MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 13

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 13
“Amman dai baka min adalci ba kasani ko  twinnie?A k’a’ida yau zanje gidan su fatima sabida gobe nakeson wucewa amma kayi min haka, wallahi danasan gurin wannan wayuwayar zamuzo bazan rakoka ba”mtssd”Sanin idan na gaya maka bazaka yadda ba yasani k’in gaya maka sabida ina son muzo tare dakai.” Ne Sadeeq yayi mai banza har suka shiga cikin rugar fulanin, suna zuwa suka ga ‘yan mata yara da manya sunzo zasu wuce. Rabawa Abubakar yayi da motar gefe kasan cewar bazata wuce canciki ba sannan suka fito Sadeeq sai faman cin uban magani yake yi idonsa sanye cikin dark shade shi kuma Abubakar d’an siriri ne nashi fari kal kamar k’ank’ara. Suna Fitowa INdo dake tsakiyar ‘yan matan zasu tafi: kasuwar badume tana ganinsu ta ganesu cikin karad’i tace. “Jakar uban nan,sun biyo ni masifaffun malaman nan.” Kallon sauran abokan tafiyarta ta tayi tana gyara mayafinta tace. “Kowa ya samu sanda zamu k’arasa wajan wad’an can malaman, kawai danace muku kulle kukuma sai ku jibgesu.” Suka ce toh kowa ya juya ya samu sanda harda ita sannan suka nufi gurin suma su Abubakar lokacin sun k’araso ciki sam basu ganeta ba sabida tayi girma ta zama ‘yan mata, lokacin da ta baro sani tana 12years yanzu kuma tana 15years gashi tayi ‘yar k’iba ta kuma canza. Abubakar shine ya taresu yana kallansu yace. “K’annena dan Allah muna neman gidan da lNdo malam Hamza take, wadda tazo daga kauyen sani.”Caraf ta cafe bayan ta rik’e kugu tace, “ga wata nan laflya kuka zo inda nake..?!” Duk suka zuba mata ido Sadeeq dariya da takaici suka kusan kamashi ya kalleta kallo irinna raini sannan ya juya zai koma cikin mota yaji tace. “Wannene kaid’in dacta Habubakar ko kuma malam Sadeeq? Na ganeku rasai.” Ko waigowa beyi ba sabida haushi ita kuma ta kalli Abubakar dake tsaye yana kallonta, sam bega wani aibu a tattare da ita ba yaji zuciyarsa ta sanyaya yanajin tamkar ya rungumeta amma bahali gashi ya gansu da sandina kuma suba shanu ne a taredasu ba reyayi tunanin cewar kiwo zasuje. Cikin sanyin murya yace. “Humaira inason muyi magana dakene, naje munyi magana da mahaifinki sauran ke.” “Allahu akubar kabiran, malam Sadeeq ni ba’a renamin hankali wallahi nan garin yanzu sai nasa su rakaku da duka wallahi.” Ido ya zaro jin abinda take cewa ya fara bin hannayen yaran tare da tuna wata kalma ta bahaushe da yake cewa sarkin yawa yafi sarkin k’arfi, ya d’an kalleta cikin ransa yana tunano ko harsai yaushe ne zata yi hankali. Ya rasa ya zaiyi da su sai yayi murmushi tare da zura hannu cikin suit d’insa ya zaro wallet suka bishi da kallo ya ciro 2k ya mik‘awa wata 
yarinya yace ga wannan kusha alawa. 
Kallon kud’in suka yi sai kuma sukayi baya-baya suna zaro idanuwa, ganin dalla-dallan kud’i yasa lNdo tayi saurin k’arasawa zata fisge Abubakar yayi saurin janye hannunsa tare da kad’a mata kai yace. “A‘a wannan ba naki bane, naki yana gurin Sadeeq sai kin yadda da abinda zan gaya miki sannan zamu baki su suna can dubu ashirin.” INdo ta dafe k’irji tare da ja baya tace, “Dubu ahirin? Toh kaine dacta Habubakar kenan, meyasa kabari aka bawa malam Sadeeq kud‘ina kuma alhalin mugune ba bani zai yi ba..?!” Zai baki amma sai kin yadda da maganar da zamu gaya miki.” Tanajin haka tace “kaltume ku karbi kud’inku, kuyi gaba zan taho daga baya idan na karbi kud’ina.” Karba suka yi sannan suka tafi ita kuma ta yarda icen hannunta tare da goge hannun jikin zaninta, shi kuma sai kallanta yake yi, sam ya rasa abinda ya gani ajikinta yaji zuciyarsa na azabtar dashi, yace. “Toh kinga wani dutse can muje mu zauna in gaya miki abinda muka zo sanar miki.” Ba musu suka tafl sai juyawa take tana kallon Sadeeq a cikin motar, suna zuwa Abubakar ya zauna ita kuma ta tsaya yace. “Humaira zauna mana.” “Karkafa kuma cemin wani humaira hekace wata yarinya e’heee.” ‘ 
“Sunan Mamana gareki shima humairan na fad’a ne sabida babu yadda zanyi, k’I zauna kijini dakyau abinda zan sanar miki, idan baki yadda ba zamu d’auki wata yarinyar anan kauyan mu bata kud’in.” Da sauri ta zauna ya kalleta yama rasa ta Ina zai fara mata bayani yadda zata faminta ta gane manufarsa karta yi mai hayaniya. Zare glass d’insa yayi sannan ya kalli fuskarta sai faman wasa take da k’ananun duwatsu yace. “Humairah kina son yin karatu?“ Kai tsaye lNdo tace mai, “A’a aradu nida zanyi aure.” 
Abubakar ya kuma kallanta, ganin tayi maganar har cikin ranta yasa shi mik’ewa ‘tsaye yace. “Eh ai zakiyi auran amma ki gaya min idan kinason yin karatu kema wata ran ki zama kamar matar gwamna ko shugaban k’asa kuma kema wata ran ki amfanar da bayin Allah 
da kuma ‘ya’yanki wanda zaki haifa idan kinyi aure.” Rufe ido tayi da tafln hannunta wai kunya sannan tace. “Eh toh bank’i ta bakinka ba amma ni bazan yi wani karatu ba haka kurum naje malamai su dinga jibgata ba a‘hhjikina bana banza bane, kuma ma yazan yi da auran saleleh tunda shaura ‘yan makwanni..” Mtwww Abubakar yaja tsaki jin ta kira salele cikin d’an bacin rai yace. “Waye shi salelen? Me gareshi? Ana son fito dake daga cikin duhun kai kina wani sake dulmiya kanki? Kinga humaira ki yadda yanzu mu koma sumaila dake akwai kayan da na tanadar miki sababbi tindaga kan, atamfofi, shaddoji, materials, mayafai takalma, jakunkuna da kayan kwalliya, amma sai kin yadda zaki bimu mu koma can gidan ku…” Shiru INdo tayi ta fad’a cikin tunani, kallonta yayi ganin tayi shiru ya fara addu’ar karta ce 
mai bazata ba murya a raunane yace mata. “Please Humaira talk to me mana.” 
Kallansa tayi jin yayi mata turanci tace “sake gaya min abinda ka fad’a yanzu da hausa k0 da fulatanci sune yarena.” 
“Oh cewa nayi kiyi magana mana, inason jin matsa yarki I told you zaki samu komai idan muka maida ke sani.“ “Kai dacta habubakar kun saba cewa zaku yi amma ni bakwa bani bare ma kuma malam 
Sadeeq”hmmmm. “Humaira wannan karan nine zan d’auki dukwani nauyin abunda kike so, fatana da burina ki yadda mu koma nayi miki alk’awarin yi miki duk abinda kike so indai befi k’arfina ba.” “Harda kayan d’aki idan mun tashi yin aure da salele?!” Ta tambayesa duk da yaji haushi amma be nuna mata ba sai ma eh daya ce mata. “Toh kuwa zan biku amma hemunje mun gayawa baba iro dasu yakumbo talatu.” Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abubakar yace mata. Toh muje.“ 
Jerawa suka yi INdo sai d’an tsince-tsince takeyi yana hanata da haka har suka k’arasa. Tun a bak’in k’ofa ta fara k’iran yakambo talatu tame da d’aurin k’irji tana tambayar. “Lahiya mai sunan uwa.?“ “Anzo tahiya dani gida, ina lawisa da kande suzo muyi bankwana” A gindin bishiya Abubakar ya tsaya yana kallon inda suke rayuwa ya kuma tuno cikin garin kano kam ya tunano garin abuja zuciyarsa ta dira a k’asar Spain. Lallai Allah beyi ko ina dai-dai ba, wani yafika kaima kafi wani sannan ya furta kalmar “Alhamdulillah.” “Ina wanda yazo tahiya dake d’in, karki ce mini wannan ne?” “Aradu baba iro shine, d’an uwan malamin mune a sani.” Tabarmar kaba aka shimfidawa Abubakar ya zauna tare da baba iro yayi musu k’arin bayani da kuma sanar dashi cewar da izinin malam Hamza yazo d’aukarta. Abinciccika aka kawo mai saidai beci ko d’aya ba sannan baba iro yace. “Toh gaskiya bazan baku yarinyar nan ku tafi da itaba, hedai muje tare har garin, idan kuma ka yankamu kaida Allah domin hine mesakayya.” Babu gaddama Abubakar ya amince, aka sanar da mutanan gari lNdo taje ta harhad’a kayanta akayi mata tsaraba da yawa sannan mutane mata da maza suka tafl raka ta gurin mota. “Yakumbo dan Allah idan salele ya dawo kice mihi na tafi amma ya dinga zuwa sumaila muna gaisawa kafin bikin mu kinji.?!” INdo ta fad’a Abubakar dake gaba ya dinga jan tsaki yana jin yadda take k’ara jajjada sak’on da za’a gayawa salele suka k’arasa wajan mota dama tundaga nesa Sadeeq ya hangosu ya dinga kwasar dariya ganin yadda sukayo gungu guda sai tada kura sukeyi, suna zuwa ya had’e rai sukuma mutanen suka dinga fad’in ahe ‘yan biyu ne. 
INdo da baba iro suka shiga gidan baya sannan Abubakarya zauna a driver seat Sadeeq na kusa dashi ya tada motarsuka dinga d’aga musu hannu anayiwa baba iro adawo lafiya. Har suka fito daga surkullen babu me magana sai lNdo datake lissafo wad’anda zata yi kewa, suna hawa babban titi iska ta fara hurata ta A.C ta mirgina kal’ sai bacci har rawar sanyi take yi. ….. 
Sani…Suna zuwa har k’ofar gidan malam Hamza suka tsaya baba lro ya tashi lNdo duk ta cika su da munshari wanda hakan be damu Abubakar ba amma Sadeeq iya kuluwa ya kulu, ta bud’e k’ofarda sauri tana fitowa ‘yan unguwa suka fara cewa. “Ga iNdo… Ga iNdo…!” 
Ta bud’e ido tare da kuma mistsike shi tana dariya, duk wanda ta gani saita fad’i sunansa kafin ta shige cikin gida da gudu tana k’iran Innar su. “Kai INdo yaushe kika dawo?!” Cewar k’aninta shehu yana wankin kayansa, bata kulasa ba Inna ta fito iNdo ta d’areta cikin murna tana washe mata baki. “oh ‘yarnan kina nan da halinki kuwa?
“Tab Inna kenan Ina zeje, yana nan aradu wai ina Nafeesah da Sagiru duk bangansu ba..?!” “Suna waje k’ila dai suntai wani gurin ne, ahe yau zaya d‘aukokijiya malam ke gaya min yadda sukayi da malam Saddiqun.” Cewar Inna INdo tayi dariya bata ma bata amsa ba tace, Inna ina Rukayya kuwa, oh ni INdo tana nan kuwa?!” “Tana nan yanzu ma ‘ya’yanta uku sai kuma wanda zata kuma haihuwa.” 
“Kai Inna yanzu cikin wani gareta kama d’ahare ta saye? Bari naje gidan naganta nikam.” “Haba ‘yar nan daga dawowar ki?!” 
“Eh wallahi Inna ai Rukayya mutuniya tace kinga tunda na tahi ban mance da ita ba.” 
Tashi tayi ta suri takalma tayi waje, a k’ofar gida taga su malam Sadeeq da baban ta amma ta wuce sai tsayawa take suna gaisawa da mutane. Lokacin da su Abubakar suka gama magana da malam Hamza abubakar kasa tafiya yayi domin yana son suyi sallama, k‘ofar gidan Rukayyar ya k’arasa ya tura yaro ya kirata ya kalleta sai faman dashare baki takeyi tana rufe ido yace mata. “Humaira zan tafl gida, Zan dawo jibi insha Allahu karki dinga tafiya yawo idan ba haka ba bazan baki komai ba.” “Ai bazan yiba dacta, ammafa karkak’i zuwa kaji?!” Yace “Toh Humaira Zan tafi amma fa kiyi wanka ranar dazan zo.” Tace “Toh dacta Inajiranka.” Yana tafiya ta koma gidan Rukayya shi kuma ya shiga mota bayan sunyi sallama da malam Hamza da baba iro. Sadeeq yaja mota suka nufi gida. Da daddare suna zaune abin duk ya damu Sadeeq ya kalleshi yana danna laptop yace mai.  twinnie can you tell me why u cared and protect her? I know bawai dan wancen dalilin bane tunda gashi har kana cemin zuciyar kace please tell me.” Ture laptop d’in yayi tare da kwanciya ya sanya hannuwansa ya tallafo kanshi yana kallon fankar sama yace. “Twinnie bazan boye maka ba hakan yasa naje tare dakai muka dawo da ita gida, twinnie I’m in love with her, I can not do anything without her. Ina son ta zama matata, ina son na mallaka mata ragamar rayuwata koda kuwa bata zama wayayyarda nake da burin aura ba.” 
Cikin tsananin mamaki da al’ajabi Sadeeq yake kallon Abubakar jin abinda ya fad’a. Ganin Sadeeq na niyar yin magana yasa shi saurin cewa. twinnie kayi min fatan alkairi, ka kuma taya ni yak’in neman yarda da soyayyar Humaira please and please twinnie.” “Allah ya k’ara dankwan soyayya Allah yasa ayi komai muna nan.” Cewar Sadeeq yana kallonsa, Abubakar yayi murmushi tare da cewa. “Amin twinnie thank you.” Kowa ya cigaba da abinda yakeyi zuciyar Sadeeq fal da mamaki, shi kuma Abubakar tashi 
kaddarar kenan auran lNdo Allah kadiran alaman yasha. 
Washe gari Sadeeq ya tafi k’wara state, a day after Abubakar ya shirya Tafiya sumaila yayi sallama dasu Mama, sannan ya d’auki k‘anwarsu Hawwah ya kaita wani shago yace ta had’a mai kayan kwalliya, tayi-tayi ya gaya mata na meye yak’i tana dariya ta had’a mai komai sannan ya bata kud’i yace tahau napep. Ya wuce a hanya ya tsaya ya shiga wani Boutique ya siyawa INdo wasu tsala-tsalan dogwayan riguna guda biyar da takalma guda uku ya had‘asu da kayan kwalliyar sannan ya wuce sani… 
Hmm ga indo ga dacta muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE