MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 12

MUSAYAR ZUCIYA

CHAPTER 12

Washe gari Abubakar ya yafi abuja danyin abinda Abba yasa shi. Tunda kuma ya dawo daga abuja kullum akwai inda zashi sam baya samun zama gashi yayi-yayi Sadeeq ya d’aukar masa amana da alk’awarin nemo INdo ya kula da ita amma Sadeeq yak’i shi adole idan zai tayashi toh saidai ya canza wata amma ba INdo ba, da haka sukayi bankwana baram-baram kowa najin haushin d’an uwansa. INdo kuwa wayyo Allah tazo saye kauyanci da k’arin abubuwa duk sun dad’a k’aruwa ta zama tamkar ‘yar garin duk inda kaje sai kaji labarinta kaf kauyan sun-santa dan akwai shiga jama‘a. Da mutum d’aya ne basa shiri wato yakumbo tsahare, sam basa jituwa da juna ko a layin band’aki.
Ranar da lawisa ta haihu kuwa su INdo sune masu jigo, anyi ruwa anyi tsakl’ tazama tamkar itace mejegon dan ta kanainaye komai lawisa kuwa sai kawaici take bata magana. Ranar suna aka sanyawa yarinyar Raihanatu suna kiranta da Ladi kasan cewar ranar lahadi aka haifeta. Watan INdo biyar a garin saye ta kuma irin wayewar nan ta karkarar fulani. Jin dad’inta kawai takeyi samari kuwa su tara ne kowa sonta yakeyi suna yi mata kyaututtuka sosai dan da haka take tattara kayan sawa tana kuma siyan kayan kwalliya abin sai wanda ya gani duk bak’in cikin yakumbo tsahare sai dai ta kawar dakai. Ta manta dasu Inna tama manta dasuwaye malam Sadeeq sam yanzu rayuwarta takeyi babu takurawa…

‘BAYAN SHEKARU UKU’

K’arfe hud’u da rabi da minti shida, Sadeeq Salman Haruna ne cikin mota 403 ash color yana bin bayan wata kyakyawar budurwa. Tafe take cikin nutsuwa da iya bawa k’asar da take takawa hakk’inta, duk da cewar taga ana binbayanta hakan besanya ta waiga ko tayi alamum tsayawa ba harta shiga kwanar gidansu.
Shima beyi mata magana ba yana ganin gidan data shiga yayi murmushi sannan yajuya kan motarsa yabar layin yana sak’awa da kwancewa ta yadda zai fara tunkarrata da kalma mafl tsada da daraja a gurin wata d’iya mace. Saida aka d’ibi kwanaki hud’u yana bibiyar rayuwar budurwar ba tare da tasani ba sannan. Ranar asabarda misalin k’arfe hud’u da rabi ya dira a k’ofar gidan, yaro yajira yazo yace yashiga ya k’ira masa Fatima Kabir ya’u. Ba jimawa sai ga yaron da wani matashin saurayi wanda zaiyi sa’an Sadeeq d’in sun fito tare, yana zuwa suka kalli juna cikin tsananin mamaki matashin yace. “Kardai ace twin’s d’in dana sani ne? Abbakar ne ko kuma Sadeeq?!” Dariya Sadeeq yayi tare da bawa saurayin hannu suka tafa yana cewa “cinka da kanka Shamsu kabeer Ya’u dama kananan.?!” “Hahaha ina nan mana, dallah ka tabbatar min waye akinku kasan kud’inne sai a hankali.” Sukayi dariya dukansu sannan yace. “Sadeeq ne Shamsu ya rayuwa.”
Shamsu yace “Alhamdulillahi, gaskiya na dad’e ban sake sanya ku cikin idona ba tun sanda mukayi candy a GSS kwangwaso, ya wai kaine kenan ka biyu sisi na gida.” Shafa kai Sadeeq yayi bayan ya zame hular zannar shi sannan yayi murmushi yana cewa. “Wallahi kuwa ashe ma k’anwata ce. Anyway nidai nagani kuma ina so ya za‘ayi kenan?”
“Toh ya zanyi tunda kazo kawai zakajamin raini, k’anwata ce Fateema kuma kayi sa’a this year tayi graduation but gaskiya munan gidan ba’ayi wa mace aure sai tana da ilimin NCE ko Diploma, gashi ita kofarawa batayi ba yakenan?!” Murmushi Sadeeq yayi cikin jin dad’i domin hakan yayi dai-dai da lokacin dawowarsa daga k’wara state. cikin rashin nuna damuwa yace. “Shamsu babu damuwa ni dai burina gidan ku susan dani, kuma a bani dama mufara fahimtar juna tun yanzu.” ”Karka damu tunda kana dani babban yaya, wai yanzu wane aiki kake yi.ne.?!” Sadeeq yayi murmushi tare da cewa “Toh kasan rayuwa babu yadda bata zuwar ma d‘an Adam, da ina teaching ne a wata secondary school amma yanzu ina nan BUK shekarata d’aya da dawowa nan ina lecturing, sai dai akwai wani business danakeyi acan k’wara state hope babu wanda ya rigani Fateema..?!” Dariya Shamsu yayi tare da sake bawa Sadeeq hannu suka tafa yace. “Karka damu abokina insha Allahu zaku dai-daita bari ma naje na Fito maka da ita.””Toh godiya nake dad’in aboki a gidan su budurwa kenan suka kuma tafawa sannan Shamsu ya koma gida. Yana shiga falo ya kalli Fatima dake kwance tana karatun wani novel akan kujera, had’e rai yayi shi a dole babban yaya yace. “Ke Fatima tashi ki shirya kije waje abokina yana jiranki.” Da mamaki ta d‘ago tana kallasan yace “eh ko bazaki je bane?!” Fatima tace “Haba Yaya Shamsu amma kasan dai baba yace karna kula kowa k0…” Ya sake had’e rai sannan yace, “ke! Toh waye baban yanzu a gabanki? Zaki tashi kosai na bugeki, sakarya kawai.” Tashi tayi tana zumburar baki ta kalli Umman su ganin harkar gabanta kawai takeyi yasa Fateema shiga d’aki tana gunguni. Hijabi ta zurma ta fIto Shamsu ya kalleta tare da cewa. “Ke koma ki shafa hoda da janbaki, kinsan ko waye yazo gurinki kuwa.?” “Gaskiya ni Yaya…” Yayi saurin katseta ta hanyar daka mata tsawa yana cewa, “Baxaki je
Kiyi abinda nasaki bane?!” Sake komawa tayi harda hawaye sannan ta shafa hoda tasa coffee d’in janbaki sannan ta kuma fitowa, Shamsu ya kalleta sannan yace “Good girl sauran kuma kije kiyi mai fitsara ko ki gayamai babu dad’i ranki saiya baci wallahi domin bata mana suna zakiyi wuce.” Fita tayi tana kunkuni, a zaure tagan shi suka had’a ido Sadeeq ya sakar mata Murmushi tayi saurin kawar dakai tare da tsayawa ta jingina jikin bango. Jitayi yayi mata sallama ta amsa yayi dariya kad’an ta kuma d’agowa ta kallesa karaf suka had’a ido. Samun kanta tayi dayin murmushi sannan ta gaidasa ya amsa tare da gabatar mata da kansa tana jidai amma batace komai ba sai daya ce mata. “Ina fatan zaki yarje min nashiga cikin rayuwarki har muyi aure, nayi miki alkawarin kare duk wani hakkinki da kare miki duk wani mutuncin ki burina kawai ki yarda dani.” Samun kanta tayi da cewa “Shikenan na gode tunda har Yaya nane ya baka damar da bantaba tsayawa da wani ba kamar haka.” “Toh godiya nake yiwa Yaya Shamsu, sai kuma yaushe zan kuma dawowa Zarah..?!” Ya tambaya yana kasheta da salon shi tayi murmushi cikin sanyi, ita kanta batasan lokacin da take maida reply ba. Ya had’u iya had’uwa dan k‘irjinta banda bugawa babu abinda yakeyi. “Nima ban sani ba.”
Ta bashi amsa yace “Toh sai wani satin insha Allahu a gaida Umma.” Da sauri ta shiga gida yayi dariya yana zuwa mota sai ga Shamsu ya fito yace.
“Kai abokina irin wannan shaf-shaf d’infa wai har kagama siye tane?!” Sadeeq yayi dariya tare da cewa, “ban fad’a ba nidai, kawai dai dama zuwa nayi na gabatar mata da kaina.” “Hakan ma yayi kyau mutumina, toh Ina Shi Abubakar d’in.”
“Yana Spain sun rik’esa amma nan da one month zai shigo k‘asar insha Allahu.” “Ahh lallai kaji manya toh Allah ya dawo dashi lafiya muna murna.” “Toh Shamsu godiya yake bari na gudu nima ka kular min da matata.” “hmmm harta zama ma kenan, Allah ya kiyaye hanya a gaida mutanan gidan.“ Suka yi sallama Sadeeq ya tafi tun daga lokacin indai yana kano toh zaije gidan su
Fateema idan baya nan suna mak’ale da waya ta hanyar shamsu domin babanta yaki yadda ta rik’e waya sai ta fara karatu. Sun shaku sosai fateema na sanshi shima yana sonta alkairi kuwa duk zuwa da abinda zai kaimata. Doctor Abubakar Salman Harun, matashin saurayi mai tak’ama da kyau da ilimi nagarta da wayewa ya zama babban likita wanda duniya ta sanshi take kuma tak’ama dashi. Tun bayan gama karatun sa da shekara biyu a, k’asar Spain suka rik’esa domin suma ya ceto alummar su ta hanyar kwarewarsa, yana gudanar da aikin cikin walwala da jin dad’i duk da cewa tunda yabar k’asar tunanin lNdo be taba gushewa daga cikin al’amransa ba, ya sakawa ransa cewar Allah ne zai bashi lNdo bawai wani abun nasaba hakan yasa ya kwantar da hankalinsa yacigaba da karatunsa cikin nutsuwa da sadaukarwa rayuwarsa akan Al-ummah.
Ganin yak’i dawowa ne hakan yasa mahaifinsa ya umarce sa da yadawo gida domin taimakawa ‘yan uwansa ‘yan Nigeria, bai k’i tayin mahaifin nasa ba saboda shima bak’aramin missing d’in gidan yayi ba. Ga wasu mafarkai dayake yi game da INdo da yake kusan kullum yana son ya ganta yana kaunar sake had’uwa da ita. Hakan yasa yayi niyar komawa gida bayan yayi wa asibitin ‘CANTABRIA HOSPITAL’ bankwana. ba suji dad‘in barinsa aiki ba aman sun bashi damar duk lokacin da yake da buk’atardawowa suna maraba a kowane Iokaci..
Wednesday morning at 8:30am cikin airport d’in malam Aminu kano matashin saurayin mai shekaru 32 ya sakko daga cikinjirgin Nigerian airlines. Sanye yake cikin wasu dakakkun suit coffee color sai ta cikin white da cover shoe gashin kansa a saisaye bakikk’irn ya gyara kyakyawan sajansa sai wanda ya ganshi zai iya tantacce d’an wace k’asar ne. Sadeeq ne ya fara ganinsa dan haka shi yafara k’arasawa wajan cikin fara’a suka rungume
junansu. Abba ma ya karasa Abubakar yayi saurin tsugunnawa yana mik’a gaisuwa mutanen gurin sai kallonsu ake, zuciyar Abba tayi fari ganin yadda ‘ya‘yan nasa suke bashi respect aduk inda suka had’u. “Welcome twinnie am glad to see you sai daifa yanzu bama kama kazama bature.” Cewar Sadeeq suna tafiya ajere, Abubakar yayi dariya har suka k’arasa cikin mota suna tsokanar junansu. Kwanansa d’aya da dawowa batare da kowa ya sani ba ya tafi Sumaila kauyen sani, ba  ayiwa kauyan sauye-sauye ba ya nufi gidan malam Hamza direct cikin ikon Allah kuma ya sameshi a k‘ofar gida bayan ya tambaya annuna masa shi. Bayan sun gaisa ne shi duk a tunaninsa malam Sadeeq ne shi kuma Abubakar be nuna bashi bane ya kalli malam Hamza yace.
“Malam INdo kuwa ta dawo?!” Malam Hamza ya kad’a kai cikin takaici yace “Ai malam Saddiqu uwata dai k’arfl da yaji ta gujemu, k’iri-k’iri tak’i dawowa, harma gidan su yaron dazata aura acan sayen sun aiko mun kuma bashi dan idan ba haka bama uwata ba dawowa zatayl’ ba. Wallahi harzuwa nayi da kaina nace mata kabar garin amma tak’i yadda mudawo.”
K’irjin Abubakar ya buga jin cewar an aiko, cikin d’imuwa yace.
Malam wane kauye ta tafi ne? Nidai wallahi inason ganin yarinyar nan tasamu ilmi koyaya ne, idan babu damuwa kuma ka yadda dani kagaya min kauyan da INdo taje na dawo da ita zan samar mata da rayuwa mai inganci da ikon Allah nidai burina ka yadda dani.” “Toh malam Saddiqu na yadda amma dasharad’in sai munje mun sanarwa dame unguwa, shima yasani da kuma aminina malam ‘Dalha..”
”Hakan ma dai-dai ne Malam na gode.” Hannu yasa ya ciro kud’i duba ashirin ya mik’awa malam Hamza ya karba yana ta godiya tamkar zai mai ruku’u sannan yace suje gidan me unguwar. Suna zuwa aka yi komai sannan suka koma gida Abubakar suka gaida Inna bayan sun kwatanta mai kauyan sayen ya koma gida cike da murna. Da dare suna zaune a d’aki Abubakar ya kalli Sadeeq yace. twinnie zaka min rakiya gobe dan Allah.” Zuwa Ina kuma daga dawowarka?!” Cewar Sadeeq Abubakar yayi dariya tare da cewa.
“Wani guri zamuje wajan k’arfe 12:00pm.”
Allah ya kaimu tunda gurin bashi da nisa, kasan dai Qibd’iyya tayi aure ka yaudare ta.” “A’ah twinnie Allah ne beyi ba.” Suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha’wa.
Washe gari suka d’auki hanyar zuwa saye cikin suit d’insu iri d’aya da Abubakar ya taho musu dashi. Tafiya suke tun Sadeeq yana kawaici harya fara magana.  twinnie wai ko katsina zamu je ne naga mun wuce dawanau..?!” ‘ Abubakar yayi murmushi sannan yace “A’a kaidai zuba ido kayi kallo.” Cigaba sukayi da tafiya har suka d‘auki hanyar saye Sadeeq dai yayi shiru idan ya gaji sai ya kira Fateema har yaga sun fara shiga daji da kewaye mugayen ramuka ya kuma yin magana.  twinnine ko kafara sana’aryankan kaine shine zaka fara takaina?!” Abubakar ya kyalkyale da dariya tare da cewa. “A’a ban faraba zuciyata nazo d’auka a garin.” “Tofa.. Waye zuciyar take twinnie??” Abubakar yace “Aisha! Hamza,sadeeq yace what,,,,Abubakar yace i mean INdo malam Hamza.‘ cikin rudewa sadeeq ya sake fadin Whatt………???!”
Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE