MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 16

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 16
Zaune suke a cikin ajin wanda yawancin su duk matan aure ne da alama makarantar manya ce ta yak’i da jahilci. Gefe guda kuma INdo ce ta duk’ufa tana kallon wani littafi na alifun ba’un sai faman mamul-mamul takeyi da bakinta da alama sotake tasan su ta kuma gane su a haka wata dattijuwar malama ta shigo hannunta rik’e da littattafai idanta sanye da glass fari ta samu guri ta zauna. Bayan ta kammala biya musu littafin ahkdari ta zauna tana kuma yi musu bayani har tazo tana yi musu sharhin isra‘i da mu’iraji tana basu labarin ire~iren matan da annabi (s.a.w) ya gani a cikin wuta tace. “Manzon Allah sallallahu alaihi wa’sallam yana cewa aure sunnah tane duk wanda baya son aure baya tare dani, baya da alkairi mutum ya zauna yayi ta kace nace da mutum musamman idan bata fuskar addini ba. Lokacin da ma’aikin Allah (s.a.w) ya dawo daga isra’i Nana Fateema da megidanta sayyadina Aliyu suka je gurinshi suka tarardashi yana kuka suka tambaye shi menene yasanya shi wannan kukan, sai ma’aiki yace, yaga mata dayawa daga cikin al’umarsa anayi musu nau’i-nau’in azabobi kala-kala. Yace yaga wata mata an d’aureta d’auri irinna azaba da gashin kanta, _itace mace baliga wadda take barin gashin kanta a waje dan wasu sugani_ ya kuma ganin wata an zaro harshenta an nannad’eta dashi, yace _itace wadda take d’aga murya idan tanayiwa mijinta magana duk yadda taga dama, duk abinda zai mata ta kushe,ta dinga ganin be’iya yi mata komai ba_ wata kuma an tsananta d’aurin nononta, _itace wadda bata kula da shimfid’ar mijinta, bata bashi hakk’insa, ko zatayi saita garashi dan taga yana buk’ata, sannan tana bin wasu mazan a waje_ wata kuma aka maida fuskarta ta alade jikinta najaki. _itace wacce ta kassance munafuka, annamimiya me d’aukar magana ‘akaiwa wannan taje can ta kunsa wata maganar_, ita ake yiwa wannan azabar..” ‘ Akwai nau’ika kala-kala daya sanar dasu wanda ya gani, anan gurin kowacce tasan abinda takeyi na rashin dai-dai dan haka sai kowacce taje ta gyara wanda takeyi kafin tilon ganyenta ya bushe ya fad’o ma’ana kafin ta koma ga wanda yayita. Akwai masu iyaye a raye babanki neko Mamanki kiyi musu biyayya akan abinda besabawa shari’ar musulinci ba domin saba musu babban laifine a wajan Allah dama cikin rayuwar mutum gabaki d’aya, Allah yayi mana kyakyawan k’arshe..” ‘ Duka ajin suka amsa da amin sannan malamar ta fita, kasan cewar ajin duk matan aure ne mutum uku ne ‘yan mata yasa lNdo bata irin wannan haukan gashi basa kulasu ita kuma karatun ba wani shigarta yake yi ba saidai tana matuk’ar san tarihi domin jinta takeyi tamkar agabanta akeyi wasu abubuwan. 
K’arfe shabiyu da rabi aka tashesu gaba d’aya makarantar hijjab suke sawa kuma kala d’aya shine ya zama kamar uniform d’insu. Yau kwanakinta talatin da biyar da kawota makaranta babu abinda za’ace sai hamdala domin ta fara iya yin sallah sai dai sam kwakwalwarta bata d’aukar hadda, a gurin za‘a biya tanaji amma kuma ya zauna a cikin kwakwalwar ne wahala. 
Tana fitowa itada k’awayen da tayi sababbi Zainab da Hadiza suna maganar littafin k’awa‘idi sai ga me mashin d’inta wanda Abubakar ya samar mata yazo d‘aukarta, shine yake kawota ya kuma dawo ya d‘auketa duk sati Abubakar yake bashi kud’insa sukayi sallama ta hau suka tafI. 
Zama tayi a cikin d’aki suna hira da Inna ita kuma tafito da littafan tana kallonsu taja 
tsaki tare da fad’in. “Wallahi Inna karatun nan badai wahala ba, ni wallahi duk makarantar ta iheni dacta Habubakar ya takura min.” Ta k’arasa maganar tana turo baki tare da yatsina fuska, Inna tayi dariya tace. “Haba ‘yar nan ki dubafa kigani zuwanki makarantar nan yanzu sallah bata wuce ki, sannan kina zaune a gida kina k’ok’arin yin alifun ba’un d’inki aini kam naji dad’i wallahi.” “Tab lallai Inna, nifa ma wallahi inajin film zan higa dan wallahi dana fara Inna zaki ganni da narkekiyar mota wadda tafima ta dacta.” . Tafad’a cikin nuna son yin abinda tace, din Inna tace, “Ahir d’inki da wannan sana’ar, yanzu keko cewa akayi kihiga ai bakyaje ba sabida ma tsarinku ba d’aya bane su sunfiki kud’i da karatu.” “Toh Inna bakiga ‘yar autah bane me sa bakinjanbaki, yanzu kina nufln kice min itama tafini kud’i ko iya film d’in…?!” “Oh ni maryama nace bana son kiyi amma kina dagewa.” “Toh kiyi hakuri Inna dan yau anyi mana magana akan yiwa iyaye abinda basa so,malama Hansa’u tace me sabawa iyaye idan ya mutu Allah ze k’onashi na denayi miki na fasa higa film d’in.” Daga nan suka cigaba da hira duk ranar asabar, lahadi da litinin INdo na makaranta kuma alhamdulillahi duk sanda taje ta dawo akwai abinda zata d’an tuna musamman idan anayi musu k’arin haske akan littattafan. Shi kuma Abubakar idan yazo zai kuma sanar da ita abinda shima ya sani da haka lNdo ta fara gane fari da bak’i sannan gashi Abubakar yana iya k’okarinsa wajan ganin yayi mata abubuwan zamani wayace kawai yak‘i siya mata sabida yasan ba k‘aramin d’auke mata hankali zatayi ba shi kuma yana son yaga ta samu wani abun a Cikin addininta. ‘Bayan shekara d’aya DA rabi’ 
Waya ce kare ajikin kunnansa yana ‘ta faman cike-ciken files sai faman murmushi yake yi sannan yace. twinnie na riga na gaya maka bazan samu damar zuwa gidan su Fateema ba gobe sabida akwai inda zani, nifa Fateema ma ta rainani wallahi ko ta d‘auka kaine babba dan cewa tayi min wai wasan k’anin miji ta farayi dani.” Sadeeq yayi dariya tare da cewa. “My sweet heart kenan ai tayi min dai-dai kasan wayayyen mutum gashi dama ta shiga college abin ya kuma k’aruwar mata Ina son Zarah twinnie.” Abubakar ya tabe baki tare da cewa i see. Yanzu dai sai goben idan ka dawo ma had’u nima idan naje wajan babyna zan baka ku gaisa da ita.” “Okey no problem Allah ya kaimu.” Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayaryana kewar d’an uwansa, har tsawon shekarar nan Sadeeq besan Abubakar yana tare da INdo ba domin duk iya hutun da zaiyi a gida baya taba gigin nuna mishi dan ko wayarshi gallery d‘insa password ne ajiki bazaka taba tunanin ma cewa yana ajiye hoton mace a cikin wayarsa ko laptop ko wani gurin ba sabida iya taku da d’auke kai irin nasa. Washe gari Sadeeq ya dawo ranar raba dare sukayi suna hira. Da gari ya waye su Mama da sauran yaran gidan anata shirye-shiryan zuwan budurwar Yaya Habu domin a ranar yake son kawo INdo gidan su ganta itama taga ‘yan gidansu. ‘ 
Sam Sadeeq besan lokacin da Abubakar ya fita ba, sai shiga d’akin yayi ya tarar da k’amshin turarensa, wanka yayi ya kwanta tare da janyo waya ya k’ara Fateema lokacin sun fito daga lecture around 2:45pm. 
Abubakar kuwa yana shiga kauyan Sani yayi parking a k’ofar gidan su indo,malam Hamza ya fito suka gaisa sannan yace. 
“Ai uwartawa tace idan kazo kajirasu su dawo taje gidan kwalliya, nace yanzu ita kwalliyar ce bazata yi ba sai anje har cikin garin sumaila. Wai ai waccan tafi kyau nace toh Allah ya kyauta.” Murmushi Abubakar yayi yana shafa k’eya tare da rissinawa yace. “Ai babu komai baba zanjira.” Fita malam Hamza yayi yana ta shiwa Abubakar albarka yanajin aransa zai iya bashi duk abinda yake so indai yana dashi burinsa ma a yanzu kawai yaji Abubakar d’in yace yana son INdo amma yayi likimo ko ita bata taba furtawa kalmar ba sai ‘yan gidan su daya dama da zancen Aisha budurwarsa. A bangaran INdo kuwa tunda ta fara gane kyautatawarAbubakar da karamcinsa a gareta da irin yadda yake nuna kulawarsa gareta yasa ta mallaka masa zuciyarta gabaki d’aya, ta sallami salele jira kawai takeyi taji Abubakar yace yana sonta amma hakan ya gagara, gashi zuciyarta ta riga ta mutu akan sa dan ji takeyi tamkar ta fad’a mishi sai dai yanzu tana da kunya dan a makaranta ana gaya musu cewar kunya adon macene duk macen da batada kunyar gayawa namiji abu toh k’imarta zubewa take yi kuma bazai sota ba hakan yasa ko abu take so yanzu bata iya gaya mai saidai ta hak’ura. 
Abubakar na zaune cikin mota ya ziro k’afarsa waje yana danna waya kamar ance ya kalli gabansa yaga su INdo da Nafeesah suna tahowa cike da nutsuwa tamkar basu ba. “Masha Allah.” 
Yafurta a hankali yana yana me binsu da ido. Har k‘asa suka tsuguna suna gaida shi ya kasa amsawa INdo sai kallonta da yakeyi. Sanye take cikin les Orange da ratsin green ajiki ta yafa mayafi green tamkar ranar da ake sanyata a alalle, wuyanta yasha sark’a tasa d‘ankunne yatsanta da zobe sai k’amshin turare sukeyi yace cikin fara’a. “Aishatul humairah da my sweet sis Nafeesatu kunyi kyau.” Nafeesat tace, “Kai Yaya Abubakar ai kafimu nidai bari na shiga na sake takalmi.” Tayi maganar tana mik’ewa daga tsugunnan lNdo tayi saurin riko hannunta tare da mik’ewa suka shige gida ya bita da kallon mamaki ganin yanzu kunyar da take nuna Mai tayi yawa ya kad’a kai yanajin wani mugun dad’in yanayi yana ratsa shi. 
Suna shiga ba dad’ewa suka fito domin sunsan su yake zamanjira, Inna tayi musu fatan alkhairi da addu‘ar Allah ya dawo dasu lafia. Yana jingine jikin mota suka fito a hankali ya juya yana kallon INdo suka yi four eye’s ta sakar mishi murmushi da fararan hak’oranta daya kaita asibiti aka gyara mata su lebanta yasha’ red janbaki ta bud’e gidan gaba ta zauna tare da kawar dakai tana kallon k’ofar gidan su. Shima shiga yayi yana cewa Nafeesah, “Zamu tafi mubarki fa.” Tayi saurin fisge hannunta daga rik’on da shehu yayi mata yana bata sallahun abinda zata siyo mai idan sun shiga cikin kano. A hankali ya dinga tafiya har suka fita daga sumaila sannan ya fara gudu dan ayau zai dawo dasu, suna ta hira wanda yawanci akan makaranta ne data ke zuwa lesson sai dai abin ayi addu’a kawai amma INdo kam bata fahimtar turancin da akeyi sai ‘yan k’ananun words 
wad’anda basu da wahalar rik’ewa. ‘ A k‘ofar gate d’in gidan su ya tsaya, ba wani gidane had’add’e ba sannan kuma ba wai gajari bane dai~dai magidanci me rufin asiri da kuma kwanciyar hankali. Suna tsayawa k’irjin INdo ya fara bugawa taji kamar bazata iya shiga ba Nafeesah ta fito INdo ta kalleshi kamar zata yi kuka ya sakar mata murmushi tare da cewa. “Ya aka yi naganki haka?” “Yaya Abbakar jinake inajin tsoro.” “Oh toh ai bama cinye mutane kifito mu shiga.” Dakyar INdo ta iya fitowa ‘yan layin sai kallansu sukeyi suka shiga parking spaces sunzo wani d’an corridor yajanyo hannunta tayi saurin kallansa ya kai fuskarsa saitin tata kamar zai yi kissing d’inta yace. “Idan kina yin haka su Halima zasu rainaki, ki saki jikinki.” 
Ya fad’a tare da sakin hannunta, Nafeesah kuwa hartakusa shiga ciki sannan ta tsaya suka k’arasa sannan Abubakar yayi gaba sukuma suna bin bayansa. INdo kuwa abinda yayi mata ba k‘aramin sake tsuma jikinta yayi ba hakan kuma yasa ta fara mai wata fassara domin a makaranta ana gargad’in su akan taba namijin da ba aure kukayi ba. Da gudu k’annansa suka fito suna musu oyo-yo suka rungume INdo suna cewa. “Yaya Habu itace k0?!” Ya dinga d‘aga musu kai yana murmushi yadda INdo da Nafeesah bazasu gani ba.A k’atan falon gidan aka sauke su an baje musu kayan abinci dana sha kala-kala lNdo kuwa kamar ta nutse cikin carpet d’in da aka malale fa’lon dashi. Su Mama da Umma suka fito su lNdo suka gaidasu har k’asa sannan suka huta k’annan su Abubakar sukayi ta janta da hira suna jefo mata turanci haushinsu ya fara cika ‘ta domin baganewa takeyi ba su kuma a tunaninsu kunya ce take hanata yin magana basu san duk taci ubansu a surutu ba. Sun jima kafin su sauka zasu ci abinci domin tunda Abubakar ya shigar dasu ya koma d’akinsu ya tarar Sadeeq sai shak’ar bacci yake yi da alama ma ko sallan la’asar beyi ba Abubkhr yace. twinnie ka kashi kazo mu shiga ciki gashi na kawo maka wadda zan aura kugani.” Da sauri Sadeeq ya mik’e cike da mamaki yace. “Are you serious?!” Yap tana ma ciki gurin su Mama.” Sadeeq yace “wai kana nufin kace min zuwa kayi ka d’akko ta, kuma babu wani labari?!” Abubakar yace “Ya daman Ina sonayi surprising d’inka ne Ya nagani toh bari naje nayi sallah sai na shiga, nasan ko wacece wannan toh ta had‘u and degree nawa gareta  twinnie?”ldan zaka shiga ka gani toh idan kuma labari kake so toh kaci gaba da baccinka.” “A’a zanso ganin matarka mana  twinnie Ya fad’a yana shiga toilet dan shi a tunaninsa Abubakar ya manta dawani batun lNdo. Saida ya watso ruwa yayi sallah yana idarwa Abubakar na shigowa Sadeeq d’in ya zura kaya sannan suka nufi cikin gidan, tun daga kan takalma Sadeeq yasan budurwar d’an uwan nasa ta had’u suka shiga tare dayin sallama Sadeeq ya zauna kan kujera ita kuma INdo ta d’an juyo ta kallesa suka had’a ido sam Sadeeq be ganeta ba har ta kaidashi sannan Abubakar ya kallesa cikin sign ya cewa Sadeeq. “Ya tayi…?!” Sadeeq yajijjiga kai yana kallon gefen fuskar lNdo yayiwa d’an uwan nasa alamar yes yana kashe mai ido d’aya. Dariya Abubakar yayi ganin be ganeta ba yace. Aisha ce fa student d’inka ta sumaila kauyan Sani Tsefawa secondary school, idan baka gane ba toh lNdo malam Hamza ce…” 
Sadeeq dake zaune sai gashi a tsaye yana mata kallon mamaki. Sai yanzu ya gane domin ga fashin gushinta nan sannan ya fara tuna kamanninta cikin kwakwallawarsa zuwa idanunsa cikin tsananin mamaki yace ….. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE