata gama jarrabawa dan haka ya tattaro ya dawo gida tare da shiri da tsare tsaren yadda aurensu zai kasance .yana karati sannan wani lokacin yana zuwa gidansu farida suna karatun tare ,,yana koya mata abinda bata gane ba . Haka nan yana matsawa mahaifiyarsa akan tafara yiwa mahaifinsa maganar auren sa da farida .
Takanyi murmushi tace karka damu mahaifinka zai yi kama komai ,,farin cikinka shine namu duka “
Hakan yasa hankalinsa kwanciya tare da alkawarin dagewa yayi duk abinda mahaifinsa yakeso,donya faranta masa ko da zaiyi abin da ransa bai so,don ya yadda farin cikin mahaifinsa shi ne samun nutsuwar sa da kwanciyar hanklainsa
* * **************
Farida !farida!!farida !!! Taji muryar kaninta na kwala mata kira.
Tana kwance kan gado rungume da hoton deeni,yayin da take magana dashi ta waya,kuma ko minti goma basuyi cikakke da rabuwa ba . Ba abinda ta tsana irin tana magana dashi a katse ta .
Ganin harar datayi masa yasa kanin nata me suna yusuf shima ya turo baki .
“Meye kikke hararata ? Ai nima Abba ne ya aiko ni in kiraki ,in ba zaki zo ba sai inje in fada masa kina waya baki da lokacin amsa kiransa;””
A’a’a ,zo yusuf,tsaya,yi hakuri bazan sake harararka ba ,kace masa ina zuwa””
Harararta yayi yace kinci sa”a da kinga sharri :”
Nan ya fice ,ita kuma ta mike da sauri ,ta bangarwn deeni a waya kuma yanata tsokanarta.
“Kicewa Abba kina biyayya wa mijinki ne ,kina faranta masa rai ,kina masa hira me dadi ,yana jin miryarki me dadi yana ratsa masa jikinsa,kina samun lada,””
“”Eh sosai zan fada masa,in yazo mun fada sai in tattaro har da kai ya hada-”
“Bakomai ya bata amsa”
“Ai dama dadi da wuya munyi alkawarin rabashi ni dake “
Tayk murmushi zan dauki wuyar ka dau dadin .
“A’a ni zan dauki wuyae ke ki dau dadin ” ni dai a’a . Ta fada xikin muryar shagwaba .
Kin gankk ko ? Kin fara kashemun jiki da shagwabar kin nan ko ? Yanzu tunaninki sai ya fitine ni ya hanani sakat “
Tayi daria , ai haka nake so ,tunani na ni kadai ya fitini zuciyarka “”
Farida !
Ta sake jin murtar mahaifiyarta ,da sauri ta katse wayar ta fita da gudu ,ta ce
Gani nan zuwa umma ,ina bayj ne .” To maza kiyi ki fito Abbanku nasan magana dake tun dazu ” to umma ”
Nan fa tayk falon nashi zuciyarta cike da tunanin kiran me yake mata haka?
Ganin sauran yayunta mata yasa gabanta faduwa ,dole akwai maganar da Abba zai mata .
Nan ta nemi guri ra zauna ta gaishe shi tare da fadin “Abba gani “
Ya kalleta yace naki ra yan uwanki nayi musu maganar aure ,kamar yadda kika san aladar gidan nan kuna gama sexondry nake auren ku . To Alhamdullilah ,lokaci yayj yan uwanki kowacce ta fada mun zabinta ,kuma nace su turo iyayensu ,sannan zanyi bincike in mun dai daita sai aure,don haka kema nakeso ki fadamun zabinki ,in baki dashi to sai ni in zabar miki .”
Kanta sunkuye zuciyarta taji tana harbawa ,ga Abba yasa mata ido alamar ita yake saurare . Bata dago kai ba ta ce .”Abba Deeni ne mukayi maganar aure dashi “”
Dama dai hakan ya zaci ji ,,sai dai saboda sanin su tare da kuma mahaifiyarta ta fada masa,sai dai yana son jin hakan daga bakinta . Ya gyara zama ya kalleta ya ce ” deeni dan gidan makwabcin mu ko ?”
Ta amsa da eh “
“Yace to kamar yadda na fadawa yan uwanki ,kema ki fada masa ya turo mahaifinsa inhar aurwnki zai yi da gaske ,yaro ne da aka haifeshi a ido na nasan iyayensa,nasan halayyar sa,don haka bani da bukatar bincike akansa illa maganar aure. Ku tashi kuje dama maganar kenn””
Nan suma mike duka suka fita.
Farida ta tsinci kanta cikin wani yanayi dabata taba shiga ba ,,ta rasa wani irin abu takeji a zuciyarta da jikinta ? Fargaba ne ? Farin ciki ne ? Doki ne ko tunanin aurwn ne ? Ta rasa me takeji ,sai dai tabbas jikinta ya mutu murus.
Jiki ba kwari ta dau waya ta latsa sunan deeni ta sa a kunne, sai dai wayar tayi ringing har ta gaji ba amsa.
A dai dai wannan lokacin deeni na zaune gaban mahaifinsa eansa bace yana masa fada saboda sake faduwa jarrabawar sa da yayi wannan karon . Ya jima baiga mahaifinshi cikin bacin rai haka ba,shi dai kansa sunkuye yana bashi hakuri,saboda shima baiji dadin hakan ba .
“” Baba kayo hakuri ,nayi iya kokarin iyakacin iyawata amma har yanzj Allah bai sa na kai ga masara ba “”
Wannan kake kira kokri ” baban ya fada a fusace.
” ai mai kokari ba ya gazawa,kar ka dauka zamu shirya muddin kana wasa da karatu,in har baka min yadda nakeso ba kar ka zata zan taba maka yadda kake so “”
Nan ya mike ya fita ya barshi a wurn .
Hankalinsa ya tashi matuka ,haka ran sa ya mummunan baci ,yaji wanj irinzuciya da bacin rai na taso masa. Rufe ido yayi yana addu’a saboda samun saukin abinda yakeji. .
Wai har yaushe za su dunga samun rashin fahimta da mahaifinsa ? Sam ya kasa fahimtar sa ;ya kasa ganin kokarinsa. Ya makale a aji biyu ya kasa gaba ya kasa baya ,tabbas in ya sake faduwa korar sa za’ayi.
Zuciyar sa da kwakwalwarsa suka cushe da tunani iri iri ,ya rase meke masa dadi .
Mahaifiyarsa ce ta shigo tana bashi baki da lallashi tarw da kalamai masu kwantar da hankali har ya samu zuciyarsa tayi sanyi kadan ,,sannan ya mata godia ya samu ya mike ya shiga ciki . A nan yaci karo da tarin kiran farida a wayarshi,bai bata lokaci ba ya kirata ta dauka cikin muryar shagwaba tace “
” nayi fushi “
“. Afuwan my dear “. Ya fada cikin mueyar lallashi.
“”. Deeni meke damunka naji muryarka kana cikin damuwa?
“Akwai farida ,yau ma kamar kullum ban sami nasara a jarrabawata ba ,banji dadi ba ,haka na batawa baba rai , dukkan wani tsammani na yanaga jarrabawata””
Murya kasa kasa tacw nina banji dadi ba deeni ,,wannan karon naji ciwon abun diue da kai da Baba ”
“”Farida kalamanki sun razana ni ,yau ce rana ta farko danaga kin nuna damuwarki akan rashin nasarata , na zata kin fahimce ni ,kinsan matsala ta na rashin fahimtar karatun da nake amma duk da haka ina dagiya don ganin na cimma burin baba da kuma burin kasancewarmu tare da ke “” na sani deeni ” ta bashi amsa .
Murya kasa kasa tace “kamun rashin fahimta nima,na nuna damuwata ne badan gazawarka ba ,sai dan son kasancewarmu tare ,tunda da bakin ka kace idan ka ci wannan jarrabawar babanku yayi alkwarin maka duk abinda ka nema ko kake bukata ,tabbas da ka samu nasara da yazo dai dai lokacin da muke da neman biyan bukata …….