MRS AMIDUD CHAPTER 5
MRS AMIDUD CHAPTER 5
Zura mata ido nayi ina kifkifitawa, shi kuma ya tsaya sai kallonta yake, gyad’a kai nayi sannan nace. “Hmmmm!” Juyawa tayi muka kalli juna, yadda muka zubawa juna ido yasata jan bakin tayi gum tayi shiru, murmushi nayi sannan nace. “Bari naje na nimo masu keken shanu! Su fitar mana da kayan mu” Ajiye ludayi dumar yayi sannan ya mike tare da goge bakin shi yace. “Muje!” Kallon kwanun shan nayi, sannan na buɗe ba zan yi magana yace. “Muje nima naga gari,”+ “Toh mun fita” nace mata, Mun fita tare mun sami masu kuran amma ya hanamu dawowa dan yawo muka yi ta yi a saman kuran, har na gaji nace mishi. “Mu tafi rana tana yi” “Ko kin gaji dani ne?!” “A’ah kawai na fison mu isa gida da wuri ne!” “Hmm” yace min, muna isa ya sauka sannan yasaka hannu zai sauko Ni na dauje sannan na diro daga keken, muka shiga cikin gidan muka kwaso kayan mu, zuwan d’an gidan wakilin hakimi ya sani zuwa gurin shi nace. “Toh Ni dai zan tafi a rike min amana kuma duk wanda yaci amana ta, bashi karewa kalau” Washe haƙora yayi sannan yace.. “Ai bazaki tab’a kamani da laifi ba, i Lobi yu” Dariya nayi sosai sannan na kauda kaina nace. “Meye kuma i Lobi yu?!” Caraf a kunne Jalal birki yayi a gaban mu sannan yace. “A ina kika ji kalmar?!” Nuna mishi d’an wakilin hakimi nayi sannan nace. “Samari na ne shi” Hararar ya kwad’a min sannan ya juya gurin haruna yace.. “Kar na kuma ganinka! In ba haka ba zan kai ka bauchi a daure min kai, ke kuma wuce mu karasa kwaso kayan wato har soyayya kika fara, daga zuwa hutu. Sai na gaya wa Ya AMIDUD ya dawo daga kasar da yake yazo ya zane min ke tunda baki tsorona, kinsan me yake nufi da kalmar cewa yayi zaki mutu” Dafe kirjina nayi ina zaro ido sannan nace. “Na gata kaina bani kuma barin wani ya gaya min” Muna gama kwaso kayan naje jikin Iyata na saka mata kuka nace. “Iyah a dey mis yu!” Cikin tausayawa jikarta, dan tasan ta had’u da iftila’in rayuwa, yatsina fuska tayi sannan tace. “Allah ya kawo miki karshen wannan iftila’in da ya shiga rayuwarki, amma akwai matsala” Haka muka bar garin cike da kewar juna, ina share kwalla na har muka bar garin. Hannun shi naji akan nawa, d’ago kai nayi ina kallon shi, janye hannunsa yayi, tare da shafa kan shi. Har muka isa gurin motarshi, aka zuba kayan har cikin motar, tunda ya buɗe min gaban motar na zauna, shima ya shiga ya tadda motar sannan ya mikawa me keken kuɗin shi, kafin ya tadda motar, ya janyo hannuna ya daura kan motar, yana tuki da ita. Zaro ido nayi kafin nace. “Raba ni da Y’ar akurkura” Sake hannuna yayi sannan ya lakuce min hancina, kafin yace. “Ina kaunarki!” Ya fad’a a hankali, dariya nayi sannan nace. “Nima haka, amma me haka ke nufi?!” “Bazaki gane ba sai nan gaba idan kin kusan gama school!” Gyad’a kai nayi sannan nace, “Kana da kirki! Kuma kafin wancan mummuna kyau!” Ware idanun yayi sannan yace. “Ya AMIDUD! Sai na gaya mishi” Dafe hannun shi nayi cikin sanyin jiki nace. “Kayi hakuri! Bani kumawa.” “Shi kenan!” Komawa nayi na cigaba surutu tare da bashi labarin abinda ya faru dariya yake, har muka iso darazo anan naga doya da kwai nace sai na ci. Ya kuma saya min, Karfe biyar muka iso dan koda muka iso bai kai Ni gida ba, sky crown ya kai Ni muka sha kankara me dad’i. Dakyar ya kama hanyar gida duk sai ya diririce, yace. “Parih! Karki gayawa kowa mun zo nan kinji, kuma karki gaya musu na” Sai yayi shiru kamar zai fashe da kuka. “Ai bazan gayawa kowa ba, indai kullum zaka na kawo Ni shikenan babu wanda zai ji abinda ke faruwa kaji.” Lakuce min hanci yayi sannan yace. “Ni zan dinga kai ki makaranta ina dauko ki, sai muna zuwa musha abin dad’i” Gyad’a kai nayi sannan muka cigaba da tafiya, har muka iso gida da murna su Amrozia da Buhayyah tare da Aarib….. Muna shiga gidan Aunty Amarya tace min. “Kaza kanki da motsi kin dawo!” Juyawa nayi na kalli Jalal ashe ya fita, tura baki nayi nace. “Babu abinda ya dame ki dani! Tunda ba gurinki nake ba” Make min baƙi tayi na rike gurin, tare da fashewa da kuka, na bar falon na nufi d’akin Mamie! Kallona tayi dan na bar su Buhayyah suna kwaso min kayana. “A ina kuka tsaya?!” Niman kukan nayi na rasa, domin kuwa ban yi tsammanin tambaya daga gareta ba sai da ta kuma buga min tsawa, wanda ya sani fashe mata da kuka nace. “Ai shine ya kaini yawo muka ci kayan dad’i”+ Ban tab’a ganin b’acin ranta ba sai yau fad’a take kamar zata doke ni, sai da ta min tass sannan ta tura aka kira shi tayi mishi fad’a sosai. Tsabar kuka shiga d’aki nayi na kwanta, ban tashi ba sai kiran sallah, na tuna tun a wunti yayi Sallah sannan yace. “Idan muka koma sai Kiyi a gida” Shine na tadda faɗar Mamie, har abinci rana fushi nayi baki ci, da dare ma kin fita nayi, ina kwance har Mamie ta gaji ta kawo min abinci nace na koshi. Kallon Aarib tayi sannan tace. “Kai dauko min wayar charge nan naji da wannan me kunnen kashin.” Da sauri na tashi ina tura baki nace.. “Wannan tulelen mugu ne! Toh na tashi!” Haka ta sani cin abinci har sai da na fara yunkurin amai, sannan ta hakura, ta kuma kara da min nasiha sosai sannan ta shafa kaina. Kafin ta futa a dakin. +++ Bayan dawowata da kwana uku muka koma makaranta, duk yadda Jalal yaso mu shirya naki domin a cikin nasihan da Mamie tace min. “Idan kika bari maza suna rike ki, mutuwa zaki yi kuma, Ni da baffanki babu ruwan mu dake, dan haka babu ruwan ki da Jalal.”1 Tun ta tsorata Ni kuma, gani da shegen tsoron mutuwa, ya sani gudun shi, da ya dame Ni kuwa na sanya mishi kuka, dan dole ya kyaleni. +++ Bayan shekara uku Lokacin mu yana tafiya, fiye da tafiyar hawainiya. Rayuwar mu karewa take kamar yadda ake karar da ruwan a cikin mazubi, kwanci tashi asarar me rai, dan har na shiga aji d’ayan Secondry, abubuwan sai a hankali domin bawani canji sai na alamun girman da nayi dan yanzun na cika shekaru sha biyar, kuma amadadin nutsuwa sai na kuma haɗuwa da shaidanun kawaye, masu masifar rashin ji, da wasan banza.3 Wani abinda yake d’aga hankalin Mamie yadda muke wasan banzan da muke da Jalal, wanda tayi fad’a har ta gaji. Ban san yadda zan fada muku irin girman da nayi ba, dake ina samun kulawa da cima me kyau, nayi wani irin cika ne daga sama har kasa zuwa sama, wani lokacin kuma ina makaranta zai je lokacin break, idan na shiga motar, wasan banza zai ta min har sai na gaji nace mishi wallahi sai na gayawa Mamie. Yau na dawo a gajiye, ina taku kamar bazan yi tafiya ba, ina shiga motar nan. “Malam Nura! Ya aiki” “Lafiya! Parih ya karatu” Kwanciyata nayi dan cikina na ciwo, kallon fuskana nayi na sake murmushi, na janyo jakata na ciro karfen hujin hancin da Sa’imah Garu ta saya min na sakala, sai wani button da ake sakawa a kasar baki ko saman baki, mannewa nayi sannan na saka na hancin na, sai wani wanda Faseelah tace min. A jikin cibiya ake sakawa.(🙄 Anya Parih kawayenki nan yan arziki ne! Wannan ai duk yan iska ne) Murmushin jin dadi nake sakewa har muka isa gida, muna shiga naga wata dalleliyar mota, Ni kaina motar ta hauka Ni, sauka nayi ina kallon motar har na shiga cikin gidan, dake yau kafin na tafi makarantar sai da Mamie ta rankwshi ni, na fita da kuka. Akan wani sakon da ta gani a jakar makarantar ta samu sakon Faseelah, ban san me sakon yake kunshe ba ta mare Ni har da rankwshi. Tana min fatan shirya. Koda na shiga falon kauda kaina nayi ban kalli kowa ba, ina jin muryan mutane a falon amma naki ce musu komai. “Kee zo nan!” Gabana ne ya fadi nace.. “Wayyo Allah na! Yaushe wannan mutumin ya dawo.” Juyawa nayi cikin jin haushi nace. “Xkuzimi! Sannan nayi wuccewa ta, ina jin muryan Aunty Amarya tana cewa. “Wallahi Yarinyar nan ta lalace! Dubi Hancinta fa! Sai kace yar iska duk idanunta ya buɗe bata tsoron kowa sai Mamienku” Shiru tayi yana girmama girman da nayi, sai kace wacce ake bata abincin kaji yarinya ta haɓɓaka haka. “Durling tunanin! Tunanin me kake yi” murmushi yayi yace. “Honey! Babu komai ina mamakin yadda yarinyar ta girma ne” “Hmm! Baka jin abinda Aunty take fada ne maybe akwai me matseta ne, dan naga tafi su Buhayyah girma! Gaskiya Daddy ya aurar da ita, ko kuma taja muku abin kunya dan idanunta ya rigada ya buɗe.” Nan ita da Aunty Amarya suka yita zuga shi. Ni kuwa ina gama cire kayana, na saka wani boom short na jeans sai yar shirt me hannun vest na fito abuna, dan kayan da Jalal yake sayi min Ni da matar shi, na wuce su nake kitchen na zubo dan wake, da manja sai gurji da tumatur na zuba yaji, nazo gaban su na zauna na fara ci a hankali. ……. Tafiya ya fara miƙewa ina ganin na kusan dakatarwa sabida Azumin da ya tunkaro mu Ganin yadda nasaka su a gaba ina cin dan wake yasa shi, daure fuska tam sannan yace. “Ki tashi kije ki saka kayan ko kuma ba zane ki babu abinda ya dame ni” “Duka!!” Nace har sau biyu, mik’ewa yayi tare da zare belt din wandon shi, mik’ewa nayi da sauri na bar falon, ina buga kafaffuna a kasa, ina shiga daki nayi kwanciyata dan ko hannu ban wanke ba nace. “Ji min d’an jaraba daga dawowa zai fara takura mutum” Ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba, sai dai naji ana jan kafana, ga wani sanyi da nake ji yana shiga ta kafana, buɗe ido nayi nagan ni a wani lambu me kyau, sai kamshi gurin yake. Ga kayan ciye ciye, an zuba a wasu kwandon azurfa, sake jan kafana akayi na kalli inda ake jan kafar, ware idanuna nayi ina son nayi magana bakina yayi nauyi, kura musu ido nayi cikin farin ciki, zuwa suka yi kowane su ya zauna kusadani. Shafa kaina tayi tace. “Jal Parih! Me yasa kike kuntattawa iyayen rikonki! Ta hanyar abinda bai dace ba! Ko baki son muma musami salama ne! Kin manta damu ko guzirin baki riko mana! Kinga Uwar rikonki na kuka saboda halin da kike ciki” Ta nuna min Mamie na share kwalla, riko hannuna yayi sannan yace. “Ki daina azabtar da zuciyar da ta ginu da kaunarki! Kinji muna muna miki fatan Alkhairi” Gani nayi suna matsawa a hankali, sai lokacin na samu damar bude bakina nace.. “Mamana! Abbana!” A firgice na farka, naga Jalal yana ƙoƙarin saka hannunshi a cikin rigana, kura mishi ido nayi sannan nayi maza na rike hannunsa, dan duk wasan banzan da muke bani barin shi ya tab’a min kirjina, har gwara Faseelah. Takan tab’a tace. “Wai! Parih kinfi mu wallahi” B’ata rai yayi sannan yace. “Ki bari mana kullum nazo tab’awa sai ki hanani, kice akwai lokaci, toh ga shi Ya AMIDUD yazo kuma nasan zai sa miki ido dan yanzun Mama take gaya min! Kuma muna da partyn Abokina kisan yadda kika yi ki fito” Kwace hannun shi yayi sannan ya fita, tare da sake murmushin mugunta, yace. “Kamar yadda kika lalata min komai na nima sai na lalata miki baki gobe! Kinsan an had’ani da macen da bana so sai dai na more jikinta! Kika ja min mahaukaci ya min dukar mutuwa kice zan kaunace ki?! Sannan kika ja min na ji ciwo ta hanyar daura min macijin roba! Hmm Yau Insha Allah zan gama komai kuma ki bar gidan nan! Rashin kunyar da kikewa mahaifiyata ya kusan karewa! Kawayen da kike tare dasu ni na turosu rayuwarki” Ya ficce a gidan tare da sake murmushin farin ciki, wannan shine burin Jalal kenan ya tarwatsa rayuwar Parih, kamar yadda tasa aka aura mishi, Hansatu. Wasu jaka na gani a inda ya tashi, sannan na mike tare da gyara zaman rigana, na zazzage kayan naga kananun kayana, tsaki nayi na wurga gefe. “Nusent kawai! Ko Uwar me zai yi da tab’a min kirjina, mi Nu go fil tak nusent” Ni daya na tayita masifa, kamar yana gurin, tashi nayi nayo wanka. Sannan nazo na kwanta akan idan lokacin tafiya yayi sai na fita. Karfe sha biyu saura na farka, naji gidan tsit, dan haka nasa kayana na fito, babu kowa. A hankali na murda kofar fita a gidan na fita daga falo, da sauri na fita na same shi yana jirana a bakin get,muna zuwa ya mikawa baba dubu biyu, sannan muka fita. Kallon shi nayi sannan muka shiga motar shi da take wajen, yace. “Yau zaki bani damar na tab’a ko ina!” “Hmmm! Mamie zata min duka” “Ban ciki da iskanci! Sauka min a mota ko na baki mamaki” “Ai ba sai ka min wulakancin zan san ka dauko Ni ba, sauke Ni nima na koma gida” Zaro ido yayi waje cikin jin haushi yace.. “Karki min rashin kunya!” Ni kuwa na murguda bakina nace na nawa kuma” Make min bakina yayi, naji zafi sannan nace. “Allah ya isa min!” Dan har yanzun bakina bai mutu ba, kuma bashi zai hana idan da Mamie zata titsiye Ni na faɗa mata gaskiya abinda muke dashi ba. “Ni kikawa Allah ya isa?!” “Eh anyi maka sai me?!” “Yau zan ga karshen rashin kunyarki” “Ka jima baka ga karshen ba, mugu kawai” Haushi ne ya kama shi yayi gangara gefen hanya tare da fincikoni, Ni kuwa Allah ya bani Sa’a na kwad’a mishi mari,, abinda ya kuma fusata shi kenan Yasaka hannun shi ya yaga min rigar jikina, wanda ya bayyana bra din da nasaka, a tsorace na kai mishi cizo, kafin ya dawo daga zafin na balle kofar zan fita, ya janyo Ni na kuwa kwala kara tare da fincike jikina na aruntuma a guje. . fitowa yayi cikin d’aga murya yace. “Ki dawo na kai ki gida! Dan wallahi kika kuskura na kamaki zan miki wulakancin da baki tab’a tsammani ba” Jin haka ya kuma jefa Ni cikin tsoro, ban san inda nake jefa kafana ba, kawai dai abinda na sani ina gudun ceton raina, kuma insha Allah sai na tsira daga nufin Jalal. Gashi dama riga da skirt na saka a jikina iya cinyata, kuka na fashe da shi ina gudu ban masan ta inda zan fara ceton kaina ba, karfina ne ya kare gashi na gaji, kawai na tsaya kawai har ya kusan cimma Ni, sai ji nayi an fisgoni tare da toshe min baki, hawaye ne ya zubo min sakamakon ban san waye ya janyo ni ba, haɗuwar jikinmu ya bada wani irin spark wanda yasa muka d’ago kai kallon juna muka yi, ban san lokacin da na fashe da kuka ba ina ƙoƙarin kwace kaina…… Kuka nake son nayi sabida tsananin tsoro yasani sake fitsari a jikina, ga uban rawan da nake Ni bana sanyi ba, A’a na bala’in tsoron Ya Amiduddawlah, wanda yake shake da bakina, yana kallon cikin idanuna. Yana ganin Jalal ya wuce. “Lallai kin rika! Kice labarin da ake bani ba karya bane da gaske ne! Kin zama karamar karuwa! Shine bari ki lalata mana sunan gidan, wallahi kin cuci iyayena! Wallahi nayi da nasanin da Uncle Abtisham da Aunty Amatul Islam suka haife ki,tir da halinki kazamar yar iska mara kunya.”+ Shiru nayi sabida ban isa na mishi rashin kunya ba, haka Jalal ya gama sintirin shi bai ganni ba yaja motar shi ya koma, ture Ni yayi sannan ya tsinka min Mari har uku, kuma ya hanani kuka, cire rigar jikin shi yayi sannan ya wurga min yace. “Wannan rigar ko da kudi aka hada Ni dashi bani kuma sakawa! Haka wacce babu komai akanta sai tsageranci.” Kuka nake sosai saboda irin zagin da yake min bazan iya dauka ba, wucewa yayi na bi bayan shi. Motar shi ya buɗe sabuwar dana gani yau, ya tab’a wani guri boot ya buɗe, sannan ya nuna min Boot din yace. “Allah yayi min tsari na dauki karuwa a cikin motata, sai dai ki shiga bayan motar” Kallon shi nayi wasu kwalla masu zafi suka sauko min. “Ya Amidud don Allah ka barni na shiga cikin motar sit mana.” kiciniyar cire belt din shi yake nayi saurin shigewa cikin Boot din na kwanta tare da fashewa da kuka, yana zuwa dan mugunta ya buga motar da mugun karfi, sannan ya koma yaja motar da mugun gudu, dan rashin Imani haka yayi ta gudun ganganci, har ya isa gidan sannan yaje yayi parking. Yana fita ya nufi gurin Baba me gadi, ya mika mishi hannu sannan yace. “Nagode 🤝 sosai, baba ka rike amanar da na baka sannan ka nuna kai dattijon Kwarai ne, Allah ya fadawa zuri’arka.” “Ba komai ai yiwa kaine! Gashi kuɗin da yake bani tsawon shekara guda ban tab’a ci ba, sabida mahaifinka bai rage Ni da komai ba” “A’ah kabar shi hakkinka ne Allah ya cire maka a jikin shi, kaci abinka nagode!” “Ba komai! Alhaji karami, ina mutuniyar take?!” Nuna mishi bayan mota yayi sannan suka iso, ya buɗe Ni. Tsili tsili nayi da idanuna, riko kunne na yayi sannan ya fidda Ni daga cikin boot d’in muka nufi, cikin gidan shi yana magana kasa kasa, muna shiga falon shi ya tunkude Ni, faduwa nayi na fashe da kuka, har ya juya zai nufi dakin shi. Sai yaji ina ai ina cikin jin dadi ne tunda ga fanka Nan na juyawa, dauka na yayi ya kaini kitchen ɗin su ya wullani sannan ya rufe da key yayi tafiyar shi. Washi gari da asuba ban san shigowar shi ba, sai da naji ya watsa min ruwan sanyi tare da cewa. “Maza ki nufi cikin gida, ki duba store kizo kiyi mana abin karyawa ko na miki dukar tsiya wallahi babu wanda ya isa ya min magana! Karuwa kawai.” Kamar maciji haka nazo na wuce shi, na nufi cikin gidan na kwaso duk abinda yace. “Tsayawa nayi ina kuka! Dan ban san me zan dafa musu ba, kuma sun koma barci” Tattara kayan nayi na zuba a tunkuyar nayi tafiyata, cikin gida dakin Mamie na wuce dan tana sama gurin daddy, sannan nayi kwanciyata bayan nacire kayan jikina, na daura towel nayi kwanciyata. Barcin da banyi jita cikin salama ba itace nake yinta yau, sosai na sake nake barci. …… Ashe Jalal ya ganni, kawai ina ciki da Barci yazo ida nufin shi, lokacin kuma Ya AMIDUD yazo tafiya dani. A ka’idar gidan wacce take da miji ba ita ke girki ba sai abokiyar zamanta, dan haka ganin Mamie tana sama, kawai Jalal ya burma dakin Mamie sabida ya leka d’akina bana ciki, shine bari yazo yayi watandar shi son ran shi. Sai gashi akan idanun Ya AMIDUD, shima leka d’akina yayi yaga bani ciki, a masifance ya nufi dakin Mamie, inda ya sami Jalal ɗin yana kokarin janye towel daga jikina, rike hannunsa Ya AMIDUD yayi sai da yaji kashin hannun yayi kara, sannan ya kifa mishi mari wanda ya sashi sake ihun, da ya farka dani. A tsorace na tashi zan zauna yayi wani kwallo da Jalal, sai da ya isa bakin kofa, cikin hargagi yace. “Wallahi kika sake na dawo kanki baki suturta kanki ba, sai na miki abinda bazaki manta dani ba” Da sauri na sauka a gadon na wucce ban daki na saka key jikina na rawa, sosai dambe ya kacame a tsakanin Jalal da Ya AMIDUD, na rasa me zanyi rigar Buhayyah da na gani a nan dakin Mamie na saka na fito, lokacin Aunty Amarya, tana ƙoƙarin rabasu, sai dukar Jalal yake, yana fad’in. “Duk lalata mata rayuwa da kayi bai isheka ba! Amma kana gani akan idanun ka akayi komai dan bakin masifa kana cigaba da bibiyarta! Dan abu kazanka wawa jaki saba!” “Toh ka sake shi Indai akan Parih ce ba zai kuma tab’a ba, ka kyale shi Amiduddawlah nace.” Sake shi yayi lokacin na fito daga dakin. Cikin b’acin rai yace. “Wuce muje, zaki gaya min me kike nima a jikin namiji, da kika lalata Kuruciyar ki, bazama guri daya yasa kika lalace ba muje, Next zamu koma London dake.” “Wayyo Allah na! Wallahi bani zuwa ko ina! Idan sai na bika ne gwara na mutu kowa ya huta” Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace.. “Hmm! Yar so! Yar dangi tace bazata bika ba, ku nime mai nima taimako ki bashi ita ku bar zargin Jalal ne zai b’ata muku ita, Yarinya ba, sau nawa tana fitar dare yawon banzata sai shine zai lalata muku ita.” Zaro ido nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba. 🙄