MRS AMIDUD CHAPTER 4

MRS AMIDUD CHAPTER 4

Kafin yace wani abu, tuni ta rab’awa Jalal macijin nan a kafad’arshi, ta kuma ce mishi. “Kaii! Wayyo ga macijin a jikinka” A firgice ya juya kafad’arshi kawai yayi mugun gamo, aikuwa ya sake wayar shi me kirar LG, sai da ta ɓare gida biyu. Ya kuma buga ihu tare da watsar da key din motar. Ai kuwa ya fadi a sosai sai da yaji ciwo. Dariya tasaka sannan tace. “Kutt! Sai kace wanda aka sanya mihi maciji me rai duk ya tsorata”+ Duk da ran AMIDUD yan ɓaci amma bai hana shi dariya ba, musamman yadda Jalal ya birkicewa. Tana ganin AMIDUD ta falla a guje, tana kyakyatawa. “Sannu! Kaji wannan Yarinyar kai jama’a zan zaneta” “A’ah! Kyaleta, yarinta ke diban ta wata rana bazata yi ba.” Ya karkad’e jikin shi sannan yace. “Bro muje!” Duk yadda AMIDUD yaso yayi magana Jalal ya hana shi, sai ma shiru da yayi mishi. Tunda Mamie taga ta manno a guje ta fahimci ta lakato AMIDUD shine ta arto a guje. Tana shiga d’akin ta shige cikin cikin drowe. Koda ya shigo ya gama nimanta bata d’akin yaji haushi, haka ya kyaleta. Ya kuma kai kararta gurin Mamie. —– An sanya miki su cikin wata uku, dan haka suka fara shirin kai. Ranar da aka gama hada kayan su dake duk sayayyar a nan bauchi akayi tunda muna da manyan shaguna irinsu (Nasiru Bababa! Iron d’an gombe! Zubairu da Aminu! Lutaye brothers! Arabia super market! City store! Jifatu! Ga laushi da sauran shaguna, ina ga babu amfanin zuwa Kano ko Dubai 😎🤣) Parih bata gida aka kawo kayan tana makaranta, suna gama had’a kayan za a kai ta shigo tayi wurgi da jakar da basket ɗin, sannan ta zubawa kayan ido ta kalli Mamie tace. “Wannan fantimotin waye?!” Murmushi Mamie tayi sannan tace. “Wancan na Jalal ne! Wancan kuma na Yayan ku, za a kai gidan su Lamisah.” Sam bata ma fahimci me Mamie take cewa ba, kawai abinda ya biyo bayan, shine zuduma musu ihu da tayi ta fara wurgi da komai na falon itama sai an mata kayan aure. Gabaki d’aya ta tashi hankalin mutane, tayi birgima har ta godewa Allah. Shigowar AMIDUD bai wata wata ba ya dauke ta, sai dakin shi. Sai da ya kaita cikin d’akin shi sannan ya direta, ya kuma ciro bulala, had’iye kukan tayi ta koma can gefe. “Ke zo nan!” A hankali ta rarrafo inda yaƙe, kura mata ido yayi sannan yace. “Me aka miki kike kuka?!” Cuno baki tayi sannan tace. “Nima aure za a min!” Zaro ido yayi waje sannan yace. “Ke ban da jaka irinki waye kika tab’a ganin anyi mishi aure shekarunki nawa ne ma tukun?!” Kallon shi take kafin ta sunkuyar da kai kasa cikin murya me ban tausayi tace. “Goma sha biyu!” “Wawuya! Dakikiya! Banza sha-sha-sha mara kan gado keda zaki tsaya kiyi karatu kina tunanin irinta jahilai! Da wannan jakuntar zaki yi aure, sannan Uban waye zaki aura, kin ma tab’a kallon kanki a madubi! Sakarya idan kin fasa kuka a miki aure ke ba yar halak nace, ke har mace ce da zaki kira kanki a miki aure jeki jikin madubi ki ga kanki, wawuya” Hankad’ata yayi jikin madubi, tayi kamar zata fad’i rike jikin madubin tayi tana kallon warware gashinta wanda suka zubo har kafad’arta, waye ne yake zubo mata kuka na kara cin zuciyarta. Duk da rashin hankalinta tashan bakar magana saboda ita din renon tsohuwa ce, kuma wacce ta iya sarrafa harshe, ta kuma iya magana. D’aga hannunta tayi ta tattara gashin kanta, sannan ta share kwallar dake sauka a idanunta, d’ago kai tayi taga yana gutsira chocolat na roxy, a hankali ta isa gaban shi ta saka hannunta amsa, sannan ta juya ta fita, ta kuma juya ta sake mashi murmushi, tace. “Yau Ni kasa kuka! Sabida ka tsane Ni! Yadda na amshi wannan alewar Insha Allah sai kazo da kafarka gurin jaka! Dakikiya! Sakaryan nan! Niman alfarmata! Aure kuma Insha Allah na ajiye shi daga gobe zan fara karatu Ni dai wanda ya fasa. Ya rena kan shi.”4 Tana fita ta sake chocolat din ta juya zuwa can bayan gidan ta zauna ta fara kuka sosai, dan tunda take ba a taba zagin, irin wanda yayi mata dole ma take gurin Iya kaka, dan tana mugun kewar ta. …….. Tunda yayi mata gori iskancine ya ragu sosai, ko zaman falo bata yi abinda ya dame mutanen gidan kenan suka sata a gaba da tambaya karshe ta fashe da kuka, tace. “Ni kawai ku kaini gurin Iyata kawai dan ina jin kamar zan mutu idan ban ganta ba.” Shiru duk suka yi, har shi kansa sai da yaji ba dad’i. “Toh kiyi hakuri idan kuka yi hutu za a kai ki kinji ko” Inji Alhaji Muhmood, Gyad’a kai tayi, tana share kwalla, tashi tayi har ta kusan zuwa bakin kofar dakin su ta juya taga ita suke kallo, cikin muryan kuka tace. “Mamie! Ko kuna da hoton Mama na da Baba na!” Mikewa Jalal yayi duk iskancin da take mishi bai gani ba, yaje inda take ya dawo da ita, zaunar da ita yayi sannan ya fita can sai gashi hoton kato a hannun shi ya mika mata, duk sun yi kura, cire hular kanta tayi ta goge kurar. Ta kura musu ido kuka ne ya kwace mata.. “Nima da suna nan da babu wanda ya isa kirana jaka dakikiya!” Tashi tayi ta bar falon tana kuka, kowa juya ido yayi kan AMIDUD dan sun san tun shekaranjiya da tafiya da ita ta sauya baki daya, sai kuka ita da take kukan banza yau ta daina sai kukan takaici da b’acin rai. Tashi yayi ya bar falon, a hankali kowa ya watsa, Bin AMIDUD Mamie tayi ta same shi yana aiki a laptop din shi. “Nagode sosai da abinda ka aikata min! Ƙasa marainiya kuka har tana jin rashin iyayenta yasa ake wulakantata!” “A’a! Jal Parih da hankalinta abinda nayi kuma, babu kusakura a cikin sai ma taimakon da nayi muku! Ina gaya miki zaku ga canji”. “Wani can ji kuma? Me zaka gaya min wanda kariga da ka aikata! Wallahi baka min Adalci ba da kabar mana ita haka babu wanda aka haifa akan dai dai! Kowa yana kuskure amma ka zauna kaci zarafinta, Allah ya bamu yawan rai” Tana gama fad’ar haka ta juya tafita, daga dakin murmushi yayi kawai yace. “Bazaki gane ba Mamie na” Tun daga lokacin bai kuma sakata a ido ba, asalima ya daina ganinta. Abin ya bashi mamaki sau d’aya ya ganta tana shiga mota zata makaranta. Sati Daya da da mata gori, ta shigo gidan a gajiya daga islamiyya, ta kalli Jalal da yake zaune tace. ” Buroda! Pilisi gibi min yo wata” Shiru falon ya dauka sakamakon turancin Parih, murmushi tayi sannan tace. “Sitof lukat mi! An tak tu yu!”4 “Wow! Parih” turanci ne haka” Satar kallon Inda AMIDUD tayi sannan tace. “Eh kasan wasu suka niman raunin kane dan su cutar da kai kuma Allah yafi su kifi na ganinka me jakar koma! Babu wanda aka haife shi da iyawa! Dan haka daga yau karatu zan yi sai na haɗa ilimi akan halayyar mutane. Dan ina shirme bawai bansan me nake yi bane. Shiru falon yayi, sannan ta amshi ruwan hannun shi ta fita daga falon wuce dakin Mamie. Tun daga lokacin Parih ta maida hankalinta kan abinda take sai dai wani lokacin tana tab’a rigima musamman idan ta tuna gida anan ne ake yinta dan ta ringa kuka kenan.+ Abinci kuwa idan ba dumame ba bata cin komai da safe, ganin taki shiga hidimar kowa. Sai abin ya dame su dan har sun fara jin ba dad’i, suna hira a falo da Jalal ya shigo, kallon inda yake bata yi ba tace. “Mey buroda, lemi go tu mamie rum” Kunshe dariya Amidud yayi tare da komawa inda ta tashi ya zauna, yana kallon yadda ta tsuke fuska yana dariya. Barin falon tayi har tayi nisa tace. “Oho dai! Mummuna wanda kowa yafi shi kyau.” Zaro ido yayi yana mamaki kafin yace. “Yar kauyen dabji kawai” “Oho dai kaima can ne kauyenka! yu niba git eni bileje fas dabji” Mik’ewa yayi ta kara a guje. Duk yadda yaso daurewa sai da ya dara musamman yadda ta arta a guje. Dariya Jalal yake har da rike cikin shi, yana kallon AMIDUD yace. “Yaya ka kyale Parih in ba haka ba zatayi ta baka ciwon kai” Murmushin gefen baki yayi sannan ya cigaba da kallon kwallon da ake, yi. +++ Duk abinda aka sami shi rana tabbas yana zuwa, ranar talata gidan su Lamisah suka fara hidimar inda suka fara da wasu kanaun biki. Ranar juma’a suka yi walima baki daya, ranar Asaba aka daura auren Amiduddawlah tare da Lamisah, sai Abdul Jalal tare da Hansatu. Bikin ba laifi yayi kyau, ranar Lahadi aka yi wuni da bud’ar kai.1 Biki da sati Daya, aka bawa Parih basket takai musu abinci takaiwa Hansatu har suka yi hira da ita sannan ta dauki na gidan AMIDUD takai musu abinci tana zuwa bakin kofar taga shi da abokan shi. Turuss ta tsaya kafin ta karasa gurin su tana tafiya tana cin magana tana isa gurin su suna hira shi da Aashiq Ali da Aarzam tace. “Yaya pilisi a go koros yi hedi da baskit d’in” Dafe goshinsa yayi goshinsa yayi cike, baki cikin sabida Aashiq Ali da Aarzam suna tare da shi su kansu kwashewa sukayi da dariya turanci. Ita kam ko a jikinta, sai ma cogewa da tayi cikin fusata yace. “Zaki wuce ko sai na balla” “Pilisi gibi mi rodi zan wuce” Nace mishi, tsawa ya buga min sannan yace “ee Get out banziya kawai ansaki turancin dole ne” Murguda baki na nayi sannan nace. “Nu bodi fafet” Dariya suka saka tare da rike cikin su Aashiq Ali yace. “Ya Salam no body perfect” Gyad’a kai nayi ina murmusa mishi, Rike haɓɓa nayi sannan nace. Bat wai kuke foon fou mi” Rike baki Aarzam yayi, na kuma cewa. “Bi kos i sifiki ingilise beri wey” A fusace Ya Amidud ya Mike yayo kaina. Ana na watsar da abincin na shiga gidan ina hali, kallona Mamie tayi tace. “Yau ma kun kuma raba halin ba?!” Tura baki na nayi sannan nace. “Tunda akayi bikin shi yake jin haushi na sauka ce nice nasa shi auren tabarya da zanin” “Kul! Kar na kuma jin haka dan yayanku ne, jibi ma zasu tafi ku huta da masifar shi” Shigowa yayi muna kitchen dukkan mu muna taya su aiki tunda su Fahhamah sun koma makaranta. Hararar ta yayi sannan yace. “Mamie ki jawa Mahaukaciyar Nan kunne taje gaban abokaina sai tsinkani take” Dariya nayi sannan nace. “Wai sauka lafiya ruwa eat monki” Sake baki suka yi suna kallona, make keyata Mamie tayi tace. “Ke kam Allah ya shirya ki” “Amin” nace tare da fashewa da dariya sannan na fita. Ana gobe zasu tafi shine Maman Nibra suka zo, inda suka haɗu a d’akin mu ina sallah suna hirar su naji matar dan kwallon tana cewa. “Allah Sabriyah na kasa sabawa da Sex kullum abun kamar sabo nake ji shi yasa da zaran yazo min nake cewa bani da lafiya, shine yake cewa min idan nayi hakuri Mrs AMIDUDDAWLAH tana nan zuwa dan haka na daina mishi yanga da abinda yana dab da mallakar wani nan kusa lokaci yake jira, Sabriyah ina jin tsoron kar ya samu wacce zata fini juriya da hakuri ya manta da Ni da duniyata don Allah Kiyi wani abu kinji” Shiru Maman Nibras tayi sannan tace. “Ai kuwa hakuri zaki yi kina shan fruit, sannan kina kula da kan ki tunda kinga Allah yayi shi fitinanen ne a sex” Dama can nayi Sallama ina nad’e maganar sune kawai Sannan na ficce daga dakin na nufi dakin Mamie inda suke zaune nace. “Mamie meye ne Ses?!” “Ses?!! Kuma” Watsa hannu nayi nace. “Yanzun matar wancan take gayawa Maman Nibras wai yana hanata barci da ses kullum da.” Dauke wuta suka yi baki daya an rasa me magana. Sai shine ya daka min tsawa. “Ke dalla fita ki bamu guri, Sokuwa wawuya kawai.” Da sauri na fita daga d’akin ina tura baki, karshe dan kunya fita yayi Mamie bata sallame shi ba, yaje har dakin mu ya kira matar sa suka tafi daga nan ban san ya suka kare ba, Ni dai Mamie tayi min fada tace wai abinda na faɗa kisa yake dan haka koda wasa kar na kuma fa cike da tsoro na gyad’a kaina. +++ Ranar da zai tafi ina makaranta, duk sun rigani dawowa, Ni haka kawai dan bakin ciki ya sani a lesson. Koda na dawo nasamu ya tafi da matar shi murna a cikina kamar zan yi me gida ya rage daga Ni sai mu sauran yan gidan yanzun kuwa shiri muke da Jalal har da Hansatu. Wato Jalal da Hansatu kamar su cinye kansu dan masifa, dan sosai suka gurji amarci kam dan sai da aka hana mu zuwa shashinsu tunda naje naga suna wasan kwarzo abin ya dame Ni nazo na gayawa Mamie ta make min baƙi na, sai ban kuma Magana ba. Muna samun hutun na d’aga musu hankali sai sun kai Ni gurin Iyata, aikuwa aka fara shirya min kayana, tare da tsaraba kai har da abin kwadayin da ake samun na zuwa makaranta. Ranar Laraba Jalal da su Buhayyah suka raka Ni har cikin Dabji, yan garin mu suna gani na aka fara murna “ga Jan Parih ta dawo,” Murmushi nake dokawa kawai dan nasan nayi kewar Dabji. Muna isa kofar gida dan a keken shanu aka shigo damu, sai ga Iyata ta fito da gudu na dira, sai da Jalal ya riko ni. Tuni na isa gurin ta, na fad’a jikin ta tare da fashewa da kuka. “Iyata Alqur’ani na damu dake”+ Goge kwalla tayi sannan tace. “Parih na! Kullum dake nake kwana nake tashi sannu Y’ar nan” D’ago kai tayi sannan tace. “Ku shigo ciki barkan ku da zuwa.” Saukar min da kayana suka yi sannan suka shigo cikin gidan. Taburman kaba aka shimfida musu, shiga daki tayi ta dauko musu ruwa, ta ajiye musu a sabon kwashinta sannan ta kuma kawo musu kindirmo, ta ajiye musu. Ta kuma tura aka sayo sugar, aka zuba kafin wani lokaci, su jummalo sun cika gidan mu har dasu Aairah. Bayan su huta Jalal ya dube Ni kamar zai min kuka yace. “Baby Parih! Sai nazo daukar ki kinji” Dariya nayi sannan nace. “Toh ai wancan katuwar Matarka itace ke kiran ka baby, Ni kuwa ai ba baby bace.” Dakyar Jalal ya bar garin dabji dan ya wani narke min sai salo da fi’ili yake min. Bayan na kwanta a jikin Iya ina kallon fuskarta nace. “Mey Iya i mis yu” Kallona tayi sannan tace. “Me kika ce!” Dariya nayi sannan nace. “Ina kewarki!” ” Da wani Yaren?!” Dariya na kuma sakawa nace. “Da Yaren nasara” A firgice ta ture Ni daga jikinta tace. “Na shiga uku! Wato sai da Muhmood ya kai ki gurin shaidanun nan ko” Dariya nake kamar me yadda ta firgice sai kace na koyo wani masha’a, tashi nayi na bud’e inda aka zuba min kayan tsaraba ta, sannan na fita. Fita nayi da gudu ina cin chocolat din da na buɗe bakin shi. Can dandali na nufa, inda na sami su jummalo ana labarin irin kyan da nayi wai kamar bani ba. Ina zuwa suka zagaye Ni suna kallona kafin suka shiga jefa min tambayoyi. Nan na shiga basu labarin Birni nace jummalo. “Ef i taili yu, de hawus d’in da muke, ibi laki tangaran, gahi da fanfu, jummalo yo mu ba taliya muke kiran, sufa acan bini sofageti suke ce mihi: ” “Don Allah Parih toh ya sifagetin yake?!” “Hai-hai-hai! Sofagetin ake cewa ba sofageti ba” “Ai toh amma! Da baki nan Aairah taci amanarki ta kula Iroro.” Zaro ido nayi sannan sannan nace. “Jummalo. I suwai ef i kachi Aaira, i go fass a hedi” Zuba min ido tayi kamar ta fahimci abinda nake nufi sannan tace. “Me haka yake nufi?!” Dariya na saka cikin jin dad’i nace. “Nusent a dey tali yu, duk cikin bini nu bodi fass min ingilse” Kina wuta Jin yadda suka rud’e da ihu nayi murmushin jin dadi abinka da kauyawa. Ashe daga nan dandali anje an gayawa Iyata ai gani can Aljanun nasara sun shige Ni sai wani yare nake, Sai gata da kanta tazo komawa sani gida ina ganinta nace. “”Iya wata de firobilan!?” Kuka ta kuma sakawa tace. “Yanzun abinda Muhmood zai min kenan ya kaiki aljanun nasara sun shigeki Cikin gafara da nunawa miki bani kaunar tafiyarki amma kika kafe yar nima me kama da aljanun gaskiya.” Cike da jin haushin yadda take fada tana kiran sunan Baffana ya sani tura baki na nace. “Kaka Iya, waiti konse yu, she bi a de sifiki ingilise.” Kuka tasaka sosai. “Wayyo Allah na shiga uku, Ke Pari wannan mugun alkaba’in da kike fa, duk a zuwa binin kika koyo” tace min,.5 Tura baki nayi cikin kuka nace. “Kaka Iya iz but lai daya, babu aljanus a kaina, na oli Ingilishi” “Wayyo Allah na shiga uku meye kuma ledas Parih aljanun ashe ba d’aya bane har dasu ledas” “Iyah nifa bani da aljanun da kike fada.” Gyad’a kai tayi cikin jimami tace. “Hakkun! Baki da su ina ma zaki samu! Tunda sun miki mugun kamu aike sai gidan yar me ganye itace tafi dacewa da laluran ki” Kuka na saka mata nace mata lafiyata lau amma taki sai da suka je gurin yar me ganye suka yi ta zane min kafaffuna. “Kai dan tsugudi! Dan kaburburan! Lagwas maza ku ficce a jikinta.”3 Murmushin mugunta nayi sannan nace. “Weririri! Yasin bamu fita ai mun kai mu dari akanta, kuma sai mun karo wasu darin ke yar me ganye zaki daina borin karya ko sai na bankad’e miki ahirinki a garin! Sannan duk wanda yace Parih ta zauna a garin ga Alqur’ani sai mun haiyen mihi kafa da hannu mu kuma mai da mihi bakin hi keyar yi, sannan mu dauke ta zuwa sama jannati wato birnin almatsotsai! Inda fadar burburasa yake mulki, Keeee Iya kaka ki godewa Allah kin manyanta da yau sai mun saki murmuhi da hakori d’aya, kuma ef i silafi yu, yu go rimanba mi” Jinjina kai tayi cikin tashin hankali, alamar ta gamsu da Yaren karshe da na mata, cikin jimami tace. “Da alamu aljanun da suke jikin Yarinyar nan dirka dirkan ne, domin ita d’aya sai nishi take bari na tattara ta mu koma gida, tunda nan gurinki abun yaki.”+ Wani sowa na saka tare da mik’ewa nace. “Wififififi?!” Sannan na sauke ajiyer zuciya karya na kwanta warwas, ko nace hannu sakayau. Dakyar Iya kaka tattaro Ni muka nufi gida, muna tafi nake atishawa, ina zance. “Zanci namar kaza” “Muje yar naje y’ar nan! Aiko me kika ce zaki ci za a yanka miki” “Toron agwagwa zanci!” “Aiko d’an maraki kika ce zaki ci zan baki muje Allah ya baki lafiya.”3 Wato a cikin yan kwanaki da nayi a dabji naci kaji da agwagwa da zabi, sai zuma da nasha son raina.” Ina da kwana ashirin sai ga Jalal yazo, munsha yawo dashi da zai koma kamar dai ranar haka yayi ta min rigima Ni kuwa ina ta dariya har ya tafi. Spain…. Shigowa yayi a gajiye yana zub’ewa yayi a cushin. “Misah!!” Ya kirata, yadda ya fita hakan ya dawo ya same gidan sai a hankali, tattara komai na falon yayi sai gata tafito daga ita dai wata doguwar riga barci, mika tayi sannan tace. “Honey! Ka dawo?!” Girgiza kai yayi sannan yace. “A’ah tsirowa nayi! Kalli gidan nan har kunyar shigo da abokaina nake, Tsabar kazamta da son jiki wai duba ko ina da kome a watse sai da na tattara Haba don Allah” “Ayya! Honey, na gaji ne kuma ai kaine kake gajiyar dani shi yasa nake rama barcin jiya! Kuma batun gaskiya Ni ban iya aiki ba, sai dai ka nimo mana me aiki” Kamar ya rufeta da duka ya kalleta cizon lips din shi yayi sannan ya mik’e tare da tattara kayan shi ya shige dakin shi wanda kullum yake gyare, sosai yake bakin cikin lalacin Lamisah dan shi da farko ya zata ciki ne da ita, sai gashi ashe lafiyar ta lau. Tana ganin ya shiga daki itama ta koma d’akinta. Haka suke rayuwar su abin tausayi, dan kullum yana hanyar gidan abinci ko shi ya girka musu, gashi abinci a kasar Turai musamman namu na gargajiya masifar tsada ne dashi dan sai kaga dan mulmulen tuwo sai kaji kudin shi kamar zai kaika wani yanki na daban. +++ Ana gobe hutu na zai kare sai ga Dan wakilin hakimi yazo, zance gurina. Iya kaka kuwa sai murna take wai Jikar ta tasami mijin aure. Cab’a kwalliya nayi kamar zani gasar kyau Ina fitowa na tsaya. Cikin Mugun turancin kare dangi nace. “Barka da zuwa my suwetin hat, kasan weya tugeda” Gyad’a min kai yayi cikin jin dadi ya samu yar binni mana ya washe haƙora yace. “Hmm! Me kika ce?!” Gyad’a kai nayi sannan nace. “Amma Haladu ance min kana zuwa binnin kuma ai kanajin turanci” D’aga min hannu yayi kamar wanda aka kama yayi laifin yace. “Dan datse, ko yas da go bani ji” A tsorace na zaro idanu nace. “Alqur’ani! Bani soyayya da kai sai ka koye Yes da go” Na juya mishi baya ina murguda mishi baki, kamar wani sauna haka yayita rokona sannan nace. “Kaga Ni yanzun makaranta nake bani aure yanzun sai nayi ilimi nima na rama wulakancin da aka min.” Cike da bakin cikin yace.. “Amma baki ga Aairah an kai baiko ba.” Tsaki naja tare da shigewa nace. “Kwarankwatsa! Allah sai ya saka min taci amanata.” Karshe haka na barshi a waje cike da bakin ciki, dan wallahi ko kashe ni, za ayi bazan tab’a yarda na aure yi auren cin amana ba. Ina shiga dakin Iyah na fasa mata kuka, ina gaya mata abinda ke faruwa dani itama dake ta iya taya b’era barna tace. “Barni da yar banza me kama da Banu ƙasa-ƙasa”(😂🤣💁🏻‍♂️ ji wani zagi wai banu ƙasa-ƙasa)1 Sosai nasha kuka, tun a daren Iyah ta had’a min tsaraba da zan kai bauchi, manshanu, zuma, kwai, da daddawa, bankono, citta, garin dakka na geron kunnu, sai kukar miya, garin kub’ewa. Sai zabuwa da kaji uku, sai soyayye nama wanda ta zuba mishi yajin me dad’i. Wanda aka had’a da adinar mota,. Sosai aka hada min tsaraba. Da dare ina barci ya kama kafata ta kunsa min lalle har da hannu, washi gari da safe bayan nayi sallar asuba na sameta a madafi, ina zuwa ta mika min miya a ludayi nasha ina yatsina fuska, sannan na tashi na shiga wanka, ina gamawa Jalal na shigowa gidan, dariya na mishi sannan nace. “Wannan uwar sammakon! Ko ana ka kwana ne?!” Girgiza kai yayi sannan ya gaida Iyah bashi kujera nayi ya zauna, sannan na dauki kunnu gwab’el na ajiye a gaban shi wanda akayi da dafaffiyar madarar saniya sai kindirmo saboda yayi kamshi ga kamshin kanunfari da citta da yake tashi. Ajiye mishi nayi a gaba, sannan na amshi nawa na, kosen da aka sayo min na ajiye mishi. Saka ludayi duba yayi ya fara sha, lumshe idanunshi yayi sannan ya bude akaina kafin yace. “So sweetest” Washe baki nayi da jin sabon kalmar turanci wato. *Son suwetie” Gyad’a kai nayi nace “Hmm! Ya matar ka? Kuma Yasu Mamie na da Aunty” “Kin hanani sakat shi yasa nazo na maidaki gida da kaina na”1 Zaro ido nayi sannan nace. “Ta ina na hanaka sakat ga tulaliya Matarka Ni babu ruwa na kar ka ja min bugu” “Kai Jalalu, zan baka aika ka kaiwa Muhmood ka gaya mishi a nimawa Parih magani domin magirkan ifiritai ne bisa kanta ai ranar da kuka zo an sha artabu, dan ma Allah yayi Ni da kashi d’aya, sai da nayi ta buga su da kasa kafin suka tafi.” Sake baki nayi ina kallon yadda Iyah ke gundura zance, sake baki nayi ina kallon ta, cike da mamaki har da nuna min ita din jar wuya ce….. Ko ya zata kaya 😂

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE