MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 17

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 17
“Wallahi kuwa itace, lNdo malam dama zaki iya zama haka? lkon Allah da….” Cikiin sauri Abubakar yayi magana ranshi a bace ganin yana neman kwance mata zani a kasuwa yace,  twinnie ya isah haka ko ka manta matsayinta a gurina ne..? Kake neman cin zarafinta.” Sadeeq ya karasa wajan Abubakar tare da dafa kafadarsa ta hagu yace. “Oh sorry  twinnie ba nufina kenan ba abinne ya daure min kai.” Jin-jina kai Abubakar yayi yana kallon yanayin lNdo yaga ta cukume ta kasa boye fushinta sai faman cizon lebenta takeyi na kasa tana murde kasan mayafln jikinta ya kalleta yace. “Humaira zo muje kiga wani abu.” Kamarjira takeyi yace taje ta mike suka flta lokacin Sadeeq na tsaye a parking space tsananin mamaki sun addabi zuciyarsa sai gasu, lNdo na hangoshi ta karasa gurin Abubakar ya bi bayanta. Tsayawa tayi tana kallon Sadeeq cikin salon raini tace. “0h malam Sadeeq kayi mamaki ko? Toh aishi dama Allah ba yadda bayayi da bawansa nasan baka taba kawowa ranka cewar zaka ganni a makamancin haka ba sai gashi ta silar d’an uwanka.””Hakane Aisha nayi mamaki kuma har yanzu ina kanyi, shin wace school kike yanzu.?” Ya tambayeta ta yatsina fuska tare da gyara mayafl tana gyara zaman dankwalinta tana son cewa, ba zamu iya magana anan ba da turanci dan ta bashi mamaki amma ta kasa tana dai danjin alamu-alamun zata iya amma batason ko gwadawa ne dan karyayi mata wani kallon (We can not talk here) tayi mata wahala kawai ta matse tace.
“I dant talk.” (I don’t tell you) Suka kalli juna Sadeeq da Abubakar fuskar Abbakar a hade ganin haka yasa Sadeeq girgiza kai yana kallonta yace. Oh good Allah ya bada sa’a, Ina su Innar ku da malam..?!” INdo tace “Kalau suke duk suna gaihe ku.” Tayi maganar tana matsawa kusa da Abubakar,murmushi ya sakar mata itama ta mayar mai sannan tace. “Kazo ka maida mu gida Yaya Abbakar dare nayi.” INdo akwai dadin murya saidai ta kasa dena sh da hi musamman idan tana magana cikin fushi. “Toh kuje ku shirya sai mun fara zuwa gidan su budurwar Sadeeq daga can sai mu wuce.” Abubakar ya fada yana kallon fuskarta, wucewa tayi ta koma ciki shi kuma Abubakar ya gayawa su Mama cewar zaije ya maidasu. Nan fa kowa na gidan ya fara kokarin flto da abinda zai yiwa lNdo kyauta dashi baga kananan ba baga su Mama ba, haka suka cika lNdo da Nafeesah da tsaraba kala-kala. 
 Fita suka yi duk ‘yan gidan suka rake su mota anayi musu fatan sauka laflya. Sadeeq ne yake tukin yayin da Abubakar ke kusa dashi su kuma su lNdo suna baya har suka karasa gidan su Fateema, waya yayi mata dama dawowarta kenan daga gidan suna ta raka Ummanta, fitowa tayi lokacin anata kiran magrib INdo ta kalli Fateema itama Fateeman ta kalli INdo kowa ya fara sake-saken abubawa a cikin ransa. 
“My Zarah ga girlfriend din twinnie nan kusan juna bari muyi sallah tukunna.” Cewar Sadeeq Fateema ta kamo hannun lNdo tana cewa, 
“Okey My Dear sai kun dawo, shi yasa naga mutumin ankasa an tsare ashe-ashe.” Tayi maganar tana kallon Abubakar ya galla mata harara tare da cewa. “Whatever dai please take care of her, if not.. Hmmm.” Dariya Fateema tayi INdo kuma ta bita da kallo, oh itakam taji abinda yace tunda gashi tana dariya ita kuwa please d’in kawai taji amma raguwar duk bata ganeba shi kuma Sadeeq ya zauna saman motar kafln yace. Ki kawo mana ruwan alwala karmu rasa jam’i.” Jan hannun lNdo tayi suka shiga Nafeesa na biye dasu, a falo suka zauna Fateema na zuba ruwa a buta tanayiwa Umma bayani kasan cewar itama alwala take a gurin. Bayan takai musu ta dawo suka gaisa da INdo ta kawo musu juice da cin-cin a cikin wanda tayiwa Sadeeq d’inta tsaraba domin ba karamin so itama Fateema takewa Sadeeq ba kowa yasani tana mugun sonshi. Kad’an suka ci wai na ‘yan birni karsuci da yawa duk da cewar yayi shegen dad’i amma haka suka hakura, suna Idarwa Sadeeq yayi mata waya cewar su fita zasu tafi. 
A bakin mota suka tarar dasu banda ban-bancin kayan jikinsu da babu wadda zata gane waye nata, suka karasa Fateema ta kalli Abubakar marainin wayon nata tace. “Toh gata na dawo da ita, kaga har ‘yar kibama saida tayi a gode min.” Murmushi yayi tare da zagawa drive seat ya zauna yana cewa. “Tayaya zan yadda bayan ni a yadda na baki haka na kuma karba, anyway thanks amma kad’an.” Tayi dariya su INdo suka shiga mota bayan sunyi Sallama da Fateeman, a bakin titi suka sauke Sadeeq ya kalli lNdo itama ta dago ta kallesa tana faman had’e rai dan karma yayi mata turanci sai taji yace. “Aisha sai yaushe?!” Ta sauke numfashi tare da cewa, “Sai wata rana kuma.” “Okey please send my regards to your parent.” Mtwwww taja tsaki mai karfl cikin kufala tace. “ldan bazakai Hausa ba kayi gaba ai bada yaren annabi kayi min magana ba.” “Lallai Aisha ni kike gayawa maganar nan?” Sai tayi mai da fulatanci itama shi kuma yayi shiru dan shima baji yake ba ta kallesa tace. “Ko bakaji abinda nima nace ba? Toh duk sanda zaka ganni kayi min wani turanci nima henayi maka wanda na iya ai kowa Allah ya tsaga ya bahi.” Juyawa Sadeeq yayi yana taran napep yana mamakin lNdo, wato yanzu ta koyi rainin hankali gashi yagano cewar tanada dauke kai akan abinda beshafe taba amma idan ka shiga nata zata yimaka rashin kunya duk girmanka. “Humairah dawo gaba.” 
Abubakar ya fad’a ba tare daya juyo ba, futowa tayi ta koma kamar yadda ya umarce ta. Kallonta yayi ita kuma tana gyara rigarta yaja motar suka tafI. Tun suna hira dashi da Nafeesah hartayi bacci, sai da yayi nisa sosai sannan ya gyara murya yace. “Humairah meyasa kikewa Sadeeq rashin kunya..?!” Banza tayi Mai sai kunkuni takeyi ya kuma yin tambayar tayi mai banza sannan yace. “Baki ga dan uwana bane? Kuma bakiga ta dalilinsa nasanki ba meyasa kikai mai haka.” Tunda suka saba da juna bata taba jin haushinsa ba sai yau, Allah kuma ya kimsa mata yin magana cikin taushi dan da wani ne kila da  sun kwashi ‘yar kallo tace. “Duk babu wanda yaflku sanin wacece lNdo daga iyayena heku, meyasa hida yasan bajin turanci nakeyi ba amma heya dinga yimin, wannan ai izgllanci ne. Kuma malamar mu a islamiya tace mana, komai na Duniya jarabawa ce haka tace mana lafiya da Allah ya baka jarabawace rashin Lafiya ma haka,idan Kud’i Allah ya baka himajarabawa ce hakama talauci, Ilimi idan Allah ya baka jarabawa ne idan bebaka ba himajarabawa ce, aure jarabawa ne rashinsa ma haka, amma himeyasa yake min haka kuma yasan ban iya ba? himeyasa baka yi mihi magana ba heni…?!” Shiru Abubakar yayi yana tuki, lallai wannan kadai yaci ace angodewa Allah tunda har 
lNdo tasan shi. Murya a sanyaye yace mata. “Haka ne kiyi hakuri.” Cigaba da tafiya sukayi har saida suka shiga garin Sumaila yayi parking akan kwanardazata kaisu kauyen Sani ya kalleta ta kalleshi bayan ya kunna kwan cikin motar yace cikin wata irin murya. 
“Humairah kina sonah..?zaki iya aure na…?!” INdo tayi saurin rufe fuskarta da gyale tanajin wani farin ciki da annashuwa suna yawo aduk wani sashe na jikinta. Murmushi yayi shima yanajin tamkar an d’auke mai wani gungumeman abu aacikin kirjinsa ya kuma tambayar ta lNdo ta d’aga mai kai alamar Eh sannan ya furta kalmar Alhamdulillah. “Thank you Humairah Ina sonki so me tsanani, Zan kula dake iya gwargwadon iyawata, zan kare duk wani hakkinki daya rataya a wuyana zan biya miki shi sannan zanyi iyayina wajan ganin kin cigaba da samun llimi ta kowacce hanya thanks again I love you.” Tunda ta rufe ldo bata bud’e ba harya gama magana, ganin haka ne yasa shi riko hannunta ta fara kokarin kwacewa murya a sarke yace. 
“Idan kina son na sakar miki hannu sai kin bude fuskarki.” Kada mai kai tayi sannan kuma taki bud’ewa, ganin dare nayi mai ne yasashi sakar mata hannun yana murmushi tare dajan motar suka shiga cikin kauyan har kofargidan su lokacin malam Hamza na zaune zaman jiransu. Da sauri Abubakar ya fito yaje gurin Malam Hamza yana bashi hakuri, shidai malam Hamzah tunda yaga yaransa sai yaji hankalinsa ya kwanta yace ai ba komai. Sim-sim INdo ta shige gida Abubakar ya tambayi malam Hamza inda zaije ya nemi auranta Malam Hamza yace. “ “Ai malam Habu tunda ka tambayeni ai kagama tambayar duk wani wanda zai baka uwata, yanzu kawai kaje duk sanda ka kintsa saika kazo ayi.magana” 
Godiya Abubakar ya dingayi tamkar cewa akayi an bashi kujerar president. Kayayyakin su ya ciro musu su Sagiru suka kwashe suka shiga dasu cikin gidan shi kuma yaja mota ya tfi yana mai jin farin ciki da nishadi
Washe gari yayiwa abban su magana sannan abban sukaje harkauyen Sani aka tambayowa Abubakar auran lNdo malam Hamza ya tara abokansa suka shaida an bashi, a take a gurin kanin abban su Abubakarya bada kudin nagani ina so dubu Hamsin sannan suka tafl suna mamakin gidan da Abubakar yazo neman aure sai dai sunsan ba yadda Allah baya tsara abinsa dan haka babu wanda ya isa yaja da al’amarin. Labari ya zaga gari an kawo kud’in INdo dubu Hamsin masu bak’in ciki nayi masu murna nayi dama haka lamarin mutane yake. A cikin satin ya siyo mata waya sabuwa tecno sabida anyi mai transfer zuwa abuja sabida haka zasu kuma yin nisa. lNdo ta cigaba da zuwa makaranta duk da tana saka wasa a cikin lamari sai dai fa ta kara yin clean domin idan kaganta sai ka dauka tana a matakin degree program ne nan kuwa ko secondary school bata kammala ba. Ta kuma rik’e alk’awari bata kula kowa duk kudinka duk kyawunka duk ajinka duk meye dinka bazata kulaka ba tace bazata yi ‘
MUSAYAR ZUCIYA‘ da kowa ba Abubakar shine a cikin zuciyana shi kuma take da burin aura… 

Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE