MRS AMIDUD CHAPTER 6

MRS AMIDUD CHAPTER 6

Ban tab’a ganin abinda ya girgiza Ni kamar abinda Aunty Amarya da Jalal suke fad’a, cikin d’aga murya, da kwakwazo wanda yaja hankalinsu Mamie, suka sauko daga sama. Kuka ma ashe rahama ce, dan gani dai amma babu kukan ya dauke, saukowa Mamie tayi take tambaya abinda ke faruwa, Aunty Amarya ta nuna mata ni, sannan ta fara magana da cewa. “Wai Amidud ne yake zargin Jalal! Wanda suke uba d’aya zai lalata wancan sakaryan wacce ta gama yawonta cikin dare!” Murmushi Mamie tayi sannan tace. “Allah ya shirya mana su, wuce d’aki” “A’a! Mamie ta wuce muje kawai,” Haka na koma bayan ta ina kuka nace. “Mamie!” Matsawa tayi cikin nuna bata damu ba tace. “Ka dauketa!” Barin falon tayi, na juya zan Kamota ya, sai gani na nayi ina yawo, a sama kafin na fahimci meke faruwa ya ficce dani daga gidan, kuka nake da ihu nake da iya karfina, amma babu wanda ya kawo min agaji haka ya kai Ni har dakin shi, ya dangwala ni a kasa. Sannan ya shure ni tare da tsirta min yawun shi, gogewa nayi ina kuka.+ “Wallahi na kuma ganin kin fita a gidan nan sai na karyaki, kowa yayi miki mugun shaida, shi ya koya miki amma gashi Mahaifiyarshi ta nuna bata san da haka ba, na kara ganinki a inda yake, makarantar tunda can ma kina da kananun karuwan da suke bud’a miki ido” Yana gama gaya min me zafi yayi ficewar shi, Kuka nayi shi har na godewa Allah. Ina zaune sai gashi yazo. “Tashi ki wucce ki dafa mana abinda zamu karya dan matana tasa ba cin abinci karfe biyu.” Jikina na rawa haka na mik’e na rab’a gefenshi na fita, ina shiga kitchen ɗin, dakyar na gama abin karyawan, ina gamawa ya shigo kitchen ɗin ya duba abincin, d’aga hannun shi kamar zai mare Ni, yace. “Lusara kawai! Dubi jagwalgwalon da kika mana ko waye zai ci kayan amai idan mata ta tace bazata ci, Ni dake ne a gidan nan.” Komawa gefe nayi, kamar zan shige cikin bangon tsabar tsoron shi, ba karya ina jin tsoron Ya Amidud saboda fuskarshi babu alamar wasa, kullum a take yake. Kwashe abincin nayi naje na jera musu, ina gamawa yana shigo min da Kayana, watsa min yayi a tsakar dakin. Sannan yaje ina jin shi cikin wata nauyayyen turanci me mugun shakuwa, wanka nayi na saka wata karamar gown ta ankara, iyakarta gwiwata, sai wando slim jeans, baki nasaka yar karamar gyale na, na fito zuwa falon. Kitchen na nuna na dauko abincina, nazo na wuce abuna. “Honey! Meye ya kawo aljanar yarinyar nan cikin gidan nan!” “Hmm! Gwarama Kiyi hakuri domin kuwa tare zamu koma London Arsenal!” Wani irin kallon tayi mishi shima kuma ya tsuke fuska, irin babu wasa a Maganar shi. Ture abincin tayi sannan ta mike zata bar falon, kallonta yayi sannan ya kauda kai yace. “Ki zauna ko kuma na sab’a miki” Kuka tasaka mishi, tare da cewa. “Wallahi bazan zauna da karuwa ba, dub’eta fa. Yarinyar karama sai karuwanci har tasan tayi wanka ta dauki kwalliya har haka.” “Ke wani shegen ne ya hanaki tashi kiyi?!” “Kana nufin har wannan jagwalgwalon itace tai?!” “Da kika gama cinye dadin zaki yi tunanin itace tayi ko ba ita bace!” Sannan ya kaiwa bakin shi luma, tare da lumshe idanun shi yana cinye dad’i, na rigasu gama cin abincin na fito. Ina ganin yadda suke diban Gara, dariya nayi nace. “Ashe dai karuwa ta iya haɗa Gara” D’ago kai yayi, tare da watsa min wani irin kallon, tare da nuna min kitchen. Wucewa nayi bakina kanin kafana, naje na fara wanke filet dina, shigowa tayi tare da fisgo ni cikin masifa tace. “Wallahi zaki bar gidan nan!” Cikin iskancin da na koya a makaranta nace. “Kika ce!” “Ubanki nace” Zaro ido nayi nace. “Yanzun dubeki kamar tabarya da zani shine zaki zagar min iyaye, abu ko fasali wata salaf salaf dake” “Kan kutumar bala’i! Ni kika zaga?” Ta nuna kanta. Dariya na saka sannan na juya mata baya ina tafiyar agwagwa, nace. “Can da yawarki” Sannan na wuce dakina, ina dariya, ihu ta shiga kurmawa. Tana zagina dake yana ban daki, kafin ya fito yazo kofar d’akina tayita dukar kofar tana zagina da karuwa. Har da ce min. “Mijina yafi karfin yar kauye haka karuwa!” Ta window na leko tare da cewa. “Idan mijinki ya same Ni mata! Haba ai Kawayena since sai yafi kowa sa’a dan ina da kayan aiki, dan haka mijinki ko a tire ake kasa shi bani daukar shi Ni Parih sai Mr Handsome!” Dukar kofar tayi, nace. “Oho dai bulogari kawai.” “Sai naci kaniyarki idan kika fito.” “Oho dai idan baku nime Ni dan komai ba kodan kwasar Gara wa tumbinayenku, mijin ki ma zai nime abinda zai tada komaɗar da yayi” “Wallahi zai na miki duka” ” Hhhhh! Matar Ya Amidud wallahi ko mafarki kika yi kin dake Ni, da safe kina tana tashi kiyi sadaka, maganin masifa” Haka ta biye min nayita manna mata hauka har ya fito. “Meye haka! Lamisah kin biyewa Parih kunata hauka a cikin gida kaman wasu yara” “Karuwar ce nake biyewa Wllhy sai ta bar min gida, dan ban fahimci zamanta a gidan nan ba, yarinya baliga kuma wacce akwai aure a tsakanin ku! Wallahi bazan yarda ba sai ta bar gidan nan” “Aiko sai da ki mutu! Amma gidan Ya AMIDUD, kamar gidana ne, kuma na zo kenan bani fita” “Ina wasa dake? Ko dake muke magana?! Akwai sa’anki a cikin mu ne?! Wallahi kika Kure Ni sai na karya miki mukamiki” Kamar ruwa ya cinye Ni haka nayi shiru, ina zan iya hayagagar, shi yasa naja makatar bakina nayi shiru, tunda bani da hujjar magana kuma tsoron shi nake ji kar ya shigo ya min bid’ibid’i,. “Honey! Kace tafi min daga gida” “Babu inda zata fa!” Ya bata amsa…… Daga gobe ne?!🤣😂😎🙄 Yana gaya mata haka ya tawo bakin kofa na ya buga, buɗewa nayi sannan na sunkuyar da kaina kamar mutuniyar arziki. “Wallahi na dawo naji labarin kin mata rashin kunya sai na zaneki! Kuma karfe uku ki shiga ki mana abincin rana” Tura baki nayi gaba, cikin kunkuni nace. “Ita matar gidan zaman me take da bazata girka maku abinci ba sai!” “Keee! Zagina kike?!” Zaro ido nayi tare da yin rau-rau da idanuna nace. “Ni ban zageka ba” Tsaki yayi tare da barin kofar dakin nace. “Allah zai yaga min baƙi ne a hana Ni magana” Cak ya tsaya Alqur’an garke kofar nayi tare, da sauke ajiyar zuciya. Ina cewa, ” Mutum sai kyan tsiya! Mtseew ko burge Ni bayi ba, kawai kayan shi ne yayi min kyau”3 Dafe kirjina nayi lokacin da matar shi ta shiga buga min kofar cikin tsokana nace. “Doguwa da hankali dace ne! Me zan miki” “Ubanki kika zaga!” Sai dai window naje sannan nace. “Eh naji Ubana ya gode! A wuce a yi girki idan arusa ya dawo ya loda a tumbiyeyen shi dan yau boyiboyinku bazata dafa ba!” “Kan Uba!” “Coman Gara way! Yau sai dai yunwa ta karku dan bazan girka muku ba, ai Mijinki ne ki shiga ki zuba mishi esfirianki ki!” Dukar kofar tayi cikin wani irin zagi. Nace “oho” Gyara kwanciyata nayi na fara barci, cikin jin dadin sam na manta zan shiga na mishi girki. Sai can da naji ana kiran sallah na tashi, sannan na wucce nayi wanka saboda bani da tsarki, ina fitowa naji yana cewa. ” Zaki buɗe ko sai na karyaki idan na bude.” Tura baki nayi naje na bude, shaf na manta towel ne a jikina, zaro ido matar sa tayi, to Ni ina ruwana, rankwshi kaina yayi na fasa kuka tare da rike towel ɗin da yake shirin faduwa a jikina, turani dakin yayi sannan ya shigo, tare da banke kofar. Tsaro yasani shigewa ban daki da gudu, ina shiga na rufe gam ina kuka. “Wato ban isa ince kiyi abu ba shine kika kwanta, wallahi na kirga goma baki fito ba, sai na biyo ki har ban dakin.” “Toh naji kayi hakuri ka daina dukana, idan kana min haƙa zan dinga jin haushinka” Tsaki yayi ya ficce tare da buga kofar fitowa nayi na dauki riga da skirt na saka na lace na fito ko dan kwali ban daura ba, na sake gashin a bayana na wuce kitchen ashe kayan abinci ya sayo wanda zasu yi amfani dashi na kwanaki kafin su koma, cus-cus na. Dauka dauki kayan lambu na wanke, dukda bani da kintsi (🤣😎 idan kaci ka mugu ko mara kirki dole sai ka zambaci kanka) Mamie bata barmu haka ba, sai da ta koya mana sarafa abinci na gargajiya da na zamani, jollop ɗin cus-cus din nayi da kayan lambu, sannan na duba naga d’anye kifi na ice zama nayi na wanke dan naji Mamie tana cewa shi mutum ne me son kifi musamman na ice. Wanke kifin nayi da lemon tsami, na cire mishi karnin sannan na markad’a kayan miya kamar jajjage, na zuba akan kifin zuba mai a tunkuya na yanyanka albasa suka shiga soyuwa, rage wutar gas din nayi. Na fito duba kayana nayi babu wayata, tsaki nayi sannan na koma ciki kitchen na zuba kayan miyar na ci-gaba da soyawa har yayi min sannan na tsayar da ruwan miyar sannan na zuba kifin na fasa mishi maggi da gishiri, sannan na fito, ganin shi nayi yana zaune, kauda kai nayi dan gidan ya kaure da kamshin girkin. Ganin na nufi kofar fita, yace min. “Ke!” Juyawa nayi ina raba idanu. “Uwar me zaki fita yi” Tab’e baki nayi sannan nace. “Zanje amso zobo ne da kayan kamshi” “Dame dame?!” Tura baki nayi sannan nace. “Ni nasan abinda nake bukata!” “Toh koma ba zaki fita ba!” “Toh! Da zobo da tiara sai sigar!” ” Na sayo sugar yana cikin kwali” “Toh sai citta da kanunfari!” “Hmm! Suke nan” “Wayata!” Sannan na juya zuwa kitchen ɗin, bayan kaman minti goma sai ga Buhayyah, rungume juna muka yi sannan na matsa mata ta shiga daga zobon, Ni kuma ina kwashe abincin! Na zuba a warme biyu, sai miyar kifin. Sannan na koma yanka ganye salat, na hada na zuba a wani ƙaramin bowl. STORY CONTINUES BELOW  Ina gamawa na fitar da abincin dinning sannan na koma muka cigaba da aikin zobon, inda Buhayyah ta kankara cumcumba, ta zuba a ciki sannan na markade kankana da abarba,(🙄🤨 toh Yan gayu masu daura mana abinci a Ramadan ga dai salon zobo juice) Juye kankanar da abarban nayi muka zuba sugar, sannan na kara tiara kafin ba fasa kankara ba juye a ciki saboda yayi sanyi kuma, kankaran ya rage zak’in sugar. Sannan muka nufi waje da zobon sannan na diba mana Ni da Buhayyah muka je dakina muka ci, bayan mun yi hira ta mika min wayata, sannan nace mata. “Akwai abincin Mamie shine na cream kular nan, sai zob’onta ki kai mata,” Shiru nayi kaina a sunkuye nace. “Buhay ina kewar Mahaifiyata! Hatta Mamie itama ina kewarta, gashi an ajiye Ni sai girka musu abinci nake suna ci ba godiya sai kirana karuwa kawai” Rike hannuna tayi sannan tace.. “Kiyi hakuri! Kuma zan gayawa Mamie cin zalinki da ake, tun ai yasan matar sa bata iya girki ba ke da…” “Toh munafukai! Wallahi naji magana nan a kunnen Mamie sai na zane ku! Munafukai kawai, zoki wuce ko na karya miki kafa” ya daka mata tsawa, Jikinta na rawa ta fita Ni kuma ya karaso ya kama kunne na, sai da ya d’agani kan kafaffuna, na saka mishi kuka. Ya make bakin. “Ki min shiru! Kuma naji kin dauki wata magana daga nan kin kai wani waje sai na cire kunnenki, komai kika ga ya faru ki b’oye dan ba ayi ciki dan abinci ba har da b’oye wasu abun, kuma da kike cewa an kiraki da karuwa! Baki yi bane a ina na tsinto ki jiya kina gudu.” Shiru nayi ina goge kwallar dake sauka daga idanuna. Tun da ya fita na zauna shiru kamar da gaske, ina gurin. Hira naji a falon na fita, Aunty Sabriyah ce, cikin fara’a naje kusada ita ta b’ata rai tare da cewa. “Karki fara zuwa inda muke! Tunda lalata mana sunan gida zaki yi, yar iska kawai har da kulawa Jalal sharri ki hada shi da D’an uwan shi.” Dariya ta bani sannan na d’aga kafad’ana nace. “Ko a dan kiya! Tank God ba a taba kamani ina iskanci da wani ba, aka min auren dole shi kuwa nice naga suna lalacewar su, na kuma tona mishi asirin shi, kuma bukekiya kin wani zo kina hura hanci zan b’ata muku sunan gida, tambayi Daddy akwai kasona a cikin gidan domin wannan barin da Ya Amidud yake zaune barin iyayena ne, ke me nogo fi take nonsense ehhe! Girman burodi tashin laja🤷🏻‍♀️” Wucewa nayi ina kada musu yan kananun ɗuwais dina in nuna musu, ko a jikina an tsakuri kakkausa, Ina shiga na dibo abinci sai gats tibi tibi, kamar kaza me dauke da kwai wai zata dake Ni,. Baya naka nace. “Kambuuuu! Kingan ki kuwa, wata tibi tibi dake, kina tafiya kamar ana turaki a keken shanu, kinga go an sitdown na gaya miki bani da time dinki yanzun harkall zan yi da cikina, kuma ko Ya Amidud ne dole ya d’aga min kafa, kafin yayi jarabar shi” Don Allah meye illar abinda na fada aikuwa suka saka salati, tare da cewa. “Shegiya kin sabawa mutane sharri shine ya fado kan mutumin kirki! Allah ya isa tsakanin mu dake shegiya munafuka” Kuka Matar shi ta saka tare da komawa daki ta dauko wayar ta, ta shiga kiran shi. Yazo maza gida ba laifi. Wallahi shi a tunanin shi Jalal ne ya kuma zuwa min, sai gashi dan yana can wunti, kamar mahaukaci aka ya dawo gidan, ina zaune ina duban abincina suka shigo d’akin. “Ke maimaita abinda kika fad’a,” Dariya nayi sannan nace. “Haba sai kace karamar mace! Am a big gal! Bana mai-maita abinda ya wuce wannan sai dan achaba” Tsaki yayi dan yana bayan su, wai nan sun kawo shi yaji sharrin da na mishi wai dan nace Jaraba(🤣🙄😂🤭 Parih ai sun fassara miki kalmar jarabar ce ta hannun hagu ke kuma Kalmar fada kike nufi😂🤣) Dariya nayi na kalli Sabriyah nace. “Bijima!” A fusace ta juyo, cikin dariyar da nake b’oyewa nace. “Kalli yadda kike hura hanci kamar balama” fashewa nayi da dariya sannan na nuna Matar Amidud nace. “Wasutura waalaika! Sungulu hamama yar shilar gwangwani, shaf na sha’afa da kawar uwata” Aikuwa a fusace suka yi kaina, zasu buge Ni na kurma Ihu, yana waya sai da ya jefar da wayar ya zo d’akin, ganin yadda suke sauke numfashi, aikuwa na fashe da kuka nace. “Wallahi yau dole muje gaban Baffana! Kawai ya mai dani gurin Iyata, tunda kowa karuwa yake kirana, dan nace Ni ba karuwa bace sai su shine zasu dake Ni, wato ba dad’i kuke kirana da karuwa!” Wani irin kallo ya musu, takaici da bakin ciki ya hanasu magana sai juyawa suka yi, zasu fita k’asa-k’asa nace. “Riba uku inji sauro! Na cijeka ka Mari kanka, na maka kuka kuma a kunne” “Honey kana jin yarinyar nan ko?!” Ta faɗa kamar zata saka kuka, juyowa yayi ya kalle ni, nutsuwa nayi tare da matse kwalla. Suna fita ya juyo a fusace, kamar zai dake ni, na koma mishi fuskar tausayi, sak na koma mishi fuskar Kawun shi, tsaki yayi sannan ya fita, aikuwa na fasa dariya nace. “Ariya kurkure!” Yana fita ya saka su a gaba da fada, cikin jin haushi Sabriyah tace. “Ya AMIDUD! Wallahi zaginmu tayi kuma kaima ta maka sharri” Daga safiyar yau zuwa yanzun karfe huɗu yayi danasanin yafi kwando dubu domin daga Lamisah zuwa Parih sun kusan fasa mishi kai da, fadar su. Parih yadda ya fahimce ta Allah ya daura mata tsokana da kuma tsoro uwa uba rashin jin magana. Mik’ewa yayi sannan yace.. “Don Allah ku kyaleta bata da hankali” Dakin dunya wuce dan ya gaji da jin korafin su, Indai Parih ce ba barin su zatayi ba, wai a haka shine take tsoro. Ban san lokacin da suka bar gidan ba, dan nikan Candy crush na cigaba da yi har barci yayi gaba dani. Shigowa yayi ya tashe Ni, kallon yadda na tsuke bakina, had’iye yawu yayi dan Irin bakin da yake so kenan a jikin mace, dan karami, wanda zai ji dadin cinyewan da tushe amma ban da wasu dalilai ai da zai tabbatar da kanshi amma ina yana kyamar mace me mu’amala da wasu kartin. Zuwa yayi ya sami cinyata ya zuba min duka sai da na gantsara kirjina, tare da cuna mishi baki. A hankali nace. “Allah Sarki Ni mareniya!” Jan skirt dina nayi fararen cinyoyina suka bayyana, cikin kuka nace.. “Duba fa! Yadda hannunka ya fito sabida dukar da kai min gaskiya ka tsane ni, kawai kalla fa Don Allah shafa kaji yadda wajen ke zafi!” “Zaki fito ko sai na b’allaki” “Ai yadda kuke ɓalle juya a filin kwallo shine zaka b’alla ni! Toh me kuma zan muku! Nayi ku kirani da karuw” Make min bakina yayi, zafin da naji ya hanani karasa maganar. “Uuu! Fasa min baƙi zaki yi na godewa Allah! Da ka tsane ni! Nufa bani fushi” “Kaniyarki! Tashi kije ki daura mana abincin dare, kuma bani cin abinci me nauyi ko kuma ki had’a min har da wani juice, kuma kika kuskura kika tsokani mata na sai na sakata tazane min ke” Tashi nayi zaune, ina cewa.. “Mindinkil tsinke a tsuliyar kuturu” “Wuce muje!” Haka na sauke skirt dina nayi, ina mita. Koda na nufi kitchen din. Na same shi kaca kaca, kamar zan fashe da kuka, na juya zan fita muka yi karo dashi sai lokacin na lura falon anyi aiki a cikin shi. Tsuke fuska yayi sannan ya nuna min kitchen ɗin, na koma na gyara kitchen nayi wanda na sha wahala kafin na gama na daura shinkafa da miyar hanta sai pepper meat, da coslow. Ina gamawa ana kiran sallar magariba, lokacin manyan mata suka shigo. Sun zo diban gara, komawa nayi daki na turawa Buhay sako yazo min da Tsamiya da tazo ta amshi abinci ta kaiwa Mamie. Share musu falon nayi najera abincin. Shigowar Buhay Sabriyah ta harareta, mika min tayi muka wuce dakin. Wanke tsamiyar nayi na daura tare da citta da kanunfari, na koma gefe muna hira, jera mata abincin nayi na ajiye mata nace. “Baki dawo mana kayan d’azun ba.” Ruwan tsimi yana dafuwa na juye sannan na tacce. Bayan na kara ruwan sanyi wannan na, kuma zuba mishi kayan kamshin na zuba mishi tiara na tamarind na zuba sugar kadan, sannan nace mata. “Tab’a kiji yayi kinsan Mamie ta hanani shan zak’i”3 “Zio! Allah yayi zuba mana namu nayi gaba kafin Ya Amidud yazo ya fara min korototo” Zuba mata nayi sannan muka fidda tsimin naje na ajiye musu, suna zaune su uku sai hirar suke, muka wuce dan na rantse sai na fita, kafin ya sami damar magana nayi Wuf….. 😂🤣Nayi Wuf da makarantar Parih! Fatan Alkhairi gare ku matan quarts! Zaurena! KURUCIYAR JAN PARIH fans! My Wattpad Fans!Aunty Safarah! Mom Haneefa da Haneef! MJ comments 1,2, sai wanda ban san iya adadin miliyoyin masoya wanda suka yi dafifin d’agani duniya ta san dani! Bazanyi toya na manta Albasa ba. Aminaina My Zahrah da UmNass Allah yasa da Alkhairin 🌹😘😊 Ummu ilham! Mommyna. Ai kuwa na fecce a saba’in ko kyalina baka gani. “Parih!!!” Buhayyah ta kwala min kira, kan Uba tuni na cikawa bujena iska. Mik’ewa yayi jikin shi na tsuma, dan yasan sarai zamu iya haɗuwa da Jalal. Ai da sauri ya fice Lamisah tana ce mishi. “Honey! Ina zaka dan ance maka gantalalliyar can tafita…” Ai shima ko ta kanta bai bi ba, kallon Sabriyah tayi ƙamar zata fashe da kuka, tace. “Kin gani ko! Kamar ba matar shi ba, haka yake muzanta min.” “Hmm! Nayi mamakin da Mamie tace min zaku tafi da aljanar can! Amma ba damuwa kici Ubanta idan tayi miki Iskanci tunda fita zai nayi ya barku a gidan.”+ …… Haka suka yita zagina,1 Cikin ikon Allah na samu na shige gidan garin shiga muka yi karo da wani wanda ban san waye ba, kuma ba Jalal ba. Ware idanu nayi cikin jin haushi nace. “Ji min mutum ka bangaje ni kuma baka bani hakuri ba.” Na tura mishi bakina. “Ai bangaje ki nayi ko?” Ya tambaye ni, Cikin gatsali nace. “Hawa kaina kayi! Luk i No go fi tak nunsent, abeg give mi road meka fass!” Dafe goshi Buhayyah tayi, cikin jin ba dad’i tace. “Kaicona! Ke kam! Da alamun ana asarar kudin tara ne! Wannan jakin turancin baki ya ishe mutum zuwa lahira da kafar shi ba sai an kai shi ba, ai ga Ya AMIDUD. Don Allah Ya Najmuddawlah kayi hakuri!” Ware ido nayi cikin dariya na nuna shi nace. “Kai Amma wannan sunar taka da tsayin jaraba! Kai harufa nawa kenan! Kuttt.” Juyawar da zanyi aikuwa sai A kan fuskar Ya AMIDUD. Ban san lokacin da na bazama a guje ba nayi cikin gida, shima ya rufa min baya. “Wayyo Allah na! Na shigangadina Wayyo Allah na! Mamie ki cece Ni wallahi zagina suke” Jin irin ihun da nake, yasa Mamie tafito da sauri. Bayanta naje na buya ina haki. Leken shi nayi, shi ko halin bayayi amma dan niman magana nace mishi. ” Jimana dan kwallon! Shi kai baka hali ne? Yoh ina kaci ka koshi balle ka tara tsokokin Alqur’anin ko yar kumatai nan baka dasu! Wai tsaya kana nufin tun.” “Keyi min shiru bani son shashanci, wuce kibi shi.” Inji Mamie, Rau-rau nayi da idanuna, nace. “Mamie nasa an kawo miki abinci ko iri. Afirishetin baki min ba na abincin yana dadi ko baya dad’i” Kallon Buhayyah tayi sannan ta kalli Ya Amidud tace. “Ban fahimci me take cewa ba! Kuna nufin abincin Parih ne bata Lamisah ba?” “Kutt! Inji wani munahikin ne yace bani ke girkawa ba, ita wancan tabaryan da zanin me ta sani banda Ni na girka kuma su hadu su cinye. Sannan su kirani da karuwa Alqur’an bani komawa gidan can” Shafa gashin kan shi yayi cikin damuwa, tare da narke fuskar shi wa Mamie yace. “Kiyi hakuri! Mamie amma” “Wuce ka bar min gida ke kuma wuce daki.”1 Zaro Ido yayi waje, kamar zasu fado kasa, girgiza kai yayi sannan yace. “Amma Mamie baki tunanin cikin dare wancan Yaron zai kuma biyota, tunda haka ne shi kenan. Tayi zamanta sai da safe” Ya juya zai fita kallona yayi na murguda mishi baki, bai kula Ni ba yayi tafiyar shi, har ya kusan isa Palourn mamie tace. “Zoka tafi da ita! Ku dai ji tsoron Allah a zaman da zaku yi karka manta amanarka ce ita.” “Wayyo Allah na! Wallahi bani binshi kofa da takashi, Alqur’an wahala suke bani, Wayyo Allah Baffana.” Na riketa gam. Zuwa yayi ya riko hannuna ya fitar dani daga gidan, aikuwa na fara mishi, bori ina botsarewa.1 Cikin rashin sani hannun shi ya kai kan kirjina, aikuwa ya tab’o biredi mai laushi. “Wayyo Allah na! Ka tab’a min nan dina!”1 Da sauri ya d’aga hannun shi yana me jin kunyar kallona, haka muka isa gidan. Tulatulan mata sun saka abinci a gaba, suna ci. Wucewa yayi dani dakina, ya ture Ni. Sannan ya fita abinshi, Hannun da ya tab’a burodina yake ta kumshe shi, cike da jin wani irin abu a jikin shi. Kallon Lamisah yayi cikin nutsuwa. Sam bai tab’a lura da yanayinta ba sai da yau ya tab’o gidan laushi. Zama yayi yaki amfani da hannun wani irin kunya da yarrr yake ji. (Lolz! Ya Amidud an tab’o kayan laushi mana 🤣😎)1 Ban san ya suka kare ba, amma na daina jin motsin su a falon. Washi gari, kin fitowa nayi na gyara kwanciyata, dake banci komai ba jiya na kwanta, yunwa kuwa ta shiga cin ubana, dole na tashi na shiga wanka ina fitowa naga tara na safe, tsaki nayi sannan na fito kitchen daga Ni sai towel dan ban zata sun tashi ba, dake nayi wankar har na wanke kaina.1 Da sauri na shiga kitchen ɗin, naje na hada tea kenan, nafito aikuwa muka yi karo da mutum, tsoro ne yasa kofin hannuna faduwa. Naja da baya ina raba idanuna, kallona yayi daga sama har kasa, ga ruwa na diga akan shi, Yasaka towel a wuya. Nima kuma gashina a jiye, a dalilin karin da muka yi ya kai hannun shi k’ugu na, ya rike Ni. Nima tsoron kar na fadi na saka hannu na biyu na riko towel ɗin wuyar shi. Wannan tsayuwar da muka yi, ashe akan idanun ja’irar matar shi. Ai kuwa ta sake wata ƙatuwar salati. Wanda ya saka ya AMIDUD ya sake da ƙasa. Cike da jin haushi nace. “Wayyo Allah na! Yu bireki mey k’ugus! Yi wanto kili mi, ko? Bikos yu hiti min! Filis tak mi bak two Mamie, i kan’t tak dis ani mo!” Kura min ido yayi cikin baƙin ciki, wato shekaru hudu bai sanya na nutsu nayi karatu ba, sai wani azzalumi turancin da nake zane shi da ita. Matar shi ta dawo dashi daga duniyar da ya tafi na takaicin da na kulla mishi. Yo ko a jikina an tsakuri kakkausa. “Honey! Meye zan gani? Ba dai wani abu bane Yarinyar nan ta maka ba?!” Kutt nice ma zanwa mijinta wani abu. Mik’ewa nayi ina rike k’ugu na, daukar kofina nayi naje na zaga bayanta, kasa kasa nace mata. “Wasan kwarzo muka gama dashi, kuma ya tab’a ni sosai kema kice yayi miki irin abinda yayi min in ba haka ba, wallahi yasha dake. Mijinki ya iya wasan kwarzo.” “Zanci Kutumar Ubanki!” Ta ruga min Ashariya!. Juyawa nayi naga ya dafe goshinsa, cikin kankanuwar murya nace. “Ayya! Anti kyakyawa zagi bakyau! Idan ka zagi iyayen su naka ne ka zaga, kuma Ni bazan so na ganki a cikin jahannama kina miko min hannu ba, kin ga ki daina. Ba kyau Ya AMIDUD ma bai ji dadin ba kin zagi kawun shi,” Nasan yaji mu, sake narke muryan nayi nace. “Kuma iyayena ne fa, suna can a makwancinsu kika zage su. Ba damuwa! God dey se ebiritin.” “Ke!” Ya buga min tsawa, a firgice na juya. Sannan nace. “Auuu! Wacce tayi zagi baka fasa mata janareton kunnenta ba sai Ni yar mareniyar Allah bani da Fada da modah shine kake son bireki mai kunne wai Ya Amidud woh yor on i kili, kayi hitin dina haka?!”3 🤣🤣🤣👌🏻 WHO your on i kill! Kunsan bamu da ilmin English! Ya Allah ka albarkaci Rayuwar mu da iliman nafi’a! “Honey!! Kaji abinda wannan saryan take gaya maka!” “Dalla ki min shiru, ke kuma na Kuma jin kinyi wancan jahilin turancin sai na kareraya kafarki na zubawa karanuka su cinye, b’ace ki bani guri.” Tura mishi baki nayi, ina kunkuni. Har na kai bakin kofa, na juya tare da cewa. “Ebirbodi foo give mi! Bikos i mek ol up yu hangiri!”+ D’ago kai yayi, ya kalle ni jinjina kai yayi sannan ya zare towel ɗin wuyar shi. Cikin fusata yace, “Bari na nuna miki ina fushi!” Nufo Ni yayi aikuwa na shige d’akina da mugun gudu. Tare da rufe kofa garammmm! Juyawa yayi bai kalli inda Matar shi take ba, yayi wucewar shi dakin su. Dan Iya jin haushi yaji kuma yayi imani ba laifin parih bane na Lamisah ce. Ganin yadda ya yanke fuska ya sata jin ba dad’i, bin shi dakin shi tayi ta same shi yana cire kaya zai shiga wanka. A hankali ta isa gaban shi, muryanta na rawa tace. “Honey! Kayi hakuri. Allah ina tsoron haduwarku da Yarinyar ce, ina jin zafinta sosai gani nake kamar zata dauke min kai ne!” Dakatar da ita yayi cikin Fushi sosai. “Kamar ya zata dauke ni?! kinga nayi kama da Yaro ne da zata dauke ni?!, wani iri dauke ni zata yi?!” Rike hannunsa tayi, cikin tashin hankali. Hawaye na zuba daga idanunta tace. “Allah! Zata iya mace ce! Kuma Kanwar kace! Baya ga haka akwai aure a tsakanin ku. AMIDUD. Wallahi nasan ko baka sota dan kyau da halittar jikinta ba, zata dauketa ta hanyar amfani da girkinta. Ni dai don Allah karka kawo min ita a matsayin matar ka, dan mutuwa zan yi. Idan ban mutu ba! Zan shiga wani halin rayuwa. Don Allah.”8 Jikin shi ne yayi mugun sanyi, riƙe hannunta yayi cikin na shi. Tsabar yadda yaga tana kuka har jikinta na rawa, zaunar da ita yayi a bakin gado yayi, yana murza yatsunta, bai hanata kuka ba. Ji yayi zuciyarshi ta gama narkewa, ya kura mata ido. Lashe bakin shi yayi cikin nutsuwa sannan yace mata. “List to me! Bani da niyyar kara aure! Sam ni bani ra’ayin tara mata, ki rike alkawarin a bazan tab’a miki kishiya ba. ki ajiye wannan a ranki, surarta girkinta duk basu gaba na. Ni kece a gabana. Ina sonki ko baki da komai zan zauna dake a haka Ni dai ki cire zargin da kike min.15 Sannan ki lura Yarinyar nan Spain zamu tafi da ita, kamata yayi ki jata a jikinki yadda zata gaya miki damuwarta da wasu abubuwa. Bawai kina biye mata ba, idan baki manta ba na gaya miki Mahaifinta shi ya cika min burina na zama ɗan kwallon da ake alfahari dashi a Afrika baki daya, duk inda Na shiga a duniya Dabji ake kira. Please and Please, ki daina zafaffa kishinki akan Parih, sabida ba kalar matar da nake so bace, koda ina da ra’ayin aure balle bani dashi ke kad’ai kin wadatar dani, don Allah bani son kina zagin iyayenta.3 Idan kika daurata da wannan halin duk inda kuka shiga zata kunyataki! Ni kuma bani da ikon magana sabida laifinki ce.” Mik’ewa yayi zai shiga ban daki har ya shiga sai ya leko sannan yace. “Ki lallaba ta ku shiga kitchen, ki mana abinda zamu ci, kema ki iya in ba haka ba.” Ya kashe mata ido, tashi tayi tabishi da gudu ya rufe Kofar ban dakin cikin shagwaɓa ta shiga buga kofar tana cewa. “Buɗe in ba tsoron ba! Allah tunda kasan baka da gaskiya ba.”. Buɗe kofar yayi cikin zafin nama ya fincikota zuwa ban dakin, kasan shower ka kaisu, ya bude musu ruwa. Hannun shi na kan cikin ta, juyata yayi. Suna kallon Juna, cikin sanyin murya yace. “Kece tafarko kece ta karshe! Bani fatan wata alaƙa ya hadani da wata macen bayan ke! Ina son na kasance dake har karshen rayuwata.” D’ago kanta tayi tana kallon pink lips d’inshi. Hannunta takai beard ɗin shi tana shafawa, a hankali har ta sauko dashi kirjinshi. A sannu ta shiga shafa inda yayi guru a jiki shi, wato irin budadd’yar jikin nan ne, (body building irin jikin Salman Khan 🤣😂 tarin tsokoki) “Kina son su ne?!” Ya jefa mata tambaya. Murmushi tayi, sannan ta hade bakin su guri guda, a hankali ruwa ke kara sautin sumbatar juna da suke yi. Cikin wani irin yanayi, suke abinsu. Tunanin AMIDUD ya tsaya cak a sakamakon tab’a kirjin matar shi da tayi, take abinda ya faru jiya ya dawo mishi, ba tare da ya fahimci abinda yake ba. Kawai ya kuma dulmiya a duniyar t-b-t.4 Ganin abinshi na shirin wuce iyaka ne tasata kwace bakinta ta ture shi tana dariya da sauri ta fice a ban d’akin, dafe goshinsa yayi yana kuma hasko abinda ya faru jiya, ga kuma zafin kan da ya haɗawa kanshi da wanda Parih da Lamisah suka haɗa mishi, ……. Cire kayan ta Lamisah tayi sannan ta daura wani b’ingililin towel ta nufi dakin Parih. Tana shiga ta same ni a bakin gado, sanye da doguwar riga. Kallonta na fara tun daga kafafunta har zuwa kan towel din. Ban san lokacin da dariya ta kwace min ba.1 Wasu sirarar kafanta irin na wannan yan gwaigwai din nan. Rike cikina nayi sannan nace. “De yu no, hauw yu luk?!” B’ata rai tayi sosai, rike bakina nayi sannan nace. “An sori! But yu luk lek babi, irin an gwaigwai din nan, wanda ake sakawa a Mbc. Meye ma sunan su, akwai katun dinsu sindirela! Da silifin biyuti! Da kuma, Biyuti an di bilasta!”5 “Dalla rufe min baƙi, wawuya kawai. Jaka idan ma an turo kine dan ki rabani da mijina karyanki tasha karya. Wallahi sai kin bar min mijina, karya mara zuciya.”8 Dariya nayi, sannan nace. “Oho dai! Kije ki tambayi mijinki akan me ya ajiye ni, ya sake Ni Naje nayi rayuwata kamar kowa mana, sannan idan turo Ni aka yi! ” Rufe baki na nayi sannan na cigaba da cewa. “Kije ki tambayi shi! Nawa yaji piraz na burodin da ya tab’a, ef yi no yu no, coman gara way mey firandi!”4 *_Allah sarki! English ana cin mutuncin ka a bakin Parih 🤣😂 Akwai kura da Nagode

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE