MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 11
MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 11
Sadeeq ya bishi da kallon mamaki ganin yadda ya furta kalmar tamkar yace masa shine yabar garin ko Mama. Kallansa ya kumayi kafin ya juya yayi hanyar shiga gida yana cewa. “Kai twinnie bafa Qibd’iyya nace maka ba naga har kana ihu.” Harya bud‘e gidan ya shiga Abubakar betaso ba, hanyar gidan su INdo yabi da kallo ji yake tamkar zai ganta amma bako kurarta haka ya k’araci zamansa kam ya tashi yabi Sadeeq cikin gidan. Lokacin daya shiga tararwa yayi Sadeeq harya shiga wanka hakan yasa shi zama tare da dafe goshinsa sabida tsananin saramai dayaji yana yi. Fitowa Sadeeq yayi zama yayi kusa dashi yana kallansa soyake ya gano wani abu a tattare da d’an uwannasa, Abubakar ya d’ago ya kalli Sadeeq ganin yana mai kallon tuhuma yasa shi wayan cewa ta hanyar cewa. “Twinnie wai yaushe zakuyi hutu ne?!” Sadeeq ya mik’e tare dajanyo singlet zai sanya yace “kasan ba’a fiyeyin hutun maulud ba so kawai sai term ya k’are ni yanzu mafa na farajin dad’in makarantar sabida suna bani had’in kai yanzu shi yasa na dena neman transfer.”
“Oh idan na fahimta kana nufin kace dama Humaira ce ke baka matsala duk fad’in makarantar k0?!” Abubakar ya tambaya yana zaro ido, Sadeeq yafara shafa mai yana cewa, “eh toh idan nace maka a’a nayi kamar kuskure idan kuma nace maka eh toh shima banyi karya ba domin tun sanda ta dena zuwa nake ganin students d’in suna k‘ara maida hankali, haka nima ban sake zagin wata k0 wani ba, kai banma sake rik’e bulala ba kaga kuwa idanma nace itace matsalata banyi k’arya ba..” ‘
Abubakar ya dafe kai jin Sadeeq yace INdo ce matsalarsa yaji haushin Sadeeq sosai saidai ya danne dan yanzu so yake INdon ta dawo gida bayajin zai iya hakura har ranarda tayanke hukuncin zata dawo yayi yace. “Amma twinnie a ganina a matsayinka na malami kamata yayi ace kaine ka fara k’arfafawa yarinyar nan gwiwa wajan ganin tasamu wani kyakyawan abun dazai taimaka mata a rayuwarta kuma a matsayinta na mace.”
“Kai twinnie kasan kuwa yarinyar nan? Ka manta abinda tace min da addu’ar datayi min, wai ko’a lahira ina kusa da flr’auna. Wallahi a yadda naji zuciya ta a lokacin ko naso in targad’ata Allah yayi malamai suka saka baki na kyaleta.” Ganin yadda Sadeeq yad’auki zafine yak’arawa Abubakar damuwa, babu ta yadda zai iya samun ganin INdo sai ta hanyarsa yau gashi ta kaishi bango yace bazai temaka mata ba. Cikin nuna halin damuwa Abubakar yace.
“okey naji ni nayadda zan tallafa mata koda dawani abunne nasan wata rana al’umma zasu amfana da ita. Yanzu inason kasanya kaya kaxo muje gidan su muji inda ta tafi.” “Twinnie wai yaushe kadawo me sauk’in kaine? Kodai-kodai so kake ka kiwata ta tun yanzu kafara banruwa?!”
Mtwww Abubakar yaja tsaki dan shi kansa jinsa yake a wani bai-bai, yau ko kiran Qibd’iyya beyi ba sabida zumud’in son ganin INdo. Kai meye haka twinnie? Ni kamar ni zan tsaya jiran wannan kurkurar yarinyar, har yaushe ma zata waye tayi kamar yadda nakeson Qibd’iss? Kawai dai ina son mu sami ladane ta hanyar gina mata wata rayuwar sabuwa wannan shine kawai manufata…”
“Ohh toh ai akwai irinta da suke buk’atar hakan twinnie bawai dole sai itaba, ni wallahi na tsani yarinyar nan garama data bar garin wawuya kawai sai idanuwa kamar na mayu..” “Shhhhiii twinnie duk meyayi zafi hakan? Kayi hakuri nitunda nayi niya zan temaka mata insha Allahu tunda kai kayi fushi…” “Hakan dai yafl..“
Cewar Sadeeq. Sun dad’e suna hira har akayi la’asar zasu tafl masallaci Abubakar yake cewa twinnie idan mundawo ina son karakani muje gurin baban ta ko Maman ta dan Allah.” “Ohh wai daman baka manta da zancen ba?” Sadeeq ya tambayesa yana dariya, Abubakar ya kalli katangar gidan ya tuno lokacin da ta watso mai hijjab da takalmi yayin da Sadeeq ya tuna sanda ta watso mai ruwan k’anzo suka wuce Abubakar na murmushi yayinda Sadeeq ke famanjan tsaki. Suna dawowa Sadeeq ya d’auka ko mutumin nasa ya manta dan haka yak’i kallon koda gidan su yarinyar, suna zuwa zasu yi kwana Abubkhr yayi saurin dakatar dashi ta hanyar rik’e masa hannunsa yana cewa. “Ya haka ne twinnie? Ina kuma zakaje?!” “0h wai dama baka manta ba?” “Eh ai kasan ba’a manta yin alheri musamman idan mutum yayi niya.“
Sadeeq yace “naji toh karka gayan magana,ke shiga kice ana sallama da malam Hamza.” Yayi maganar yana kallon Nafeesah dake zaune a k’ofar gida, ta kallesu ganin su iri d’aya sak bakinta bud’e haushi ya Kama Abubakar cikin takaicin kallon da take yi masa yasa shi cewa “Ke bazaki bane kika saka mana na mujiya?!” Da sauri tayi firgit tana susa tace “Ai baya nan yana can wajan aikinsa a bakin hanya.”
Kallon Abubakar Sadeeq yayi dan yaga yazai yi amma sai yaga ya wani tabe baki irin sunyiwa kansun nan amma cikin zuciyarsa kwata-kwata ba haka bane suka juya suna tafIya Sadeeq yace. twinnie muje na kaika inda zaka temaki masu neman temako domin bawai rayuwar INdo ce kad’ai take buk’atar hakan ba, indai kayi niyar temakawan to kazo muje wani gidan.” Mtwwwww Abubakar yaja tsaki ganin yadda Saseeq din ke takura masa da zancen wani gidan, shi duk gaba d‘aya mafa yafi buk’atar yaga lNdon ko zaiji wani barin na gangar jikinsa da ruhinsa sun samu sassauci amma Sadeeq ya kasa ganewa ya kuma had’e rai cikin basarwa yace, “okey bari next week zan dawo sai musan abinyi yanzu bari na koma sabida aikin yamma gareni.” Yafad’a yasan duk bala’i nan da ranar asabar lNdo ta dawo, shi dai Sadeeq be damuba dan dama be d’aukarwa wani aiki ko takura ba bare yasa kansa cikin damuwa, yana yin alheri a duk lokacin da yake da kud’i. Sallama suka yi a bakin k’ofa Abubakar ya tafi yayin da Sadeeq ya shiga cikin gida cike da kewar abokin haihuwartasa. Abubakar kuwa tsakanin sa da Qibd’iyya sai hange daga nesa, sam yanzu ya dena ganin kyawunta bare yaji kwarin guiwar zuwa wajanta. lta kuma ta rigada ta kamu da kaunarsa domin ya riga yayi mata dashen zazzafar soyayyarsa gashi ta dena kula kowa sabida shi, yau kimanin sati uku kenan ta kasa ganokanshi ya rage nemanta ko kiranta a waya bare ya taka yaje gidansu tad‘i sam ya dena har abun ya fara damunta. ‘ Kwanaki na tafiya Abubkhr na kuma shiga cikin damuwa da tunani. Ana ya gobe zai koma sumaila kauyen na sani k’aninsa Khaleefa ya shigo d’akin nasu, kwance ya tarar dashi yayi rub da ciki ko shirin tafiya asibiti beyi ba khaleefan ya k’arasa ciki tare da cewa. “Yaya Habu Abba na k’iranka yana d’aki.” Beko juyo ba ya d‘aga mai hannu sannan khaleefa ya flta shi kuma ya mik’e dakyar ya sanya zilaika sannan ya fita yana wani bacin rai. Kwankwasa k’ofar yayi Abba yace ya shiga, yana shiga ya gaidashi sannan yasamu guri ya zauna abban yace. Yauwa Abbakar dama zance Mariya ne, mahaifinta yayi min magana an tambayeta wanda ta tsayar tace kai shine nace toh ya bari nazo naji ta bakinka ya ake ciki.”
Gabaki d’aya ya daburce besan lokacin da yace. “Abba aure kenan fa..?” Yafad’a cike da tashin hankali dashiga cikin d’imuwa, Abba ya kallesa tare da cewa. “Eh Abbakar aure tunda ai kaine kaje gidan nasu.””Amman Abba da an d’an k’aramin lokaci kafin ayi maganar auran nawa zuwa nan da wani d’an lokaci.””Amman kai Abbakar kasan dai bazan zuba ido kaida d’an uwanka kuzauna har yanzu babu Aure ba? Kuma gashi kai hargidan su yarinyar sunsan da zamanka.” “Eh Abba ai bayi ne baza muyi ba, lokaci kawai nakeso ka k’aramin dan inason tabbatar da wani abu dan Allah…” “Tom naji zan k‘ara maka lokaci aman da sharad’in wanan maganar tamu ta karo karatunka zuwa k’asar Spain dan nariga na samu duk abinda ake buk’ata. Yanzu gobe nakeson kaje abuja zakayi wani signing na tabbatar da tafiyar taka, sai kuma na koma kan Saddiqu shima a sake mai wajan aiki.” A rud’e yace “Abba har yanzu dama kananan da burinka na k’aro karatun mu? Innalillahi.”
Ya furta cikin sanyin murya, Abba yace “Eh Ina nan da wanan burin Abbakar Ina matukar kaunar naga kun cigaba a duniya, don Allah kucika min wanan burin nawa dan wata ran kune iyayen k’annanku, sannan nima naji dad’i a tattare daku.”
Nan da nan jikin Abbakar yayi sanyi, babu yadda zai yi dole yacikawa Abban su burinsa ya mik’e da kyar yana had’a bango harya koma cikin d’aki. Kwanciya yayi ruf da ciki ya fara tunanin taya zai iya samu yaga INdo har ya tallafi rayuwarta sannan ya bawa zuciyarta abinci dan yana son ganinta ra’ayul Ayn. Ina zaije yasake ganinta kaf’ln ya tafi, yanzu ya yarda ba shida wani buri sai son ganishi tare da lNdo…
Hmm wannan soyayyah haka