MISBAH CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Dab da magriba Alh.Umar ,wato mahaifin deeni ya dawo daga office dinsa,kai tsaye ya wuce gudansu farida,ya samu mahaifinta a falon sa ,suka gaisa ,suka hau tattaunawa akan kasuwanci sannan matsalolin kasarmu da muke ciki na yau da kullum har aka kira magriba,sukayi alwala suka nufi masallaci tare.
Abinci da komai tare sukaci a gidan Alh. Ahmad,wato mahaifin farida. Suna nan tare har bayan isha’i,sukayi sallah suna hira har Alh. Umar ya yi masa maganar da ainihin ta kawoshi. Sun jima suna tattaunawa akan maganar wanda ya dauke su tsawon lokaci,har kusan karfe goma na dare ,sannan suka kai ga matsaya ,suka yanke hukunci, da alama kuwa dukkan su sun amnince da hukuncin da suka yanke.
Goma da rabj sukayi sallama ya nufi gida wanda ya yi dai dai da lokacin da su deeni suka dawo daga gombe.
Alhji yayi mamakin ganinsu a wannan lokacin.
” shamsu ,deeni, daga ina haka “?
Deeni bai saurareshi ba ya kama hanyar shiga cikin gida,ya daka masa tsaqa.
” Wai bada ku nake magana bane zaka kama hanya ka shiga ciki?
Bai saurare shi ba ya cigaba da tafiya,hakan yasa Alhaji shan gabansa ya ce,,,,
“” kai saurara ,gidana kake ,magana nake maka,wa zaka gwadawa danyen kai ? Me kake ji dashi ne ? Kana tsaye a gidan nawa………….””
Deeni ya katse shi ,ya ce, ” ina tsaye a gidan mahaifina ne ,bandmga kuma wanda ya isa ya hanani shuga gidan nahaifina ba ,randa na shiga gidan mahaifinka sai ka kore ni ;;””
“” Deeni !!! Shamsu ya daka masa tsawa .
“” Bakada hankaki ne ? Baban kake yiwa wannan maganar? Ban fa sanka da rashin da’ a da kadabi ba , meye ya haifae da wannan rashin da’ar ?
Mahaifin nasu ya kalle shi ,”dakata shamsu,kyale ni dashi ,” ya kalle deeni ya yi murmushi tare da shafa kansa ya ce ,
“” kayi gaskia dana ,nan gudan mahaifinka ne ,ba wanda ya isa ya hanaka shiga ko da kuwa mahaifin ne da kansa. Ina alfahari da hakan,da fatan kai ma zaka yi kokarin tsayawa kan kafafuwanka ka samu naka gidan na kanka ka ajiyeqa naka yaran yadda watarana zasuyi alfahari da cewa nan gidan ubansu ne ,don kuwa kai zan iya kyale k saboda kace nan gidan ubanka ne,kuma ba yadda na iya da kai tunda ni nakawo ka duniya. Amma kasani bazan bar dan ko yarka a gidana ba ,sabida kai ka kawosu duniya ,dan haka kayi kokarin nema musu muhalli kafin suzo,in ba haka ba karkayi kuka dani duj randa ba kori naka yaran a gidana na bar nawa dan,tunda gidan ubansa ne ..?
Nan deeni ya dinga jin zuciyarshi kamar wuta ,ransa bace ya shige ciki ba tare da ya sake tankawa ba . Ya fahimci sarai me mahaifin nasu ke nufi.
Alhajin ya bishi da ido yana masa daria ,zuciyarsa cike da tsananin kaunar sa. Sannan ya mai da hankalinsa kan shamsu,ya kalleshi yace .
” In shi yaro ne kai babba ne a kansa,ka dunga kula dashi kana bashi shawara me kyau,ka dai na biye masa. Karku manta ku ya’ya na ne ,ni mahaifinku ne “
Yana gama fadi ya juya ya yafi batare da ya saurari me zai ce ba ,nan shamsu ya wuce daki yana nazarin maganganun mahaifinsa tare da juya su a kwakwalwarsa.
Bayan fitar Alh. Umar daga daga gidansu farida bai jira sai da safe ba ya nufi bangaren su farida don yana da bukatar yin magana da ita a wannan daren. Ga mamakin sa kuwa ,da ya buga kofar bangarensu ita tazo ta bude masa kofa,ya lura tana cikin damuwa wanda shi ya hanata baccin ma.
Hannunta ya ja har zuwa falonshi ya zaunar da ita suna fuskantar juna ,idonta jawur ,fuskarta cike da tashin hankali. Tausayin ‘yarsa da kaunarta ya shige shi,tana cikin rudani a lokacin da take da shekaru masu rauni.
” farida “” ya kira sunanta.
Ta dago kai ta kalle shi.
Menene damuwarki ?=
Menene matsalarki ? Ni mahaifinki ne ,zan miki duk wani abu da kikeso a rayuwa muddin ba cutarwa ne a gareki ba “”
Hawaye ne kawai ya fara zubo mata,don haka ya kyaleta da maganar tambaya,ya ce ,,,,
“” share hawayenki,ki kwantar da hankalinki,ki kuma sani duk wani abu da zan miki ,ko wani hukunci da zan yanke akanki ba cutarwa ba ne a gareki.
Dazu mahaifin deeni yazo gidan nan,wato Alh umar,”
Kanta a sunkuye ,sai a lokacin ta dago kai ta kalleshi ,ya ce;;;
” ya dafa mun duk abinda ke faruwa,kinsan irin mutuncin da dangantaka me karfi da ke tsakaninmu ,duk da bamu da wata dangantaka ta jini sai nakwabtaka . Sai dai fa mun dauki wannan makwabtakar da matukar muhimmancin gaske fiye da komai,ko dan uwana na jini bamu da kusanci da su kamar Alh umar . Mun daukaki juna ,kuma mun rike juna da mutunci da amanar makwavtaka. Don haka mun yanke hukuncin daura auren yaranmu ,dansa da ke ‘yata ,ina fata ba zaki ban kunya ba ,za ki ban hadin kai ki min biyayya………….