MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 10

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 10
Amsawa Maman tayi tana had’a musu zobo k’arasawa yayi ya zauna akan kujera ‘yar tsugunno sai faman shafa sajen fuskarsa yakeyi. Umma Dijeh ce ta Fito daga parlor kasan cewar muhad’u a parlo ne ta kallesa tana murmushi cikin wasa tace mai. “Likita bokan turai, daga sallar juma’a kuma sai ina’! K0 yauma za’a lek’a mak’ota ne..?!” Wayarsa ya zaro zai kunna domin tunda ya baro makarantarya kasheta sabida yasan dole Sadeeq ya nemeshi, shikuwa be shirya abinda zai gaya masa ba. Kallan Umma Dije yayi 
sannan yayi murmushi yace. 
“Haba Umma jiya fa naje, kuma yauma bata nan.” Dariya suka yi itada Maman sannan ya tashi ya flto yashiga d’akinsu, kayan jikinsa ya rage ya zauna daga shi sai vest da boxer shorts sannan ya kuma d’aukar wayarsa dai-dai lokacin kuma Sadeeq ya kuma kiransa. Babu yadda zaiyi dole ya d’aga kodan ya kare kansa daga wajan abokin haihuwartasa, cikin basarwa ya kara a jikin kunnansa tare da fad’in, “My twinnie sai kaga na taho ko?!” Sadeeq dake zaune a k’ofar gida ya tabe baki sannan yace. “Ba gani nayi ba nemanka nayi na rasa wanda kuma ni bansan dalilin yin hakan ba, twinnie kasan irin tashin hankalin daka sakani? Da police station zanje nakai report sai kuma muka yi waya da Mother take cemin gakanan ka k’arasa why did you do this to me ah?!” Duk sai Abubakar d’in yaji babu dad’i ganin yadda duk ya tayarwa da d‘an uwan nasa hankali, da kyar ya samu mafitar da zai wanke kansa ya numfasa tare da cewa. 
“Kayi hakuri nima saida na taho naga rashin dacewar hakan tunda bamuyi sallama ba, abinda ya faru shine ina fitowa Dr Inuwa yake sanar dani ana nemana a cikin asibitin da gaggawa shi yasa duk na rud’e na kashe wayana dan karsu dunga damuna sorry twinnie kaji kayi min afuwa..” “Okk bakomai yanzu tunda naji kana gida sai anjima.” Kamar ya tambayesa INdo sai kuma yayi shiru suka ajiye wayar shi kansa besan yadda zai fad’i abinda yakeji ba har mamaki yake yi ya ajiye wayar yashiga toilet. Wanka yayi lokacin har an kawo mai abincinsa an ajiye amma ko kallansa beyi ba sai wayar ya sake d’auka ya shiga gallery, hotunan dayayi mata ba tare da kowa ya sani ba. Yana gani yana duba na saurab ya rasa yagano meke damunsa amma inah..ya kasa tantancewa sai faman k’aryata zuciyarsa yake yi da abinda take shaida mai. 
INdo kuwa tana zuwa gida ta fara cire kayan jikinta tana cillarwa ta sanya wata kod’add’iyar shadda doguwar riga wanda ta d’age mata sannan ta dawo tsakar gida ta zauna tana kallon kunshinta. Wani irin tsanar malam Sadeeq da Abubakar suka sake mamaye cikin zuciyarta ta cewa Inna. 
“Inna wanki zanyi gobe na tafi gidan yakumbo Tsahare, wallahi billahillazi bazan sake zuwa makarantar ba guduwa zanyi daga kauyen naga ta tsiyarsu mugaye.” Cikin dafe k’irji Inna tace “ke ‘yarnan saye kuma? Kiyiwa Allah da ma‘aiki kiyi shiru da maganar tafiyar nan kinsan dai babanku baya son zuwanku garin nan tun abinda ya faru tsakaninsa da jummala.” “Inna wallahl saina tafi kina abinda mugun malamin nan yace, wal Idan na dena zuwa makaranta saiya saka an d’akkoni toh wallahi barin garin zanyi hena dad‘e sannan zan dawo ehe.” 
Hankalin Inna ya tashi dan tasan idan baban su yaji toh bashakka sai anyi fitina duk da cewar tsaharan k’anwarsa ce amma tun a haihuwar shehu suka samu sabani akan naman suna shikenan sukayi baram baram kowa yace bashi ba d‘an uwansa sannan yacewa Inna ya haramtawa ‘ya’yansa zuwa garin idan sukaje kuma Allah ya isah. Tashi INdo tayi tabar gidan ta shiga gidan Rukayya, tana ganinta ta fara murna tare da cewa. “Kai INdo shine ko a kawo min kyautar ingani k0?!” Saida lNdo tasamu guri ta zauna sannan tacewa Rukayyan “Yo ai basu bani ba, wai wani ban yanke farce ba ninasan dama malaman nan ba kaunata sukeyi ba kawai dan dai nafl karfin sune bayadda zasu yi dani shegun.” “Kan uba! Yanzu kina nufin babu abinda malam Sadeeq yayi miki?!” “Sai duka nama dayayi kuma nace Allah ya isa.” Nan suka cigaba da hira har INdo na bata labarin tafiyarta saye gobe Rukayya tace. “Kai INdo sai kuma yauhe zaki dawo?!” INdo na watsa shinkafa da wake tana cewa “babu lokaci idan na tafi henayi aure zan dawo yasin.” “Kai INdo baxaki dawo ba kenan?!” Rukayya ta kuma tambaya cikin jimami, ita kuwa INdo ko’ajikinta tace “Eh bazan dawo ba he randa malam yadena zuwa garin nan.” 
“Kai Allah ya wadaran wannan malamin da yaja zaki tafl, zamuyi rashinki lNdo barema 
Inna.” “Kyale Inna can na barota sai masifa take dan nace zani saye wai bazani ba toh alkur’an saina tafi.” Haka suka dinga hira da Rukayya har bayan la’asar sannan ta koma gida inda ta tarar da Inna ta gayawa babansu yace toh babu inda zata ta kule d’aki bata sake fltowa ba. Tun asubar fari ta farka ta tsinci kayanta tasa a d’ankwali ta d’aure ta d’auk’e fltilar da aka haska d’akin da ita wato shekarau mekwayayen nan k’ananu a jikin katako tayi sad’ab sad’ab gidan a kulle yake tajefa kullin kayan ta katanga sannan itama ta kama ta dirga ta kwashe kayan nata ta antaya da gudu sai bakin titi ko tsoro bataji. Tayi tafiya sosai sannan gari ya fara haske daman babu buk‘atar yin sallah dan bawani yi takeyi ba sai taga dama. Mota na zuwa ta tsayar dasu ta shiga dama da d’ari ukunta a hannu data ara wajan Rukayya. Can gida kuma tunda suka farka suke neman lnndo, duk gidan da akasan tana zuwa saida akaje bata nan. Kuka Inna tasanya domin tasan yau lNdo tayi mata abinda zai iya balla mata aure, lokacin da baban yaji cewa yayi k’arya Inna takeyi tasan ta tafi dan haka itama ta shirya tabi bayanta su dawo tare kasan cewar sunsan zata iya zuwa. Ko kud’in mota Inna batada su amma a haka malam Hamza ya takura mata kan cewa sai taje ta dawo da lNdo haka ta fito tana hawaye. A bakin titi malam Sadeeq ya ganta harya wuce ya dawo duk da cewar ta rufe fuska da mayafin jikinta tana share hawaye yaje yace. “Baiwar Allah kiyi hakuri lafiya dai ko..?” Shiru batayi magana ba duk da besan kowace bace ya zaro d’ari biyarya bata babu yadda zata yi ta k’arba tana ta zazzaga mai addu’a shidai ya wuce ita kuma mota na zuwa tashiga tana fatan Allah ya temaketa can din INdo ta tafi, ayau bazasu kwanaba zata dawo da ita. 
Wajan k’arfe biyu da rabi lNdo ta shiga wata rugar fulani anan cikin sayen bakinta a washe hannunta d’auke da kullin kaya, suna zazzaune k’ark’ashin bishiya suka hangota nan da nan yakumbo tsahare ta had’e rai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana dakan fura haka INdo ta k’arasa gurin tana dashare musu hak’ora. “Wacece wannan kamar mai sunan Gwaggo..?!” Cewar talatu yayar malam Hamza dake kwance, INdo ta k’arasa tare dayin cilli da d’ankwalin kayan nata tace. 
“Nice nan yakumbo talatu ehe duk kuna nan,yau dai gani a garin ku ina kwananku…?!” Duk suka amsa suna tambayar ta su Sagiru da Nafeesa da Shehu tace laflya lau amma banda yakumbo tsahare daketa faman dakan fura, ko ajikin INdo ta mik’e tare da zuwa 
wajanta tana cewa. “Sannu yakumbo tsahare, ina su Iawisa take..?!” “Ke karki yimin rahin kunya aradun Allah kuwa, idanma Ubanki ne yau ya turoki toh dagake harshi d’in zan iyayi muku rahin mutunci jacan ki bani guri ni.” “Allah baki hakuri daga tambaya..” INdo ta fad’a tare da komawa wajan su yakumbo talatu aka kawo mata d‘umamen tuwo da fura da nono tana ci suna hira har su lawisa suka dawo daga tallar nono, murna da farin ciki ba’a magana duk da cewar Lawisan cikima gareta har tayi aure tsiranta da INdo shekara biyu ne. Cikin gidan suka wuce suna zazzaga shirmen su. Inna kuwa la’asar sakaliya ta iso saye sabida da kyar ta samu motar da ta kawota a d’ari da talatin. Saida tayi sallah sannan taci kwad’on rama da fura bayan sun shaida mata cewar INdo tazo amma sun tafl tatsar nono, hankalin Inna ya tashi  ta kalli malam iro mijin yakumbo talatu tace. 
“So nake a yau mu koma gida gahi bata kusa kuma ina neman yadda zanyi mu samu kud’in komawa.” Malam iro ya kalleta da mamaki sannan yace. 
“Haba dai Maryamu, yanzu flsabilillahi har yaushe zaku koma gida, hasalima ita INdon bata kusa kuma da kyar idan zata yadda tabiki dan tasamu yara, kuma na tambayeta randa zata koma tace sai an kori wani malami a garin naku.” 
Inna ta fashe da kuka malam iro ya kalleta yana jin tausayinta dan yasan tsoran d’an uwan matar tasa takeyi. Hakuri ya dinga bata ita dai hawaye kawai takeyi gashi tana matukar kaunar malam Hamza duk da cewar shima yana matukar santa amma hakan baya hanashi yimata wulak’anci. Har magariba su INdo basu dawo ba sai wajan k’arfe takwas na dare, 
koda taga Inna batayi wani murna ba kotaji tsoro ita kuma nauyin mutane ya hanata yi 
mata magana. Cikin dare Inna tasamu INdo ta gama Lallabata akan ta yarda gobe su koma amma fir tace wallahi bazata koma ba nan zata zauna sai lawisa ta haihu koda zata koma. Da gari ya waye haka Inna ta kama hanya dama tunda taje yakumbo tsahare bata ko kalli inda Inna takeba har ta kama hanyar komawa sumaila. Koda Inna ta koma gida malam Hamza baya nan, kam ya dawo harta sarrafa musu gero tayi musu burabusko yana dawowa yaci yayi hani’in data sanar masa cewar lNdon tak’i dawowa sai yace. “Kyaleta Maryamu ni kaina na huta da fitinarta taje can karta dawo d’in.” 
Bayan sati biyu. 
Tunani da damuwa da begen son ganin lNdo suka addabi zuciyar Abubakar, duk iya yinsa na ganin ya kawar da hakan daga cikin zuciyarsa hakan ya gagara. Ya rasa meyagani a tattare da ita haryakejin irin abinda yakeji cikin ransa da gangarjikinsa, yasan duk lokacin da asirin zuciyarsa ya fito fili zaisha wulak’anci gurin Sadeeq dama sauran abokansa. Tashi 
yayi ya tafi Sumaila kauyen na sani direct babu wanda ya sanarwa. 
Yana zuwa zuwa ya tarar su Sadeeq sun tashi daga makaranta yarama sai tafiya gida  sukeyi, samun kanshi yayi dayin gaba zuwa unguwar su INdo ko Allah zaisa ya ganta, amma har Sadeeq ya dawo ya tarar dashi besamu yaga ko kyallin kallabinta ba hakan kuma ya hargitsa ilahirin tunaninsa na Ina zai ganta? twinnie..! Tab lallai kaida kace min kaida garinnan saidai in wucewa zakayi shine yau na ganka at this time..?!” 
K’ak‘alo murmushi Abubakar yayi yana kallon hanya dan be fidda ran zai hangota ba. Ganin yadda Sadeeq d’in ke kallansa ne yasa shi saurin cewa. Malam Sadeeq nasu INdo, wai kuwa haryanzu kana basu kyautar?!” Meza’a fasa twinnie? Itace dai tun ranar bata sake zuwa ba, dana tambayi babanta rannan danaje gidan yace wai ta gudu kauyen su sai randa aka koreni zata daw

o kaga kuwa ba rana kenan..” 

Daram..! K’irjin Abubakar ya buga besan lokacin da ya furta “what…?!” 
Hmm nanfa akeyinta

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE