MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 15

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 14
Da sauri ta shiga gidan su Uwani da Maryam na biye da ita lokacin su duk da yaransu sunyi aure,tana zuwa taga Nafeesah tayi d’aya-d’aya da kayayyakin cikin ledar su Sagiru da shehu sai shan sweet da chocolate sukeyi INdo tayi kukan kura tare da fad’awa kan kayan tana yiwa Nafeesah masifa. Dan uwarki wane d’an iskan ne yace idan kin higo ki bud’e min kaya na? Kodan kin rakani sutofes (stupid).”kawai
“Ke INdon nan wallahi masiffiya ce, bamu biyu ya siyowa kayancin ba, ai na san kayan sawar naki ne amma ai daya higa shagon nan ya dawo cewa yayi idan mun dawo mu raba Ke wallahi rintoh gareki.” “Ah Ah Kakan cewa yayi mu raba. ke waima wayake son ya dinga yiwa mutunci? Ni ko keh?” “Oho ba’a sani ba, kuma yasin komai rabahi za’ayi dai-dai.“ Sagiru daya hango wata alawa k’ark’ashin k’afar INdo yayi wufya d’auke tare da barewa yasa baki da sauri dan karta juyo yana cewa. “Wallahi kuwa Nafl karki sake ta cuceki a raba shi ki fara d’auka.” Da sauri cikin bala’i wanda har rufe mata ido yake yi tace, “Toh munafiki algungumi zugata, wallahi hekaja ink’i rabawar banza kawai…“ “Oho dai a raba mugani.” 
Ya kuma fad’a cikin tsokana tayi mai banza tare da maida kayan dajakar kayan kwalliyar ta cikin leda sannan ta kalli Nafeesah tana hararart tace. “Ki zabaa raban Allah za’ayi ko kuma raban gaskiya kike so..?!” Nafeesah ta murgud’a baki tare da cewa. “Rainin hankali, toh raban Allah da ma‘aiki zaki yi mana babu wani rabon gaskiya ‘yar latsi..!” Suna kallonta saida ta fara ware komai daban sannan ta kwashi me yawan ta turawa Nafeesah kad’an tace. 
“Gashi nan.” Nafeesar ta kwaso wata uwar ashariya ta zubeta sannan tace. “ldan kin isa kice ba uwatace ta haifeni ba kanbala’i…” Inna na kallonsu tun shigowar INdo k’irjinta ya fara bugawa kanta yana juyawa ganin yadda ‘yar tata tadawo sabuwa, Allah yasa dai ba wani abun yayi mata ba k0 yake son yimata ya fara kowa mata shiga masu kyau. Duk fad’an da suke yi ta kasa cewa dasu uffan bakinta fal addu’a da fatan Allah ya cire mata wasi-wasin da take yi akan lamarin Abubakar. “Gaskiya kema INdo kinso kanki dayawa, taya ance kiyi rabo tsakani da Allah sai kiyi yadda kikaga dama dan mugunta…” Cewar Maryam Aliyu tana bawa d’anta nono. Can Sagiru ma yace rabo beyi ba Nafesah karta yadda ita kuma Uwani tana bayan lNdo dankar sai an gama fad’an ta hanata komai. INdo ta matse nata tasa a tsakanin cinyoyinta tare da cewa. 
“Saida na tambaye ki rabon Allah ko rabon gaskiya kika ce na Allah toh ai Allah baya rabawa dai-dai sai dai yabawa wannan meyawa ya bawa wani kad‘an, alal misali kinga ai Maryam ke mijinki yafi na uwani kayan gona kuma dacta Habubakar shima yafi baban mu kud’i ko ba haka ba..?!” 
“Oho miki banza muguwa kuma bari ya dawo saina gaya mihi.” “Sai ki fad’a ko’ajikina wallahi.” Ta fad’a tanajan tsaki. d’aya-d’aya ta bamawa su Uwani, babu wanda beji haushinta ba sabida ko ‘ya’yansu bata bawaba suka tashi suka tafi. Kallon Inna lNdo tayi ganin tayi tagumi yasa tacewa. ‘ “Inna kizo kiga kayan da ya kawo min, ya kaini aka sani a inji mezafl aka gasa min kai aka dinga yafamin wasu abubuwa akaina Innajibi yadda gahina ya zama..” Tana magana tana bud’e kanta, gabaki d’ayansu suka kalleta baki bud’e cikin mamaki lnna tace. “Nahiga uku ni Maryamu ‘yarnan kanki nekuwa?” “Hehehe kaji Inna da wani batu, toh inba nawa bane jikin kuma nawaye kema dai.” “Tab lallai lNdo anyi klin kinga yadda aka nannad’a miki gahinki kamar na indiyawa.” Kuwa
Cewar sagiru yana kwakulo chocolate d’in daya mak’ale jikin jajayan hak’oransa. Banza tayi mai taci gaba da nunawa Inna kayayyakin daya siyo mata, Inna tayi godiya cikin rashin nuna kyashi ga uwa a wani bangare da wasu ‘ya’yan keyi INdo ta d’akko wani flat shoe tare da janyo k’afar Inna tana cewa. “Inna saka wannan mugani kozai yi miki.” Tana saka mata kuwa yayi cif-cif a k’afar Inna INdo tayi dariya tare da fad‘in. “Inna k’afarmu d’aya Ashe, toh nabar miki wannan innata kema kidinga sakawa idan zaki unguwa ko kauyen ku.” Da sauri Inna ta zare takalmin daga k‘afarta tare da rik‘o hannun INdo tace. “A’a ‘yarnan barshi na gode miki Allah yayi albarka amma bazan k’arba ba, sabida ke aka bawa tayaya zan k’arbar miki ya gansu ajikina a’ah.” “Toh danya gani kuma Inna heme? Zece kibahi ne? Kawai ki k’arba nina baki ai yariga ya siya min.”Ganin ta dage yasa Inna ta k’arba tare dayin godia sannan INdo ta shiga da kayanta cikin d’aki ta zuba a cikin Ghana must go d’inta. Tashi tayi tafita zuwa gidan Rukayya, duk inda tayi mutane sai sunyi mata magana, maza kuma su tsayar da iya amma sai hura anci take kanta a d’age tana zare alawa tana sha hankalinta kwance duniya tayi mata sabunta jinta takeyi tamkar akan iska. 
Qarfe 2:35pm ya fito daga office d’inshi, sauri yake yaje gida yayi wanka dan yana son zuwa sani a yau. Da sauri yafita yana zuwa gida wanka yayi tare da shiryawa cikin k’ananun kaya white jeans da black shirt me dogwan hannu ya d’ora facing cap dama ya riga yayi sallah yaci abinci a office dan haka ledar d’in kunan daya bawa Hawwa ta d’inkawa lNdo su ya d’auka yafita sai bulala k’amshi yake tamkar anyi Garin turaren. Passenger seat ya ajiye kayan sannan ya tada motar ya wuce domin yau kwanansa goma sha hud’u rabansa da kauyan Sani, yayi missing d’in INdo ba kad’an ba domin babu waya a hannunta. Yana shiga unguwar yara suka yayyame shi yayinda suke ta mik’a mai gaisuwa, yau kam suna da yawa harda matasan samari ya ciro 3k ya basu yana mamakin abinda suka maidashi tamkar wani kansilan su ko chairman d’insu. Shehu ne ya k’arasa jikin motar yace. “Bari a k’irata tana gidan k’awarta.” 
Abubakar yayi murmushi tare da d’aga kai sannan shehu ya ruga da gudu gidan Sahura kokafln yaje Ashe har an gaya mata suka had’u a hanya shehu na gaya mata irin kyawun da Abubakar yayi yau ita kuma ta k‘agara tagani hakan yasa ta yin gudu. Ta glass ya hangesu ya zaro idanuwansa yana kallonta ganin tun rigar datasa ce a jikinta tayi jirwaye su manja bak’in tukunya ne gashi nan dai ya kifa kansa akan sea-tearing. Ashe babban aiki ne a gabansa na aniyar ganin INdo ta waye, toh meye amfanin wad’ancen kayan na gurinta gashi yau harda k’aro mata kala shida duk atamfofi yasan ma aikin banza 
ne yanzu ya zaiyi. Kafin ya nemo amsa yaji tana mai magana a hargitse sai uban nishi takeyi ya d’ago da kansa a hankali tare da zuba mata fararan idanunshi akan nata yana lumshewa cikin wani irin salo. Bah k’aramin kyau da had’uwa taga yayi mata ba taji k’afarta na rawa zuciyarta na harbawa muryarsa a sark’e yace mata. 
“Humayrah look at you, da alama yau ko wanka bakiyi ba a matsayinki na ‘yanmata wadda ta kusa yin aure jibi tun rigar last week meye hakan..?!” Tana wasa da belt d’in rigar daya fara zarewa tace. “Wallahi dacta bansan zaka zoba yau bane danayi kwalliyar.” Tsaki yaja d’an k’arami sannan ya fito daga cikin motar yajingina yana kallonta. Tundaga sama har k’asa take binsa da kallo yace mata. “Dena kallo na.” Toshe baki tayi tana dariya jin abinda ya fad‘a ashe yana kallon yadda take mai ya kuma cewa. Tunda naga alamar bakya son yin wanka toh zan canza ki na koma kan Nafeesah domin ta fiki wayewa. Ko kuma na dena zuwa tunda abin naki haka ne.” 
“Wayyo dacta dan Allah kayi hakuri wallahi ko hekaran jiya da salele yazo nayi kwalliya ka tambayi inna kaji, kaima fa dan bansan zaka zo bane.“ Tayi maganar tamkar zata rarume shi dan duk ta rud’e jin cewar zai dena zuwa. Komawa yayi ya zauna sannan ya kalleta yace. 
“Toh jeki kiyi wanka ki kuma saka sabuwar riga ina nan Ina jiranki.” Da sauri ta shiga gida, kafin minti biyar sai gata cikin sabuwar riga yellow da kwalliyar gloden ajiki sai hoda data shafa da lipstick ta fito duk dan kada ya tafl. Kallonta yayi tare da yin murmushi yace. Toh koke fa, shiga muje na siyo miki wasu abubuwan ina Nafeesah ta raka mu?!” Cikin sauri INdo tace “Bata nan taje kai nik’a muje kawai basai ta rakamu ba.” Toh shikenan.” Ya fad’a tare da shiga motar ya bud‘e mata ta shiga yaja suka tafi yana janta da hira cikin salo irinnashi. Cikin gari suka shiga yayi mata shopping abubuwa na buk’ata su brush, makilin, sabulun wanka na wanki, mayukan gashi turaruka, pad, cotton balls, panties dadai sauran su sannan sukajuyo gida. Abubakar ya gargad’eta sosai akan yin kwalliya sannan ya bata d’inkunanta INdo ta dinga zuba mai godiya kamar bakinta zai tsinke sannan suka yi sallama zata fita kawai yaga k’asanta duk ya Gaci yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa. 
Humaira kinsan al’adarki tazo?!” Da sauri ta kalli bayanta domin wannan shine karo na biyu data taba yi, na farko a saye yakumbo talatu tace mata kowace mace tanayi sunansa al’adah kuma inyaxo ba’a sallah ba’a taba kur’ani. ’ Tace masa “Ban saniba yasin amma ba komai yakumbo ta gayan yadda zanyi.” Hannunta ya janyo karo na farko da hakan ya taba faruwa, ledar hannunta ya karba tare da zaro pad yaciro guda d’aya yace. “Kinsan wannan.” lNdo ta girgiza kai yayi murmushi tare da zaro pant d’aya ya nuna mata yadda zata yi yace. “Yanzu idan kinje gida saiki saka a haka kinji? Duk sanda tajik’e saiki cire kiyar kisake wata bye-bye.” Ya fad’a yana d’aga mata hannu, bud’e k’ofar tayi da ledoji a hannunta ta fita shi kuma ya janyo da d’ora kyalle agurin data bata mai ya bar unguwar. 
Bayan wata biyu. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE